'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_
~August 2017~
© *Hafsat Rano*
*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''
_Vote and Follow mie on wattpad @HafsatRano, My facebook page @Rano Online Novels_
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆
*58*
A tare suka mik'e bayan sun yima Dr. Godia suka wuce d'akin da aka ajiye Amaan don hutawa, kwance take fuskar ta tayi fayau, sae a sannan Mammy tayi realising some changes a tattare da ita..Fav. Uncle ne ya zaro waya ya fita waje, ringing d'aya Abba ya d'ago da sallama. Bayan sun gaisa ne ya sanar masa da abinda ke faruwa.. Hamdala yayi ya jinjina ikon Allah, baya barin wani don wani. Alk'awarin tura Mama har gidan Mummy ta sanar mata yayi.
Lok'acin da Mama ta gama sanar da Mummy, kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, murna sosae tayi duk da hakan ya sake dawo mata da mutuwar Affan sabuwa. Family gaba d'aya ya d'auka kowa yana farin ciki.
☆☆
Lokacin da Farhan ya fita daka consultation room d'in, varender ya nufa ya sami wasu golden wooding chair ya zauna cikin d'aya... Iska sosae take kad'a wa da sanyi amma sam sae yaji komae ya tsaya masa.. Sak'e sak'e yake yadda zae bullo ma al'amarin. A zahirin gaskia baya son ya sake rasa Amaan, amma sae dae wannnan bullo war cikin ta sashi ya zama dole yayi nisa da ita.. Deciding yayi na komawa Nigeria kawae ya rungumi kaddarar sa..☆☆♡
Lok'acin da Amaan ta farka taga yadda Mammy ke mata wata sabuwar kula da soyayya sae abin ya bata mamaki, share wa tayi suka d'unguma zuwa gida wanda tun da suka tafi Farhan be ce k'ala ba, Fav. Uncle na lura dashi sae dae dole ya kyale shi don ya rungumu tasa kaddarar.BaYan sun koma gida, Da yamma sae ga wayar Farida, tana d'agawa taji kamar zata tsinke mata kunne da ihu..
"Yeeeeee... Am so happy wlhi sis, Allah ya duba mu zamu zama mothers.. Woww am so happy.." da sauri Amaan ta zare wayar daka kunnenta don tabbatar da abinda taji.. Sake mayar da wayar tayi tana yak'e suka gaisa Amjad ma ya karbe yayi mata congrats. Ita dae kawae binsu take da "Umm..." ba tare da ta fuskanci in da suka nufa ba.. Tana ajiye wayar ta jawa ledar magungunan ta, wata yar farar takarda ce ta fad'o wadda ke nuna alamar pregnency result.. Bin takardar tayi tana karantawa, tana gama karanta wa ta kankame takardar sosae tana sauke numfashi kamar wadda tayi tsere.
_"Inason ganin ranar da zaki haifa min little prince ko princess, kai..! bana jin ranar zan iya barci.."_
_"Inason naga na haifi yara, na basu tarbiyya sosae, musamman mata, ina k'wad'ayin samun rahmar ubangji daka haka.."_
Maganganun AFFAN ne suka shiga yi mata yawo a kunne lokacin da yake nuna mata tsantsar kaunar da yake ma yara.. Kuka ta saki me taba zucia tana yi tana ajiyar xucia.
Sunbato ta fari yi kamar wata zautacciya.."Allah ya gafarta maka mijina, Allah ya baka ladan niyya.. In sha Allah zan yi kok'arin cika maka burin ka na kula da yaronmu ko yarinyar mu.."
Farhan na tsaye jikin kofar d'akin ta wanda ya iso tun daxu don duba ta,tsaye yake tsak zuciyar sa na harbawa jin abinda take cewa, fasa shiga yayi ya juya yq bar wajen da sauri.
A daddafe yayi two weeks ya tattaro ya dawo Nigeria.
☆☆
A k'wana a tashi ba wuya a wajen Allah, Nana tayi nisa sosae a islamiyya, karatu take babu ji babu gani, duk wasu abubuwa da Daddy ya mallak'a da kud'ade na al'ummah sae da Mummy ta fito wa gwamnati dasu, Babban shagon da Nana ta bud'e ya kafu sosae, Allah yasa masa albarka dashi suke komae. Tym to tym suna zuwa k'iru su gayshesu suyi k'wana biyu su dawo..Kwatsam Maman su Na'eem ta k'wanta cio, dama chan asali ba me isassar lafia bace, batayi wata doguwar jinya ba Allah ya k'arbi ranta..
Fav. Uncle ne kawae ya sami damar zuwa in da yabar Amaan da Mammy da sauran yaran achan saboda school da kuma yanayin da Amaan take ciki, Haihuwa yau ko gobe.
Bayan anyi Arba'een ne Fav. Uncle da Abba suka kebe don tattauna wa.
"Yaya ni ina ganin mu nema wa Abban Na'eem auren Hajia.." Fav. Uncle ya fad'a yana gyra zaman sa.
"K'warai..! Wannan shawarar tayi, hakan kuwa shi ne zae k'ara mana donk'on zumunci.." Murmushi Fav. UNCLE yayi sannan suka cigaba da hira,. A karshe da Daddare suka sanar wa Abban Na'eem da Hajja, babu wani ja in ja suka aminci, Abba ne ya jagoranci zuwa tambayar in da nan ma Mummy bata wani bata musu lokaci ba tace
"Allah ya sanya Alkhairi.." da haka sukayi sallama kowa yana farin ciki..
Nana na dawowa daka islamiyya Mummy ta sanar mata, murna tayi sosae daka karshe suka yiwa Allah godia da chanjin da yake musu..
Cikin sati biyu aka gama komae aka mik'a amarya cikin Familyn Kurfi.
A satin Fav. Uncle ya shirya barin Nijeria bayan sun tattauna da Abba akan wani muhimmin abu da yake son aiwatar wa..
Ignore any typing error. No tym for editin😅
Include mie in ur prayrs
Rano❣
YOU ARE READING
ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)
General FictionA story of a young girl who sees the bad side of the world from both angle.. Suddenly an angel came to her rescue.. Destiny will take it place.. Will he be able to rescue her? find out in this astonishing story