page 41

2.4K 211 2
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss Xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *41*
Algaita ce ke tashi ko ta ina, gaba d'aya unguwar ta cika mak'il da motoci na alfarma, Fav. Uncle cikin shigar Alfarma yana ta mik'a ma jama'a hannu, kalle kalle kawae yake ta ina zae hango Farhan, Abba na lura dashi ya matso kusa dashi,
"Kamar kana neman wani abu ko?" Ya tambaya yana son gasgata wa,
"Eh wlhi, banga my Son ba, kwana biyun naga ya janyemun, gashi nima am always busy." Murmushi Abba yayi yace;
"Kasan sune manya, may be yana chan shima wajn friends nasa." Da haka yayi convincing Fav. Uncle ya bar neman Farhan. Duk bayan wasu yan mintunan sae Abba yayi dialing number Farhan d'in amma amsar d'aya ce, Switched Off. Allah Allah yake a gama d'aurin auren yaje yaga halin da yake ciiiki. Iyayen Amjad ne suka fara xuwa, sannan Daddy da tawagar sa ta manyan yan siyasa suka biyo baya, yan addu'ou akayi sannan aka fara d'aura auren AMJAD da FARIDA.... Wani abkin Daddy ne ya matso gaba a matsayin sa na wakilin Affan, ran yan kiru ya baci ganin gasu amma sae suka share don a rabu lafia..

☆☆
Jijjiga shi kawae Na'eem yake yana kuka, kakam Farhan d'in ya damke wayar hannun Na'eem d'in zuciyar sa na tafasa,
"Bruh ka barni na kira Abba, dole a fasa auren nan, u deserve her more than anyone, mesa kakeson halaka kanka ne??" Bashi da bakin amsawa saboda ya riga ya zama unconcious, wasu mahaukatan pills ya zuba wa cikinsa, numfashin  kawae ne ke kawae sama da kasa da karfi, gaba d'aya Na'eem ya gama tsorota, da karfi ya shiga kiran sunan sa ganin a hankali a hankali yana kasa, nauyi sosae yaji ya sakar masa wayar hannun sa ta fad'i. Da mugun firgici ya sunkuya ya d'auko wayar ya shiga had'a battery. Number Abba ya fara kira, daidai lokacin yana gaba zae karbi sadakin Aman, yana ji  ringing d'in yayi ignoring, aka cigaba da kira ya d'an kalli wayar ta gefe ya d'auke kansa, a bisa shaidu da sadaki da siga aka d'aura Auren AFFAN da AMAN😭.

A chan kuwa cikin gida gaban Aman ne keta fad'uwa, kwana biyu rabonta da ganin ya Farhan, duk batajin dadi tana son sanin wanne hali yake ciki, tashi tayi ba tare da an lura ba ta nufi part d'insu, a rufe ta tarar da kofar, kawae sae ta sami kanta da murd'a handle d'in ta shga cikin falon, shiru ba kowa a falon, direct ta zarce bedroom tana jin wani irin yanayi a tattare da ita, zama tayi gefen bedside drawers tana kare ma babban hoton Farhan d'in cikin suit me kyau a cikin jirgi, samun kanta tayi da murmushin, tana nan zaune ta rasa me take nema, kawae taji muryar maroki yana sanar da d'aurin auren ta da Affan, kasa kunne tayi har zuwa lokacin dataji an shafa, alamar kenan aure ya d'auru. A take taji zazzabi yana neman rufe ta,  Cikin rawar jiki ta fad'a kan gadon ta jawo bargo ta shige tana rawar sanyi..

☆☆☆
Na'eem duk ya rikece jin Abba be d'aga ba, kallon lokaci yayi ganin daidai lokacin d'aurin auren ne yasa shi yayi saurin lalubo number Fav. Uncle ya kira, a lokacin yana tare da jama'ar sa ana masa Allah sanya Alkhairi, ganin kiran Farhan yasa shi komawa gefe da sauri,
"Whre are U Son?" Ya tambaya yana kara wayar, jin sautin kuka kasa kasa ya sashi saurin janye wayar daka kunnen sa, da azama ya kara mayar da ita bayan ya tabbatar number Farhan d'ince, a rikice yake tambayar sa me yake faruwa,
" Na'eem ne Uncle, dan girman Allah uncle ku tsaida d'aurin auren nan, Ur Farhan is dyein here, Uncle Farhan zae rasa ransa, uncle Farhan yana son Aman......" Kuka ne yci karfin sa ya sauke wayar yana yi ba tsayawa. Kamar duka haka Fav.Uncle yaji maganar, kwakwalwar sa ta kasa figuring out masa me Na'eem ke shirin sanar masa, cikin karaji ya daka ma Na'eem tsawa,

"Me kake shirin cewa? Ina Farhan yake? Kuma wacce Aman yake so? Answer mie!!!!!"
"Uncle Aman dai dake sani, Abba yasan komae, its a long story, u have to stop the wedding and come right away." Hanging yayi bayan yaji address d'in ya nufi inda yake hango Abba da Abban Na'eem kamar zaki, ido jajawur ya karasa gabansa, abba na hangoshi yayi saurin tararsa,
"Me ya faru?" Ya tambaya yana jin fad'uwar gaba, banza yayi wa Abba ya karasa wajen Abban Na'eem ya karbi car key ya shiga ya data da gudu ya bar layin, kowa kallon sa yake ana mamakin abunda ya faru, ta maza kawae Abba yayi ya cigabaa da gaisawa da mutane.

Reception aka nufa inda kowa ya cika tunbinsa, Affan bakin sa kamar zae yage don farin ciki, ya kira number Aman sae dae batayi picking ba, kyaleta yayi da niyyar in sun gama reception zasuje ayi pics.

☆☆
Allah ne kawae ya kaishi lafia, a waje ya ajiye motar ya shiga gidan da sauri, lokaci Farhan suman sa uku, Na'eem duk yayi loosing control d'insa ya zama wani dolo dolo, yana ganin Uncle yayi saurin tararsa yasa kuka, wuce shi yayi zuwa gaban Farhan dake numfashi sama sama, kama hannun sa yayi cikin nasa, ya jawo shi jikinsa tare da rungume shi tsammm. Kad'an kad'an ya bude idonsa ya sauke su akan Fav.uncle, ai besa lokacin da kuka yazo masa ba, ba karfi sae hawaye kawae dake ambaliya a fuskar sa, murya chan ciki ya shiga magana,
"Wayyo Uncle zan mutu, zuciyata zta fashe, save mie please Uncle,banson zama me son kaina, but wlhi uncle I lurv her wt all my heart, bansan how ba, i jst cant control it, save me pls, save me pls." Shi yayi ta nanatawa a karshe, jikin Fav.Uncle yayi sanyi sosae, ya rasa me zaece sae bubbuga bayan sa kawae da yake yana girgiza kai, yau ga ranar da Farhan yake neman abu a wajen sa, be san me zae masa ba. Jin karar bude kofa kawae sukayi, Abba ne da Abban Na'eem suka shigo tare da Dr Bilal. Da kyar Fav. Uncle ya sake shi Dr Bilal ya shiga examining nasa, mamaki yayi ganin irin overdose d'in da yayi wa kansa kawae Dr bilal keyi, kallon Abba yayi yana tuno lokacin da ya ja masa kunne a kan condition d'in Farhan d'in, gashi yanzu abu yayi worst,
"We have to transfer him to hospital Alhaji, am afraid to tell U, heart nasa ya samu problem, but bansan exctly wanne irin matsala ba, so dole muje hospital nayi examining nasa throughouly, nasan irin medication d'in da zan basa." Jikin Abba sosae yayi sanyi yayi shiru yana kallon Farhan wanda ya koma kamar bashi ba, barci yake me wahala bayan allurar barcin da Dr bilal yayi masa to ease the pain, cikin jan ido Fav. Uncle yake kallon Abba, sae kuma ya matsa wajen Dr bilal yace,
"Muje kayi duk possible abunda kaga ya dace ayi, after dat zan fita dashi Waje na nema masa magani.
"Owk." Dr Bilal ya amsa ya shiga kran Ambulance. Mintuna kadan ta karaso suka nufi hospital d'in gaba d'aya. Suna isa wayar Mama na shigowa, d'agawa Abba yayi bayan ya matsa daka wajen don bayason susan abunda ke faruwa for now,

"What! Ya furta da karfi, are u sure kun duba ko ina?"
"Mun duba ko ina and she's no where to be found, ga angwaye sunzo zaayi pics amma bata gidan gaba d'aya."
"Owk calm down, am coming home right away." Hangin yayi da sauri ya shiga mota ya nufi gida..

Ga breakfast, Manage pls

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now