page 60

5.7K 312 43
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

_Vote and Follow mie on wattpad @HafsatRano, My facebook page @Rano Online Novels_

*LAST PAGE*

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆

           *60*
*W*ani irin gud'a Hajja ta saki suna saka kai a falon ta, turus sukayi ganin mutanen Kurfi, dana K'iru zazzaune..

Gaishe su sukayi suna kallon yadda suke binsu da kallo cikin farin ciki.

"Ku zauna Anan.." Hajja ta nuna musu gefe, zama sukayi suna kallon ikon Allah. Kowacce da tunanin ta a zuciya saboda haka hankalinsu sam baya wajen, tsinkayar murya sukayi a kansu;

"Da hannu za'a fara ko kafa?.." a tare suka kalli matan dake zaune gabansu kowacce rik'e da k'wark'waron kunshi, ba magana kowacce ta mik'a kafarta aka shiga zana musu kunshi na alfarma..

Almost three hours aka d"auka ana abu d'aya, daka karshe suka cire, tsayawa fad'ar had'uwar kunshin ma bata baki ne..

Bedroom d'in Hajja Amaan ta shige ita kuma Nana ta juya zuwa part d'in Mummy.

Cikin shigar Alfarma Mummy zaune cikin manyan k'awayenta ana ta hira, farin ciki tsantsa ne k'wance a fuskarta. Har k'asa Nana ta tsuguna ta gaishe su suna mata Allah sanya Alkhairin da ta kasa gane in da suka sa gaba..

"Muje ciki Nana..." Wata k'awar Mummy tace tana mik'ewa.

Ba musu tabi bayanta suka shiga d'akin Mummy..

Ruwan Wanka ta had'a mata a toilet wanda yasha kayan kamshi ta umarce ta ta shiga. Kamar ragumi da akalarsa haka tabi bayanta zuwa toilet d'in, sae data nuna mata yadda take son tayi sannan ta fito bayan ta ja mata kofa.

Tafi minti goma zaune cikin toilet d'in ta kasa aiwatar da komae, da k'yar ta saita zuciyarta ta  ta fad'a Bathtub d'in ta fara wanka cikin kasala...

Tana fitowa ta ytarar da wani ubansun Lace Aqua Blue me da touches d'in Mint Green. Sae head d'in daya kasance Mint Green shima.

Shirya kanta tayi sosae sannan ta jawo kayan ta saka, wani irin kyau sukayi mata na ban mamaki, kallon kanta takeyi acikin mirrow kamar ba ita ba, tana nan tsaye rik'e da d'ank'wali a hannun ta don ba sanin yadda zata d'aura shi tayi ba, aka turo kofa aka shigo..

"Sunana Khadija amma ana k'irana da Dieja Ran Glamour, nazo miki makeup ne yadda angonki zae kasa gane.." ta fad'a tana k'okarin ajiya makeup kit d"inta.

Murmushi k'wance a fuskarta ta mik'a mata hannu,

"Nice to meet U dear, ina followin naki ai a instagram, woow kece Fav. Makeup artist d'ita duk da am not into make up, buh i like Ur style.."

"Its my pleasure.." ta amsa mata tana murmushi..

Cikin k'warewa ta shiga tsara mata makeup kamar ba'a Nija ba, in less than one hour ta gama mata har d'aurin.

"Wow.. Kin ganki kuwa.." ta furta tana zagaye ta,
"GAskia tukwuici na a wajen ango me tsokane.." Murmushi Nana tayi tana son ta tambayi waye angon amma bata son ta zargi wani abun, kallon kanta ta ringa yi a mirror tana admiring kyaun da tayi. Da haka sukayi sallama da Dieja Ran ta k'washe kayanta ta fita..

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 13, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now