page 24

2.9K 229 1
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by;
Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

Salma Mannir M
Asma'u Kabir Lawal
Eeesha Bagwae
ABU
Indon Village
Fateemah Aliyu
Fateemah Dan Maliki
Maryam Ammani
Meenah Ghana
And
All members Of Miemiebee👄novels grp2⃣.
'''Here Is ur Page, With Lurv From Aunty Sis'''.

Rano na gaisheku, Allah ya bar k'auna.. I heart U All❤
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *24*
Tun a hanya ba abinda Nana take sae kuka, Hany ce ta karb'i driving d'in don tsaf Nana zata iya watsa su gefe. Ita kanta ranta babu dad'i, bata zata haka Farhan d'in ya had'u ba, tana ganin shawo kansa abu ne me sauk'i, sae gashi sun zubar da kansu sunje har gida ya watsa musu k'asa a ido..

Da suka isa gida ma babu wadda ta tsaya a parlo suka wuce bedroom nasu kowacce ran nan ba dad'i.

☆☆☆
Da sauri Farida ta k'arasa part d'in Hajja har tana had'awa da tuntub'e,

"Umm Hajja, Abun duniya baya k'arewa". Ta fad'a tana tabe baki,

"Me faru"? Hajja ta tambaya.

"Ashe yanmatan Yaya ne, yace wai k'annen abokin sa, kuma da alama ba biko suka xo don naji Yayan na cewa ta ky'ale sa, ko shima tazo sawa a sace mata shine",

"Toh munafuka, Ina ruwanki"? Ya fad'a yana k'arasowa cikin parlon.

Da gudu tayi bayan Hajja don ganin b'acin rai kwance a fuskar sa, Hajja ce ta shiga tsakani amma duk da haka sae daya rank'washe ta aka, k'ara ta saki jin zafin rank'washin.

"Toh mene abun munafurci anan maigida?? Dama nima nayi tunanin haka, yarinyar a haka kamar ta gari sae shed'an ci  fal ciki".

Ficewa yayi kawae ba tare da yace komae fa, tab'e baki ita ma Hajjan tayi ta ja Farida d'aki don samun k'arin bayani..

☆☆☆
A tsaye yake yana k'are ma wasu gidaje kallo, ko shakka babu akwae wani abu da yake faruwa sae de besan mene ba, duk tunanin sa ya kunce musamman da yaji komae daka baki me tushe, sae da ya gama sak'e sak'en sa yaja motar yabar layin.

Barin layin sa kenan suka fto suna daria, kana kallonsu kasan suna cikin farin ciki,  duk cikin su babu k'aramin mutum, kowanne ya nufi abin hawan sa ya shiga suna d'aga ma juna hannu.

Tafiya yayi sosae kafin ya fara tunanin in da ya dosa, duk da mugun son ganin Aman da yakeyi Amma dole ya fara tabbatar da wanzuwar farin ciki a zuciyar mahaifiyar sa kafin kuma ya dawo kanta. Juya akalar motar yayi zuwa gidan wani abokin sa, duk da shi ba ma'abocin tara abokai bane amma yana da yan tsirari wanda tsarin su ya dace da juna. A k'ofar gida ya tsaya ya shiga nemn layin sa a waya, cikin sakonni da bazasu gaja uku ba aka d'aga daka d'ayan bangaren.

"Oga kana duniyar nan dama?" Abokin ya tambaya cikin son tabbatar wa.

"Ina nan wlhi, gani ma a k'ofar gidan ka".

"Ah lallai yau na ciri tuta, bari na sanar da madam sae naxo nayi ma iso".

katse kiran yayi ya kwantar da kansa kan steering motar yana sake zurfafa kansa a cikin tunani.

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon