page 52

2.5K 198 0
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

_Follow mie on wattpad @HafsatRano, My facebook page @Rano Online Novels_

Whre are u Home of Novels, this page is for U, thanks for ur lurv❤

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *52*
Adaidaita sahu(keke nepep)ta tsayar ta fad'a mishi sunan unguwar da link d'in, basuyi wani ciniki ba ta shiga, har kofar gate d'in gidan ya kaita ta ciro dubu d'aya ta bashi.

Tsaye tayi a wajen tana kallon gate d'in a kulle, tunanin yadda zata shiga take tunda ita babu muk'ullin a wajen ta, sai ga motar yan sanda ta shigo layin, saurin cire nikaf d'in fuskar ta tayi har suka karaso. Saukowa sukayi suka nufo wajen da take tsaye, 

"Hajiya lafia kike tsaye anan?" Daya daka ciki ya tambaya kasancewar ya gane ta,
"Wallahi naxo d'aukar abu ne a gidan sai kuma na manta ban d'auko key d'in gidan ba, yanzu haka ma tunanin koma wa nake sai gaku." Ta bashi amsa tana kallon gateman zaune a bayan motar yan sandan.

"Be kamata ki fito a wannan yanayin ba hajia, duba da halin da ake ciki, anyway tunda kinzo muje ki d'au abun sai muyi miki rakiya zuwa gida. Gaba d'aya suka dunguma suka shiga gidan har da gateman wanda dukkan alamu wani abun akazo bincike.
A compound d'in gidan ta barsu ta nufi ciki tana share kwallar data zubo mata,

"Yau zan kawo karshen wannan abun, Affan d'ina ya dawo mu cigaba da rayuwar da muka faro cikin kwanciyar hankali." Ta fad'a a zuciyar ta tana bud'e kitchen cabinet, babban kwali ne na foodflask a ciki, sabon flask ne wanda ba'a taba amfani dashi ba, sauko dashi kasa tayi bayan tayi ziping jakar ta ta d'aga shi sae ga takardu da clips d'in evidence d'in gaba d'aya, bud'e jakar tayi ta zuba su ta zauna wajen tana tunani;

'''"Lokacin da Affan ya bud'e safebox ya saka tana kallon sa, bayan ya fita gun abokin sa ne taje ta bud'e ta d'auko su, d'aya bayan d'aya ta dudduba su sannan ta chanja musu maboya, duk a tunanin ta in aka neme su aka rasa Daddy zai hak'ura, haka shima Affan."'''

Goge hawayen da ya sauko mata tayi jin d'an sandan yana kiran ta, a kofar kitchen sukayi kichibis, kallon ta yayi kamar yana nazarin wani abu, saurin k'ak'alo murmushi tayi ta wuce gaba da sauri,  bin bayanta yayi cikin tausaya wa suka shiga motar gaba d'aya.

Har daidai kofar gate d'in gidan suka ajiye ta, sai da suka ga shigar ta sannan suka ja suka tafi. Suna tafia ta fito da sauri sanye da nikaf d'in ta. Adaidaita sahun ta k'ara tsaidawa bayan ta tambaye shi in da take so ya kaita, amma ita bata san wajen ba, kasancewar babu in da yan sahu basu sani ba yasa bata sha wahala ba ta shiga yaja suka tafi..

Nana ce ta fito sanye da riga da skirt na atamfa, fuskar nan tayi fayau, tunanin tunkarar Daddy ta maganar whereabout d"in Affan take suka kusa kara da Farhan, kallon ta ya tsaya yi na wani lokaci sannan yace;

"Inason ganin ki dama." Kafin ta amsa ya cigaba,
"Inason sanin yadda akae kikasan Aman was in trouble last time da akae poisoning nata." Ya hard'e hannayensa yana jiran amsar ta, satar kallon sa tayi ta gefen fuskar ta, lokacin da sukayi wayar bata sanar dashi komae ba, and she's not ready now ta fad'a masa cewa Daddy ne da wani taji suna maganar,
"Ina jinki." Ya katse mata tunani
"Emm.. emm.. dama Bruh Affan ne mukayi waya yace naje na kula da ita akwae matsala. Karantar yanayin ta yayi na wani lokaci sannan ya wuce ya barta a wajen.

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora