page 45

2.6K 197 0
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss Xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *45*
"Daddy why?" Ta fad'a tana karasawa gabansa,
"Baki gane wace bane Nana? Yarinyar da na baki aiki kanta, har ake accusing naki akan batan ta, kin manta?"
"Ko daya Daddy, nasan itace."
"Then kikayi me?, kinsa ba karamin cikas zata kawo ma siyasa ta ba, kuma kika barta, aina shi Affan d'in suka had'u." Ya fad'a duk a rud'e. Mummy na gefe tana kallonsu bata tanka ba,son kan na Daddy yayi yawa. Masifa yake ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,
"Affan yayi kad'an yace zae wulakantani, yayi kad'an wlhi." Fuu ya fice yana dialing number a wayar sa. Kuka Nana tasa sosae ta fad'a jikin Mummy,
"Me yasa Daddy yake haka Mummy? Be damu da Farin cikinmu ba sae nasa, wannan wane irin rayuwa ce." Tapping bayanta Mummy keyi ba tare da tayi magana ba don zuciyar ta ce kawae ke raya mata abubuwa da yawa, ita sam bata yi sa'ar miji ba, Daddy sam bashi da Imani zae iya komae akan yaga yayi maintaining statue d'insa. Dago Nana tayi wadda ke jan numfashi har yanzu, ta rasa gane dalilin kukanta haka,
"Nana." Ta kira sunanta tana d'ago ta, fuska ta d'ago ta zubawa Mummy rinannun idonta,
"Me ya saki wannan kukan haka?, kar kice min akan abinda Daddy yayi wa Aman kike kuka, i wnt believ U ma" share hawaye tayi sannan ta kalli Mummy,
"Kuka na da biyu ne Mummy, last time na kira Farhan a wayar sa, sae Broda d'insa ya d'aga, dana had'a shi da Allah akan ya sanar dani me yake damun Farhan d'in,sae yake sanar dani ai bashi da lafia sosae, kuma duk akan Aman ne. Ranar Mummy kasa barci nayi, inason Farhan sosae Mummy, ba yadda buri na kuma zae cika in Aman tana nan, yanzu in Daddy yasa bruh Affan ya saketa shikenan wlhi na rasa Farhan Mummy." Ta karashe cikin kuka me tsanani. Kmar gunki haka Mummy ta tsaya tana kallonta, wato Alhaki ne yake bin Nana, ita kuma haka tata kaddarar take daka wannan sae wannan, tausayin yar tata ne ya kamata, tabbas tasan menene so tunda itama ta samu kanta ciki kafin auren su da Daddy, amma da yake akwae rabo kuma matar mutum kabarinsa sae gashi bata ci nasara ba. Rungume ta tayi sosae tana jin saukar hawayenta akan kafadarta, bata hana ta kuka ba sam, she deserves to cry, cikin dakewa ta zame jikinta tana kallonta,
"Aisha!" Ta kira sunanta for the first time in her life, da sauri Nana ta d'ago,
"Inason ki sani duk wani abu daya faru da bawa dama mukaddari ne chan daka Allah, wani baya aurar matar wani, haka wata bata aurar mijin wani, in Farhan mijinki ne ko duk duniya sun had'u basu so sae kin aure shi, haka in ba mijinki bane ba yadda zaki aure shi, ki sani sau da dama mutum nason abu amma sae ya zama ba alkhairi bane a rayuwar sa. Ki rik'e wannan a rayuwar ki, Ina rokon Allah ya zaba miki mafi Alkhairi."
Words d'in Mummy sunfi komae bada peace of mind, a take taji half of damuwar da take ciki ya ragu, kankame Mummyn tayi sosae tana sauke ajiyar zucia
"U are the best Mummy, nagode sosae zanyi amfani da abinda kika ce i promise."
"Dats my gurl, Allah yayi miki Albarka."
"Ameen Mummy." A tare suka mik'e zuwa d'akin Mummy d'in don kiran Affan a waya.

☆☆
Lokacin da Affan ya bita har ta kai gate, cikin sassarfa ya cim mata tare da rik'ota kamkam don idonta ya rufe, hugging nata yayi ganin kamar bata hayyacinta don yasan dats what she need the most, sae dayaji ta daena shashshekar ya janye ta tare da bude mata kofar baya ya kwantar da ita sannan ya zagaya mazaunin driver yaja suka bar gidan. Har suka je gida ba wanda yayi magana, sae daya gama daidaita parking sannan ya zagaye bangaren ta ya fto da ita kamar wata yar Bby ya sa kafa ya rufe motar suka haura balcony. A saman kujera ya sauke ta ya tsuguna yana zare mata takalmin kafarta,
"Am so sorry." Ya furta lokacin daya gama cire mata talakmin, murmushin yak'e tayi ganin damuwa karara a fuskar sa, hannu ta mik'a masa ya taso daka tsugunne da yake tare dayin masauki a gefenta. Hannun sa ta rik'o cikin nata tana murmushi, murmushin yayi shima yace;
"Kiyi hak'u....."
"Shsshhhh.." ta katse shi ta hanyar dora hannunta akan bakin sa,
"Babu komae, Daddy ai maihaifi nane nima, don nayi laifi yayi mun fd'a babu wani abu." Sororo yayi yana dubanta bako kiftawa, kar dai ace har ta manta cin fuskar da Daddy yayi mata? No it cant be,kawae so take ta shashantar da maganar. Ya bawa kansa amsa, mik'ewa tayi ya bita da kallo har ta shige bedroom d"in ta had'e da rufo kofar, mik'ewa yayi zae bi bayanta sae kuma wayar sa ta fara ringing. *My everyting* sunan da yayi ma Mummy saving kenan, d'aga wa yayi tare da yin handfree,
"Affan kana ji nako?" Ta fad'a bayan ya amsa sallamar ta,
"Kuna ina?"
"Mun dawo gida Mummy."
"Owk ina Aman d'in?, babu wata matsala dai ko?"
"Eh Mummy, i was trying to explain ma sae kawae tace ai bakomae." Jinjina kai Mummy tayi tana jin son Aman har ranta,
"Shikenan Allah yayi muku albarka, ka shawo kan matar ka, zan san yadda zan shawo kan Daddy dukda sam bana goyon bayan sa, amma dole a bashi girman sa a matsayinsa na shugaba."
"Shikenan Mummy na gode Allah kara girma." Katse kiran yayi yana shafa fuskar sa. Gyara zama yayi ya kiran number wani suka gama magana ya kashe.

Da yamma sae gasu Jalila da Ummi sun xo mata sallama zasu wuce gobe, murna sosae Aman take ta rasa ina zata sakasu, basu fi 30mint suka tafi, bayan sun kara mata nasiha akan zaman aure.

Da daddare suna zaune Aman tayi pillow da cinyar sa kamar babu wani abu daya faru, ahankali yake caressing gashin kanta wanda yasha gyara sosae, so yake suyi magana ya rasa ta ina zae fara, chan ya tattaro nutsuwar sa ya kira sunanta in a romantic way,
"Baby."
"Umm." Ta amsa tana kallon sa. Inason muyi magana in bazaki damu ba, nodding kanta tayi bayan ta juyo da fuskar ta ,

"Da farko zan fara gode ma Allah (S.W.A), da ya bamu chance na zama ma'aurata, Alhamdulilah, alhamdulillah. Secondly kuma akan maganar Daddy ce, nasan kinsan waye Daddy, amma kuma akwae abinda baki sani ba,na zabi na sanar dake ne saboda a yanzu in kika cire Mummy bani da wata ko wani abokin shawara da ya wuceki, a rayuwa ta na gamu da abubuwa biyu da suka zaman mun abin da nake kwana dashi nake tashi, nayi wa kaina *alk'awarin* ko *bayan rai*na inaso na cika burina.
  Na farko kece Aman, babban burina shine naga na samaar miki yanci, ki zama kamar ko wacce ya a duniya, Alhamdulillah, burina ya cika. Na biyu Aman shine na hana Daddy cin zaben."
Da sauri ta mik'e tana kallonsa jin maganar banbarak'wai

"Abinda kikaji shi nake nufi." Ya bata assurance don yaga abinda take shirin tambaya ne.

"Amma mesa habeebty? Mesa?"
"Hmmm." Ya sauke ajiyar zucia. A take ya shiga zayyana mata abubuwa akan Daddy, iya kar firgici ta shiga, kuka ta fara sosae tana jijjiga kai, shi kanshi ji yake kamar yayi kukan in ya tuno wai Mummy ce sacrife d'in da Daddy zae yi in ya sami nasara. Yan yatsunsa yasa ya shiga goge kwallar data sakko mishi sannan ya jawo hanky mai kyau ya shiga share ma Aman idonta yana girgiza kai,
"Ni danake son ki zama strong ki taimaka min, in kuma tun Farko kinyi loosing hope ya zaai muyi nasara?" Goge ragowar hawayen ta shiga yi da sauri tana kallonsa,
"Kaga ni ai na daena kukan ko? Na zama strong ko?"
"Yea kin zama, duk wasu evidence suna bedroom d'ina, na rasa yadda za bullowa abun."
"Ba komae, in sha Allah zamuyi nasara." Ta fad'a tana son gamsar dashi. Basu wani jima a falon na suka nufi bedroom don kwancia. Wanka Aman tayi sannan ta d'auro alwala wanda ya zama kamar jikinta, zaune ta sami Affan kan gado cikin doguwar jallabiya ash sabuwa kal, hijabi da daguwar rigarta ne a hannunsa, a kunya ce ta karba ta juya toilet don saka kayan, tana fitowa tayi shafe shafenta duk a kunyace, sallaya ya shinfid'a musu yace mata bismillah. Raka'a biyu sukayi sannan ya juyo ya kama kanta yayi addu'ar da manzon Allah ya koyar damu, tambayoyi yayi mata game da addini ta bashi amsa, zuciyar sa sae harbawa take kamar zata faso ta fito, mik'ewa yayi ya zare mata hijabin ganin irin zufar da take duk da fan d'in dake d'akin.
"Common whats wrong Bby?" Da sauri ta girgiza kanta,
"Amma kike sweating haka?" Nan ma girgiza kai tayi tana tuno labarin da Farida ta bata da sukayi waya, dukkan alamu sun nuna yau kam kashinta ya gama bushewa. Dayan side d'in gadon ta kwanta ta nannad'e kafarta kamar alkaki, duk sae tausayinta ya kamashi, hawowa gadon yayi ya matso kusa da ita, da sauri ta mik'e tana masa kallon ka ji kaina, murmushi yayi ya rik'o hannunta,
"Ba abinda zae faru kinji? Believe me, am always wit U." Nodding kanta take don jinsa kawae take ba wai ta yarda ba, komawa tayi ta kwanta tana karanto duk addu'ar data xo bakin ta. A hankali ya d'ora lips dinsa akan nata ya shiga aika mata da sakonni, duka tsorace take ta kasa sakin jikin ta, wani sabon al'amari ne yake mata yawo, duniyar ma'aurata naga suna nemen lulawaa wanda Aman bata san dawar garin ba sae da taji abun ya fara wuce karfin tunaninta yasa ta shiga magiya tana pleading, ganin haka yasa naja 406 dita na fece🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀.. asubah ta gari

☆☆
Farhan na zaune a gefen sick bed d'insa yana danne danne a wayar sa,zahiri ba wayar yake dannawa ba hankalin sa na wani wajen, Dr Bilal ne ya shigo Fav. Uncle na take masa baya,
"Lalle my patient an samu sauk'i, Allah ya kara sauki."
"Ameen." Fav.uncle ya amsa yana kallon Farhan. Crosschecking nasa Dr.Bilal ya karayi daka nan yayi signing discharge paper ya bama Fav. Uncle, godia yayi sannan suka bar asibitin.

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now