page 22

3K 218 2
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by;
Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

'''Ina kike Aunty Maijidda Musa Maman Yan biyu, Wannan page d'in naki ne, Allah ya bar zumunci, Allah ya raya yan Biyu ya kawo wasu yan biyun sau goma sha biyu'''🙊🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀

_Kar a gaji dani ina barar addu'a please_👏🏻

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *22*
Mik'ewa tayi tana kakkab'e rigarta, ko ina na jikin ta rawa yake. Nafi ce ta k'araso tana shrv'ar hawaye, kalle kalle kawae take kana gani kasan a tsorace take.

Sake maimaita tambayar yayi yana ko'karin haske Nafi, saurin kare fuskarta tayi, cikin muryar kuka tace;

"Dandali mukazo shine suka tare mana hanya".

"Kun sansu ne"? Ya tambaya yana sauke fitilar tasa.

"A'a bamu san su waye ba", Nafi ta bada amsa.

Kamar Aman ta furta su Garbati ne sae dae bata da sauran courage, shiru tayi tana tausayin Nafi don ba k'aramin son Garbati take ba.

"Illar fitar mace cikin dare kenan, na tabbata ba'a san kun fito ba don gidan Baffan kudu akwae sa'ido musamman akan harkar ya'ya mata."

Jin yama gane su yasa Nafi ta shiga rok'an da ya rufa musu asiri, shiru kawae yayi ya wuce gaba suna bin sa a baya har k'ofar gida. Sae dayaga sun janye yar langa langar nan sun shige sannan ya juya yana jinjina al'amarin.

"Wane anan? "Kawu ya fad'a yana k'araso wa jin motsi.

A guje suka kwasa suka shige b'angare su Nafi.

"Ja'irai da kun bari nazo nan na same ku  ai".

Kaf cikin su ba wadda ta samu wani barcin kirki, kowa da abinda yake sak'awa,. Mamakin Garbati kawae Aman take, dama haka ne wani ba da zucia d'aya yake son ka ba.

Da gari ya waye suka shiga d'akin Gaji, anan suka tarar da Rahmata zaune tana shafa mai.

"Ya jikin Rahma"? Aman ta tambaya fuskarta d'auke da murmushi tana ko'karin zama a gefen ta.

"Da sauki sosae, jia nayi ta jiranki har na gaji nae barci".

Kallon juna sukayi ita da Nafi suka tuntsure da daria.,

Sae Da asubah da suka tashi abun ya basu daria, Aman harda gwada yadda Nafi ta rud'e.

Waje suka jawo Rahmata suka shiga bata labarin abunda ya faru,

"Wallahi Nafi kinfi ban daria, muryar ki har wani rawa take, Anya kuwa baki saki fitsari a wando ba?? Hahaha Ji kake Fas a fuskar Nafi. Wayyo cikina". Aman ta fad'a tana rik'e cikin ta kamar zata kai k'asa.

Daria suke dukansu har da Rahmata,
"Maganin mara sa jin magana kenan ai, amma ina jin fa Ma'u ce tasa aka rama mata marin da kika mata". A cewar Rahmata

Shiru sukayi suna nazari, tabbas zae yiwu ita d'in ce, kafin su gama ftowa daka tunanin sae gata ta tawo hannun ta rik'e da kara tana yan wak'ok'inta cikin jin dadi. Sae data xo daidai su sannan ta k'ara k'arfin muryar tata, Ci kanki basu ce mata ba har ta wuce tana dogara kara a k'asa.

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now