page 16

3.2K 254 0
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by ;
Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *16*

A bakin Rafi suke ita da Rahmata da Nafi, dutsuna ne k'ananu irin masu sumul sumul a hannun ta tana jefa su ciki rafin.
Yanayin garin yana mata dad'i sosae. Tunani take Ko ya Mummy da Affan suka shiga lokacin da suka neme ta, har gobe bazata manta Alherinsu gareta ba.

Yanayin Kallon Da Affan yake mata da irin kalamen da ya fad'a mata in ta tuno yakan sa ta manta halin da take ciki na wasu yan lokuta.

Firgigit ta dawo daka duniyar Tunanin da take bayan jin hannuwan Rahma kan kafad'arta.

"Me kike Tunanin ne Yar uwa? Naga farin ciki lullub'e akan fuskarki."

Murmushin ta ta kara fad'a d'awa,
"Ba komai Yar uwa yanayin garin ku kawai ke burgeni."

Karaf Nafi dake gafe ta amshe
"Kwarankwatsa Tunanin Saurayin ta take, Haba ko Rahmata dubi yadda take murmushi mana."
Daria gaba d'aya suka sa.
"Gaskia Nafi ke yar sa'ido ce, ni yarinya dani ina na isa saurayi? Umm?. " Aman ta tambaye tana murmushin

"Ji mata da wata magana, aradun Allah in a nan garin namu kike da tuni kina da ya'ya kamar biyar Ko Rahmata? Muma da kika ganmu haka karatu ne ya tsayar damu, Baffanmu na birni shi ya hana a mana aure da wuri ai da tuni muna d'akin mu abunmu."

"To uwayen Surutu, aikin kenan ko? "Sukaji Muryar Baffa Mainono a kansu, cikin azama suka shiga d'eban ruwa kowacce tana tsoron masifar sa..

Da daddare suka saci jiki sukayi dandali don suna son nuna ma Aman irin kalar Rayuwarsu. Farin ciki sosae tayi don ba k'aramin burgeta abin yayi ba, ashe akwae irin wannan rayuwar me dad'i bata sani ba, gaskia dama zata dauwama A kauyen su Rahmata da bata da sauran damuwa.

Tana chan aikin tunani Bata san su Rahmata kowacce tayi wajen Saurayin ta ba. Kamar daka sama taji sallama

"Assalamu Alaiki ya kyakkyawa."
D'ago idonta tayi don ganin me mata sallama, wani matashin Bafulatani ne, fes dashi cikin yar shararsa Fara k'al da ita, gefen fuskar sa bille ne kwance na fulani.

"Wa alaika salam." ta bashi amsa tana gyara zama..

Is'hu kenan d'an gidan Sarki, gaye me k'walisa da gayu kaf kauyen ba wanda ya kaishi, yan mata da yawa sun mato kansa sae dae bashi da time d'insu, a ganinsa shi da ya fita har jihar Sokoto inda yayi secondary d'insa, sannan ya dawo Sa'adatu Rimi yayi NCE d'in sa ai yafi k'arfin yan matan garinsu..

Cikin k'warewa da nasan salon daidai wayewar sa yake karya zancen Soyayya ma Aman, gaba d'aya ma ita dariya ya bata.

Zuba kawae yake, yan mata da yawa sunji haushin Aman, Rahmata nachan da nata saurayin Lado aka kai mata rahoto, da azama ta taho don gasgata wa. Zama tayi gefen Aman, aikuwa hira ta koma kanta, farinciki kamar me yau gata ga d'an k'walisa Is'hu. Naira d'ari ya zaro sabuwa kal da ita ya mika ma Rahmata na kamun k'afa. Ba wani bata lokaci ta karbe tana k'ara jaddada masa komae yazo gidan sauk'i.

Ko a hanya da suka taho dasu Rahmata sae da suka k'ara jaddada mata kar tayi sake Is'hu babban Yaro ne. Ita gaba d'aya ma yadda yake magana da wani sa turanci shi yafi mata dariya, shi a nasa tunanin ya gama birgeta da turanci be san itama ba iyawa tayi ba..

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora