page 50

2.5K 200 3
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

_Follow mie on wattpad @HafsatRano, My facebook page @Rano Online Novels_

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *50*

A hankali numfashin ta ya fara dawowa, hamdala doctors d'in sukayi saboda ba karamin fitar da rai sukayi ba. Fita Dr Bilal yayi don sanar dasu Abba, a rik'ece Abba ya amsa ya shiga kiran Abban Na'eem da Fav. Uncle, cikin lokaci kad'an Suka isa asibitin, tsoro da firgici sosae ya kamasu jin bayanin Dr Bilal akan wai poison aka sa mata a fruit, Nana na zaune gfe ta rafka tagumi tana kallon su, Fav. Uncle ne ya shiga wajen Farhan ganin shi zaune ba magana, yana ganin sa ya rungume shi ya saki kuka me tsuma zuciya.. Tapping bayan sa kawae Fav. Uncle keyi zuciyar sa tana suya shima, lalle kowa ne yayi ma Aman d'insa haka sae ya fuskanaci hukunci me tsanani. Sae daya samu Farhan d'in ya nutsu sannan ya barshi ya fita zuwa wajen su Abba, a lokacin har yan sanda sun karaso. Gidan suka wuce don gudanar da bincike.

A lokacin da suka karasa gate man na zaune ya rafka tagumi, shiga cikn falon sukayi in da suka tarar sa ragowar Apple d'in har ya gama kumbura ya fashe, pictures d'in wajen suka d'auka sannan aka sami handglove da wani farin kyalle aka d'auke ragowar don zuwa lab ayi bincike..

Duk abinda ake gateman na tsaye yana salatin jin cewa a poison ne Apple d'in, jikin sa na rawa daya ga A.S.P ya tako zuwa wajen sa.
"Zaka bimu station don Amsa mana wasu tambayoyi." Ya fad'a yana nuna masa motar su, jikin gateman sae rawa yake haka suka tusa keyar sa.

Duk tambayoyin da suka yi masa ya amsa, tambaya d'aya ce waya bashi fruit d'in shine be sani ba, dole aka sashi a list d'in prime suspect har zuwa lokacin da Aman zata farfad'o.

☆☆
A hospital kua Nana sae trying number Affan take amma baya going, tana nan zaune tana tunanin kiran Daddy sae ga wayar sa ta shigo. Daga wa tayi a tsorace ta kara a kunnen ta,
"Where are U?" Ya tambaya.
"Muna.. Hospital Daddy."
"Hospital kuma?" Ya tambaya yana mamaki,
"Me kike a hospital?"

"Matar bruh Affan akae poisoning, ryt now ma baa san stand d'in da take ba , alive or death, and shi kuma Affan d'in All his numbers basa goin, am damn worried Dad." Ta karashe tana share hawaye,

Wani mugun tsro ne ya ziyarci Daddy, a take maganganun Na'aliya suka shiga amsa kuwwa a kunnen sa,
"Zan iya komae akan position d'ina, ko da kuwa raba mutum da numfashin sa ne don ba shine na farko ba." Safa da marwa ya shiga yi a guest house d'insa, da sauri ya jawo wayar sa ya fara neman layin Na'aliyan, tana ta ringing har ta gama baa d'aga ba, kamar wani zararre ya fito daka gidan ya fad'a mota ba tare da jiran driver ba yaja ya nufi gdan Na'aliya.

☆☆
Lokacin da ya karasa Na'aliya na zaune yana kurbar juice yana kallon restling yana ihu,

"Yawwa buga shi da kasa, yawwa ywwa chan chan dae." Sae ya kece da wata daria, yana sauke cup din bakin sa yaga Daddy tsaye a cikin falon,

"Welcm Abokina." Ya fad'a yana mik'ewa,
"Wannan unexpected visit babu sanaarwa, bismillah." Kallon sa kawae Daddy yake,duk rashin mutuncin sa Na'aliya ya taka shi , kasa magana yayi har ya nemi waje ya zauna.

"Haba honourable me jiran gado, ya naganka haka? Ko har ka fara karaya ne?"  Kin bashi amsa Daddy yayi sae ma chanja akalar zancen da yayi,
"Magana nakeson muyi excellency." Ya fad'a sounding a little bit disturbed.
"Owk owk ba damuwa, ina sauraron ka." Ya amsa masa yana kashe televisin d'in

"Don Allah ka barni da Affan, ni nasan yaron bashi da matsala zae dawo mana da komae, ka bani nan da kwana uku." Wata irin mahaukaciyar daria Na'aliya ya saki yana nuna Daddy,

"Lallai honourable ba da gaske kake son kujerar nan ba, ai da da gaske kake so da tuni ka gama komae a ranar da abin ya faru, kaga ni bana sanya gaskia, komae inayin sa da zafi zafi. Don haka kar ka damu zan yi komae yadda ya dace." Jikin Daddy yayi matukar sanyi, kasa magana yayi har sae da Na'aliya ya dafa shi,

"Be a man kawae, kaje gida sae munyi waya." Mik'ewa yayi ya fice yana tunanin mafita,

☆☆
A tsakiyar falon ta tsaya kanta na juya wa, ta baro hospital d'in ne kafin anjima ta koma, tun a hanya ba irin kiran da batayi wa Affan ba amma shiru.  Kamar daka sama taji ana bubbuga kofa a sama, da sauri ta nufi saman tana mamaki, d'akin Mummy ta nufa jin daka nan bugun ke fitowa, murd'a handle d'in tayi taji shi a kulle gam,
"Mummy!" Ta ambata da sauri,
"Are u there?" Ta tambaya a rikice, jin ba amsa sae wani irin sound yasa ta ruga a guje ta nufi d'akin Daddy, drawer ta fara jawowa tana watso kaya, duk ta birkita ko ina tana neman spare keys din gidan, sae data gaji da nema har tayi giving up sae ga wasu bunch of keys masu uban yawa. Da gudu ta kwasa ta ta nufi d'akin Mummyn ta shiga gwada su one by one. Tasha wahala kafin ta gano, ihu ta saki lokacin data ga Mummy kwance hannayenta duk jini, ko bud'e idonta bata iyayi saboda tsabar azaba da yunwa. Fita tayi tana ihu don Daddy ya sallami duk masu aikin gidan sae maigadi kawae, shi ya biyo Nana ya taimaka mata suka fito da Mummy suka sata a mota..

Asibitin Dr bilal d'in takae Mummy, da farko sun zata hatsari ne suka k'i karbar ta sae an zo da yan sanda, sae da taje d'akin da Aman take ta tarar da Fav. Uncle da Farhan zaune gabanta suna kallonta, cikin kuka ta sanar dasu, bin ta sukayi sannan aka samu aka karbi Mummy aka shiga bata taimakon gaggawa.

An samu treating wound d'in hannayen ta dana kafanta, sae magunguna da drip da aka d'aura mata.. wani irin abu ta farayi kamar numfashin ta zae bar jikin ta, Bp d'inta sukaa auna suka ga yayi mugun hawa, da sauri aka zare drip d'in sannan ta dawo normal, allurar barci akayi mata.
Nana na zaune in banda kuka ba abinda take, sae yau ta tabbatar Daddyn su ba karamin mara imani bane, shine ya rufe Mummy tsawon kwanakin nan a d'aki, tunanin ta ina  Affan yake har yanzu be zo ba. Gaba d'aya tayi regrettin life d'in ta na baya, duniyar nan babu wani jin dadi a cikinta.

☆☆
Wani babban waje suka kai Affan bayan ya sanar musu da in da takardun suke, ido a kulle suka kaishi wajen suka rufe yana ihu yana magiya suka tafi suka barshi. Yanke shawarar barin zuwa gidan sukayi akan sae yansanda sun d'auke kafa don sunsan yanzu suna nan suna bincike akan gdan.

Bayan sun tafi Affan ya tsuguna a wajen ya saki kuka me tsanani, duk tunanin sa Aman da Mummyn sa, wane hali suke ciki shine be sani ba, ya zata abin iya kan shi da Daddy zae tsaya, sae gashi komae ya juye.

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora