Page 3

1K 84 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

             *Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMAN DEE*

27/06/2018

3.

Dan haka ba tare data  buɗe kanta daga cikin bargon ba, tace waye wanda ya gaji da duniya?..................

          Shiru Yaya Ahmad yayi ba tare daya bata amsa ba, jin anyi shiru yasa taci gaba da cewa ko waye nan bayaji ina magana? Idan fa na fito jiki zaiyi ma ko waye babu daɗi, maza maza kunnamin waƙana ka kama gabanka tun kana gane hanyar fita basai ka nemo ɗan jagora ba! Ta ƙarasa maganar cikin ɗaga murya mai amon harruffa babu adadi,

          Murmushi yaya Ahmad yayi tare da gyara tsayuwanshi ya jingina jikinsa da bango ya rungume duka hannayensa a ƙirjinsa yana kallon inda take kwance,

        Rabi'atu jin shirun tayi yawa yasa ta yage bargonta da sauri cikin ɓacin rai ta diro daga saman gadon gaba ɗayanta tayo kansa, har yanzun yana tsaye kamar yanda yayi tun a farko yana ma rabi'a wani irin kallon mai nuni da bata da hankali,

Wani irin kallo tayi masa mai nuni da zaka gane kurenka! Murmushi Yaya Ahmad yayi tare da gyara tsayuwarsa, yace kiji tsoron Allah ki gyara rayuwarki saboda mutuwa zata iya riskarki a duk lokacin da baki tunani, ajiyar zuciya yayi sannan yaci gaba da cewa!

Kiyi ƙoƙarin gyarawa, sannan kuma kiyi rayuwa mai kyau domin tsira ranar gobe ƙiyama, idan baki fita daga harkar dujalanci ba da shiga ta baɗala da kika koyawa kanki wanda wannan ba tarbiyyar gidan nan bane, sannan kuma a al'adance bai dace ba, idan kuwa akayi magana a addinance kinsan yin hakan haramun ne!

       Allahu akbar! Haka rabi"atu ta faɗa tare da cewa yaushe ka zama malami ka fara wa'azi ban sani ba? Ai da nasan zaka zama mai wa'azi da faɗin gaskiya da bansha wahalar zuwa islamiya na sauke Al'qur'ani ba, da banbawa ƙwalwata wahala ba wurin koyo hadissai da kuma ɓata lokaci wurin sanin mai kyau ko kishiyarsa, Yaya duk abinda zaka faɗamin na riga dana sani,

          Kai sai ƙwalwarka tayi tunani sannan zuciyarka ta yanke hukunci sai bakinka ya faɗa, niko ni naje na karanta na gani, kaje kayi abinda kake ganin shine mafita a gareni kaima kayi naka, murmushi yaya Ahmad yayi sannan ya juya dan fita daga ɗakin!

           Ganin zai fita yasa Rabi"atu tace yawwa ji nan, tsayawa yayi ba tare daya juyo ba yace uhum! Taci gaba da cewa sai magana na gaba dana manta ban faɗa maka ba ahine ku soke lissafi na daga cikin "ya"yan nan gidan tunda ku kuna da kamun kai ni kuma banda shi, kowa ya fita daga harkata, ɗan gajeran tsaki tayi sannan tace sai kuyi ta sani yawan magana har kaina ma ya fara ciwo, ta ƙarasa maganar cikin sassanyar murya mai kama da zatayi kuka,

Murmushi Yaya Ahmad yayi ba tare daya ce komai ba yayi gaba, ita kuma ta kunna waƙar Aashiqui_2_tum_hi_ho_ft_arijit_singh, haka taci gaba da caskaɗewa abunda,

Momy bayan ta gama shirinta na tafiya Office ɗakin rabi"a taje, har a lokacin rabi"atu rawa takeyi, ko wahala ma bataji, murmushi momy tayi tare da cewa doughter zan wuce office, da hannu tayi mata alama da ta dawo lafiya!

       Allah ya shirya momy ta faɗa tare da fita daga ɗakin ranta a jagwale dan ita kullum addu"arta bai wuce taga shiriyar rabi"atu ba, ga ilimin addini bare ta ƙira abun da jahilci, a bayyane tace ubangiji ya baki ikonyin amfani da iliminki domin gyara rayuwarki,

         Zuciyar momy cike da tunani barkatai harta fito farfajiyar gidan, malam sani ne yazo ya gaisheta amma saita ɗaga masa hannu dan batajin zata iya magana a wannan lokaci, dan zuciya tayi mata ƙunci a haka ta shiga motarta ta ja amma hankalinta kwata kwata baya jikinta,

SANADIN SOCIAL MEDIAWhere stories live. Discover now