Page 34

690 60 1
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

             *Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

08/08/2018

34.

     Cikin tashin hankali jishad ya matsa wurin yana ƙoƙarin cire resmin daga jikin Rabi"atu, daƙel yake janta dan yana ɓamɓarota take ƙara kwacewa tana komawa saman jikin Rabi"atu!

Ƙara fizgota yayi da hannu ɗaya da ƙarfin jarumta, wani irin ihu resmin tayi tare da kaiwa Rabi"atu halbi cikin kuka tace ma jishad saina kasheta wallahi,

     Idanuwa jishad ya zaro kafin yayi magana ta ƙara komawa tana dukan Rabi"atu ciki zafin rai da tsananin ɓacin rai jishad ya fizgota tare da zazzabga mata mari, da sauri ta tattara gashin kanta tare da ɗaga idon ta kalli jishad ɓarkewa tayi da kuka mai tada hankali tace ni ka mara saboda mace?

    Da gudu Rabi"atu ta taso ta ɓoye a bayan jishad tana kuka, hannunsa yasa a bayan sa ya jawo Rabi"atu rungumeta yayi sosai a jikinsa cikin birkitacciyar murya yace kiyi haƙuri,

      Resmin ta sake maimata tambayarta nika mara saboda mace ko? Eyy na mareki naje na mareki ko zaki rama ne? Da gudu Resmin ta fita tana ihu kamar mahaukaciya,

     Ƙara riƙe Rabi"atu yayi sosai a jikinsa yana ƙoƙarin haɗa bakinsa da nata Resmin ta shigo da gudu da wuƙa a hannunta, da sauri jishad ya ɗago tare da maida Rabi"atu bayanshi da sauri, ita kuma a daidai lokacin data caka wuƙar a tsautsayi ta yanki hannun jishad,

       Murmushi jishad yayi tare da kallon inda resmin ta yankeshi sannan ya ɗaga idonshi ya kalleta, amma baice mata komai ba dan yasan kishine kawai yake damunta,

       Jan hannun Rabi"atu yayi tare da ɗaukar mata rigarta suka fara tafiya Rabi"atu duk tabi ta daddafe jishad tana ƙoƙarin runtumawa da gudu jishad ya riƙeta sosai,

     Resmin kuma biyo bayansu tayi tana ta hauka a cikin yarensu wanda Rabi"atu bataji amma shi jishad yasan abinda take cewa "yar gajeriyar dariya yayi a daidai lokacin daya tsaya daidai tebirin cin abincisu ya ɗauki wata "yar madaidaiciyar food plaks,

   Suka fita a palon duk maganar da Abbu yakeyi jishad bai saurara ba, dan a gaskiya iyakar rashin kyautawa ba"a kyautawa Rabi"atu ba ai ba"a rayuwa haka,

       Saida ya saka kular a baya sannan ya sakawa Rabi"atu rigarta ya sakata a motar sannan shima ya zagaya ya shiga yaja suka fita a gidan zuciyoyin kowa a kuncice,

Da hannu ɗaya ya riƙe sitiyarin motar ɗayan hannun kuma yana rumgume da Rabi"atu dake ta faman shashshekar kuka shidai jishad bai iya bada haƙuri ba dan wani irin hali yake dashi wanda shima kanshi da kanshi yana shan wahalar kansa,

    Har suka koma masauki babu wanda yayi magana, suna shiga da gudu Rabi"atu ta wuce ciki ta fara tattara kayanta, jishad daya shiga daga baya yaga Rabi"atu tana ta faman parking da sauri ya isa wurinta ya riƙeta ta baya yace miye haka?

     Cikin kuka Rabi"atu ta juyo tace nidai tafiya zanyi bana iyawa, murmushi jishad yayi cikin sigar zaulaya yace haba keko ƙawar ango da wuri haka? Ya ƙarasa maganar yana mai ɗan ɗaga girarsa,

      Sassauta muryarsa yayi sannan yace ai baza mu sake ma komawa ba anan zanyi zamana dake babu ruwana da aurensu nidai ke nake so zaki aureni don Allah? Ya ƙarasa maganar tare da ɗan riƙo daidai ƙugunta ya ɗan fizgota sosai a jikinsa ita kuma hannuwanta a saman kirjinsa yanda yayi mata abun yasata saurin lumshe idonta a hankali,

SANADIN SOCIAL MEDIADonde viven las historias. Descúbrelo ahora