Page 16

800 58 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

             *Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

22/07/2018

16.

Saida suka gama da asibiti sannan suka shiga kasuwa dan siyo abubuwan da Rabi"atu zatayi amfani dashi a wurin party gobe,

      Siyayya sosai suka jibgo sannan suka nufo gida a gajiye, Rabi"atu bata wani tsaya taya momy cire kaya a cikin motar ba ta wuce abunta,

Mai gadi ne da mai kula da tsirran dake gidan suka kwashi kayan suka kaiwa momy ciki, ita kuwa Rabi"atu ɗakinta ta wuce wanka tayi ta fito taci abinci sannan ta koma ɗakinta taci gaba da gwada number kamal,

Ganin ta kasa samunsa yasa ta ƙara fawwala wa ranta tare da bawa zuciyarta haƙuri kamal yayi mata nisa dan haka ta haƙura,

Yinin ranar haka ta yini cikin rashin jin daɗi har dare yayi tana cikin tunani, yau kam abinda ya hana ta zuwa club bawai ganin dady ba A, a, kawai dai saboda tana hidima ne gobe,

Haka ta kwana tana tunani duk lokacin data farka cikin dare saita gwada layin kamal amma dai yaren iri ɗaya ne tun shekaran jiya ake faɗa mata shi dan haka ta haƙura,

       Da safe tunda tayi sallah asuba bata koma bacci ba, wayar Aysha ta kira ita har lokacin tana club bata koma gida ba!

         Bayan ta ɗauka suka gaisa sannan Rabi"atu tace mata don Allah ki shigo da wuri saboda shirye shirye, Aysha tace insha Allah ina club ban koma gida ba amma insha Allah daga nan zan wuto gidanku, Rabi"atu tace tou sai kinzo, Aysha tace to, sallama sukayi kowa ya ijiye wayarsa,

        Dakel ta koma bacci bayan sun gama waya da Aysha, sai 12:30pm ta farka, da addu"ar tashi daga bacci ɗauke a bakinta, agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakinta ta kalla sannan ta sauko daga saman gado a hankali ta nufi toilet,

      Ruwa ta watso sannan ta fito, tana fitowa wayarta ta ɗauka dan kiran Aysha amma sai taga miss call inta yakai 11 dan haka ta fara kiranta cikin sauri dan da zata kwanta bacci silent ta saka wayar dan ta samu bacci mai inganci,

       Saida kiran ya kusa tsinkewa Aysha ta ɗauka cikin faɗa Rabi"atu tace haba banda iskanci wai sai ayita ƙiran mutum baya ɗaukar waya, cikin sanyi Aysha tace kiyi haƙuri na kirane baki ɗauka ba, kuma abinda ya hanani zuwa gidanku kai tsaye yayunki sunce idan suka sake gani na sai sunmin duka Yaya Ahmad kuma cewa yayi saiya ƙarya min ƙafa ta baya!

    Tsoki Rabi"atu tayi sannan tace tou do Allah ni kiyi sauri kizo, Aysha tace tou gani nan zuwa da yarda Allah, kashe wayar Rabi"atu tayi tare da ajiyewa a gefen gado sannan ta fita danyi kalaci, dady yana zaune a farlo yana karatun jarida momy kuwa ta tafi Office, dan haka gaishe da dady tayi sannan ta wuce diarning area dan gabatar da karin safe,

A gaggauce tayi kalaci ta tashi a wurin dan gaba ɗaya jikinta tsimi yakeyi ta ƙagara ayi shagalin nan dan ta tabbatarwa da ƙawayenta ta samu "yancin kai dan yanzun idan ta tafi Club sai safe zata riƙa dawowa kuma tasan ko banza dole sai yaya Ahmad ya faɗawa dady a ina ya ajiye mata key in motar ta, tasan zata ƙaro sabon wulaƙanci sheganta ka kuwa yanzun zasu fara sabuwa domin yanzun zata fara chat zata shiga network idanuwanta zasu ƙara buɗewa,

       Tana cikin wannan nazarin taji sallamar Aysha daga cikin ɗaki ta amsa tare da cewa shigo mana, Aysha da zugar wasu ƙawayenta ƙyanƙyasar bariki sun kwace sosai ido ya buɗe jiki ya nuna cikin tako irin na "yan duniya suka nufi ɗakin Rabi"atu,

SANADIN SOCIAL MEDIAWhere stories live. Discover now