Page 15

773 48 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

20/07/2018

15.

Nufi babban birnin abuja..........

Rabi"atu kuwa zaune a cikin motar ta ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya sai shaƙar iska takeyi dan yau jinta takeyi kamar ammata gafara,

Ɗan gajeran tsoki tayi sannan ta ɗora hannunta saman wani kwali tare da tashi zaune ta buɗe kwalin, murmushi tayi ganin abinda yake a cikin kwalin,

Ayaba ce irin manyan nan masu kyau, dan haka cikin farin ciki ta buɗe kwalin ta faraci abunta hankali a kwance,

Tana ci tana tillar da ɓawon ayabar a saman titi, cak taji motar ta tsaya dan haka bata wani ji damuwa ba taci gaba da cin ayabarta dan yunwa takeji kamar zata mutu,

Yaron motar ne ya fara fitowa daga cikin motar da sauri ya taho dan haka yana taka ɓawon ayaba ya tafi suu...... Salati ya farayi tare da kiran Ogansa!

Da sauri ya fito daga cikin motar dan ganin me yasa yake kiransa dan sudai tsayawa sukayi shi yaron motar zaiyi fitsari,

"""Kafin ya iso wurinsa shima yaji ya taka wani abu ya tafi dashi, cikin zafin nama ya dire daga saman abinda yaji ya ɗauke sa, juyawa yayi dan ganin ko miye a daidai lokacin da Rabi"atu ta sake tillo wani ɓawon ayabar,

Salati suka farayi gaba ɗayansu dan a tunaninsu aljani a cikin motar tunda sudai sun san basu taho da kowa ba kuma basu tsaya ko ina ba sai yanzun!

Dan haka cikin dakiya yaje ya kama motar ya hau saman bodynta, Rabi"atu ya gani zaune tayi irin zaman sarakuna saicin ayaba takeyi, gashin kanta kuma ya rufe mata fuska baya ganin fuskarta saidai hannunta dake shiga cikin gashin dan tura ayaba a cikin bakinta,

Cikin tsoro da fargaba yace baiwar Allah mutum ko anjan? Ba tare data ɗago ko tace wani abu ba, tace anzo kaduna ne? A, a, zamu dai shiga nan da minti 20 idan Allah ya yadda,

Da hannunta ta masa alama da ya tafi kawai, babu musu ko gaddama ya sauka, a lokacin har yaron nasa yayo fistari ya dawo haka suka shiga motar yaja zuciyoyinsu da tunani barkatai,

Suna shigowa kaduna yace hajiya anzo, yawwa sannu driver, a daidai lokacin da take ƙoƙarin tashi, saida ta sauko daga motar sannan ta zagaya wurinsa tace na gode fa, banda Allah ya kawo man kai lallai da ina can ina ansar horo,

Yaƙe yayi wanda yafi kuka ciwo 😬, murmushi Rabi"atu tayi tare da cewa kayi haƙuri na ci muku ayaba don Allah wallahi ba laifina bane laifin "yan hanjina ne, dan ji nayi zasu tsinke saboda yunwa fatan ka yafe min ko? Jinjina kai yayi tare da cewa na yafe miki dan ya ƙagara ta tafi shi tsoronta ma yakeji,

Yawwa sauka lafiya na gode, sai anjima🙌🏻 tana faɗar haka ta juya ta tsallaka titi cikin sauri, abun hawa ta tare amma ba gidansu ta nufa ba gidansu Aisha ta wuce,

Suna tsayawa ƙofar gidan su Aysha ita kuma tana fitowa tare da wasu ƙawayenta murzajjin karuwa wanda ko a karuwanci sun ansa sunansu na karuwa, dan ko iskanci ya gansu saiya sara musu saboda "yan iska ne ajin farko,

Fitowa Rabi"atu tayi, cikin mamaki Aysha ta kalli Rabi"atu dan ita a farko ma bata ganeta ba! Saidai tayi mata kallon ƙurillah sannan ta gane ashe ƙawarta,

SANADIN SOCIAL MEDIADonde viven las historias. Descúbrelo ahora