Page 29

598 60 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

             *Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki*
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

04/08/2018

29.

Jishad kuwa ya gwada kiran Rabi"atu amma karatun ɗaya waya a rufe, baida yanda zaiyi dole yasawa ransa sawaba,

      Rabi"atu kuwa damuwa kullum sai abinda yayi gaba dan gaba ɗaya ta canja layi kan wayarta dan tun ranar da jishad yaƙi faɗawa resmin ko wace ce ita abun ya babba mata rai,

     Yanzun kam babu wani maganar zuwa club ta maida hankalinta ga karatunta duk wani abu na shirme ta tattarashi ta zubar,

Bata da wata damuwa, damuwa ɗaya wanda tafi damunta yanzun banda tunanin jishad kuma ta goge numbobinsa kuma bata riƙesu a kanta ba kuma ta duba a wayar momy babu sai yanzun ta gane lallai ta jibga baban kuskure!

      Gaba ɗaga Rabi"atu jinta takeyi kamar matacciya, dan ta tabbatar yanzun gangar jikinta da ruhinta basu da wani amfani, mutuwa itace kawai tafi cancanta da rayuwarta,

     Lallai idan de wannan shi ake kira so haƙiƙa baiyi ba, baya da wata rana da zuciya zata so mutumin da bata taɓa gani ba, mutumin da yayi nisa sosai taɓa daidai zuciyarta tayi tare da cewa gaskiya bakiyi ma kanki adalci ba,

      Kin cuci kanki kuma kin tashi aiki domin gab kike da tarwatse wa, ban baki haƙuri wallahi kuma bana rarrashinki kece kika jawo ma kanki saboda tsabagen san kai irin naki,

      Rushewa tayi da wani irin gigitaccen kuka cikin muryar kuka tace miyasa da jishad ya tambayeki kina sansa kika ce A, a? Gashi yanzun ya tafi baya sake dawowa har abadan duniya,

      Sassauta muryarta tayi sannan tace kuma kika yaudari kanki kika goge hotunan shi, da sauri ta miƙe tsaye dan jin wani abu yana biyu daga cikin maƙoshinta wanda bata san ko miye ba!

Layi ta fara yi kamar wanda tasha kwaya tayi tatul da layi ta fito taga ɗakinta tana tallabe da ƙirjinta ɗayan hannunta kuma tana dafe bango, cikin murya kamar ta "yan maye ta fara cewa ai laifinki ne ya tafi yayi miki bye bye kila sai kin mutu zaizo gaisuwa,

      Momy ta ɗaga muryarta tana ƙira, cikin wata irin murya mai tada hankali, momy dake sallah taji faɗuwar gaba dan jin muryar da Rabi"atu ta kirata dashi,

A wahalce ta zauna saman step na ƙarshe wanda tana sauko ƙafarta ta shigo palo, sabbatu tayi tayi wanda ni bana iya ganesu bare na rubuta muku su,

     Momy na sallame sallah ta fito da sauri rabi"atu ta gani zaune sai amai takeyi, subahanallah ke kuma taki lalurar da amaye amaye take zuwa?

     Kafin ta ƙarasa kusa da ita tuni ta tafi luuuuu,,, cikin tashin hankali da ɗimaucewa ta ƙarasa wurin da sauri, riƙeta momy tayi ta fara jijjigata lafiya doughter?

       Ke lafiyarki ? Doughter miye haka ne? Ai doughter bata san momy nayi ba, cikin birkicewa momy ta sauke Rabi"atu ta nufi ɗakinta cikin sauri

     Tana shiga wayarta ta ɗauka ta fara ƙiran dady babu wani ɓata lokaci ya ɗauka ko gaisuwa babu momy ta fara rattafa masa halin da Rabi"atu take ciki, faɗa dady ya farayi sosai tare da cewa yarinya tana cikin matsananci hali baza ki kaita asibiti ba sai ki tsaya kirana?

     Maza a kaita asibiti mana, da sauri momy ta ajiye waya ta fito tana kwalawa lami mai aiki kira, da taimakon Allah suka saka Rabi"atu motar momy taja suka tafi asibiti Allah yakaisu lafiya dan momy bata gani haka nan kawai take tuƙin,

A asibiti taimakon gaggawa aka bawa Rabi"atu dan ceto lumfashinta da yake ta faman kai kawo, bayan komai ya lafa momy ta tambayi likita me yake damun ɗiyarta ne?

      Likita yace su sameshi Office, bayan sunje Office wurin zama ya nuna mata ta zauna, bayan "yan rubuce rubucen na ma aikantan jinya sukeyi shima yayi nashi a saman takarda gyara zaman gilashin idonshi yayi sannan yace hajiya kwantar da hankalinki,

      Da ido momy ta tsareshi, shi kuma yaci gaba da cewa ba wata damuwa bace ɗan tunane tunane take sakawa ranta idan ta daina zata zauna lafiya idan kuma bata daina ba zata iya jefa kanta a matsala Allah ya kyauta,

   Amin momy ta faɗa, doctor ya bama momy wata "yar takarda yace magunguna ne a nemo su, ansa momy tayi ta fita ba tare da tace dashi komai ba, dan ta lura ɗan iska malamin jinya ne komai tsaye yake faɗa a mutu ko rayuwa,

      Tana fita ta bawa lami kuɗi da takardar tace ta samo wannan maganin, ansa tayi cikin girmamawa ta tafi, ita kuma momy ta koma ɗakin da aka kwantar da Rabi"atu,

      A takaice dai kwanan rabi"a biyu a asibiti aka sallamesu tare da bawa momy shawarwari dan ganin Rabi"atu ta kaucewa faɗawa matsala,

      Ahmad kuwa ya kira momy an haɗashi da Rabi"atu yayi mata tatas yace tunda yake a duniya bai taɓa ganin mahaukaci irinta ba, soyayyar ƙarya soyayyar SOCIAL MEDIA, idan ma banta take daƙiƙiya uban waye yake soyayya da mutumin da bai sani ba,

       Cikin sanyi tace Yaya nifa ba soyayya nake dashi ba, kawai ina tunanin sa, Ahmad yace banza wannan ai shine so, an faɗa miki indiayawa suna auren wanda ba yarensu ba? Mahaukaci ya rainaki yana can ya manta da lamarinki, saboda daƙiƙanci kina ganin ita wannan sakarar ƙawar taki { Aysha }

      *SANADIN SOCIAL MEDIA* ta samu ƙawa ta lalata mata rayuwa ta gurɓata mata tarbiyyar da iyayenta suka bata, har tayi nasara wurin ɓata taki tarbiyar,

Ke kuma naki lissafin soyayya saboda doɗewar basira, goge hawayen idonta tayi sannan tace yaya ai well come back in layika na zanyi nasan zai kirani, kinji wani jakkancin kuma ana faɗa miki rashin fa"idar abun kina nema ƙara mayar da kanki ruwa, ƙasa ƙasa yayi da murya sannan yace yarinya kiyi haƙuri ki goge wannan ɗan iskan a ranki kiyi addu"a ubangiji ya baki miji na gari,

    Nidai wallahi bazan yi haƙuri, ke Rabi"atu saurara a faɗa miki ko a bari duniya ta faɗa miki? Ki manta da wannan jishad in ƙarya kindai ji na faɗa miki,

      Tsoki Rabi"atu tayi tare da kashe wayar, miƙawa momy wayarta tayi tace wallahi saina yi well come back layikana nasan wata rana jishad zai nemeni, ita dai momy bata ce komai ba ta fice daga ɗakin,

    Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya kwanci tashi asarar mai rai kullum Rabi"atu babu tunani saina jishad ta shige ɗaki ta rufe tayi ta kuka abinci ma wahalar ci yake mata ga ɗaya tabi ta kakkaɓe tayi duhu,

Momy tayi rarrashi da ban magana har ta gaji ta fita harkarta, ita kaɗai take rayuwarta tare da tunanin jishad duk daren duniya idan zatayi bacci,

     A ɓangaren jishad kuwa kullum da tunanin Rabi"atu maƙale a zuciyarsa idan bai manta lissafin ba yau kusan 7mouths rabonshi da ita, lallai ya zamar masa dole ya nemo Rabi"atu dan tayi masa alƙawarin zuwa bikinsa kuma gashi lokaci ya ƙarato,

     Lallai yayi alƙawari yau ko zai mutu sai ya kira wayar momy, danshi tun lokacin da yake kiran Rabi"atu baya samu yama daina tunanin kiran wayarta kwata kwata amma a daren yau saiya raya zuciyarsa da jin muryar Rabi"atu, addu"arsa ɗaya kada Rabi"atu ta ɗaukesa mai ƙarya,

SANADIN SOCIAL MEDIAWhere stories live. Discover now