Page 14

751 56 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

20/07/2018

14.

Gadai yanda Rabi"atu take cewa idan taji an taɓo aya mai zafi, saidai ta sulale ƙasa tayi ta muɗiɗɗika kamar an watsawa maciji ruwan zafi,

Cikin murya dai ta irin wanda ake fitarwa aljannu ta fara cewa, a saurara a saurara tana ɗaga hannunta alamar a jira,

Da sauri Ahmad ya matso sosai kusa da alaramma yace malam ci gaba kada ka sake ka saurara don Allah, baiwar Allah ashe aljannu ne suka shigar mata a jiki suke ta fitar da ita baiwar Allah,

Ɗan buɗe idanuwa Rabi"atu tayi tare dayin hamdala a ranta jin Ahmad ya yadda tana da aljanu dan haka tace kowa ya cire hularsa idan ba haka ba aradu cikin rawanin alaramma zan shige..........

A lokaci ɗaya gaba ɗayansu kowa ya cire rawanin sa ya ajiye ƙasa, saida tayi wani irin gurnani sannan taci gaba da cewa su waye cuke tukanmu? Ta ƙarasa maganar tana kallon inda Ahmad yake zaune,

Kallonta Ahmad yayi sannan yace nine nan kuma ko yanzun ma idan baku fita ba wallahi saina zane ku! Murguɗa baki Rabi"atu tayi sannan tace ai ce ka fugemu a banza cunda zamewa daga jikinta zamuyi kayi ta dukan ƙanwarka mu ina yuwanmu?, ta ƙarasa maganar tana hararar Ahmad!

Kai haka dai aka yini ana abu ɗaya Rabi"atu tana iskanci san ranta, kuma tayi alƙawari idan ba"a barta take zuwa inda ranta yake so ba, tou lallai zata ɗauki Rabi"atu ta tafi da ita bayan duniya.....,

Abun yayi wa Ahmad ciwo dan duk Rabi"atu ta gajiyar dasu tashi yayi ya ɗauki wata zabgegiyar dorina yaci gaba da dukan Rabi"atu babu ji babu gani a zuwan aljana yake duka,

Rabi"atu jin zata mutu yasa tace zamu tafi zan fita, Ahmad bai saurara ba, jin azaba tayi yawa yasa ta faɗi ƙasa tare dayin wata irin jiniya irin dai yanda aljannu sukeyi idan zasu fita daga jikin bil adama,

Ajiyar zuciya Ahmad yayi cikin yanayin gajiya yace shegu kai ai da idan zaku yini Ahmad yana kwana ba tare daya gajiya ba....,

Jan Rabi"atu yayi zuwa cikin ɗakin da yake ajiyeta, bayan ya shigar da ita ya kulle ƙofar ɗakin, gaba ɗayansu suka fita daga gidan......

***
***

Bayan sati biyu,
Tunda safe momy ta tashi dan tunda tayi sallah asuba bata koma bacci ba! Sai gyare gyare takeyi, saidai ta kakkaɓe can ta goge can, saida ta ɗauki awanni masu yawa tana gyare gyare ba tare data zauna ba!

Bayan ta hattama ta nufi kicin anan fa ta zuge dan yiwa mai gidanta dake shirin dawowa yau ƙayataccin girke girke, wanda zaci yasan ya dawo gida....,

Abinci iri iri momy ta girka, bayan ta gama ta jujjuye ta fara ɗaukowa haka tayi ta jidowa daga kicin tana zuwa farlo haka tayi ta jera jibga jibgan food flarks a saman diarning table,

Bayan ta gama ta koma ta gyara kicin inta, bayan ta gama ta nufi ɗakinta danyin wanka, tana fitowa babu ɓata lokaci ta zuge cikin shiga mai tsabta dan momyn "yar gayun ƙarshen zamani,

Ƙamshi ta ƙara sakarwa gidanta gaba ɗaya gida ya ɗauki ƙamshi sosai, saida ta tabbatar komai ya zama daidai sannan ta ɗauki wayarta dan kiran dady ta mishi ya hanya,

SANADIN SOCIAL MEDIADonde viven las historias. Descúbrelo ahora