Page 23

656 53 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

             *Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

30/07/2018

23.

       Rabi"atu mi yayi zafi haka kamar dai kina jirana? Daga magana sai zagi? Kifa duba abun duka bai kai haka ba amma kin zafafa idan dai har tayi miki zafi tou kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki,

      Tsoki tayi bayan ta gama karantawa tace ba zafi tamin ba tasafa nayi kuma rabuwa da ƙawar SOCIAL MEDIA karki rabu can matsalarku daƙiƙai masha "yan iska ma irin ku,

         Koda ta gama karantawa bata bawa Aysha ansa ba dan bata da lokacinta, ajiye wayarta tayi ta shiga sabgogin gabanta,

         ***

Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin Rabi"atu da jishad shaƙuwa sosai ta shiga tsakaninsu wanda duk wannan tarayyar suna ganinta a matsayin abota ce,

       Zama da jishad yasa Rabi"atu ta fara iya ɗabi"u da kuma al"adu irin na indiawa domin shaƙuwa bata wasa sukayi da jishad ba, wanda babu mai iya kai wani lokaci ba tare da yayi magana da ɗan uwansa ta chat ko waya,

      Maganar club kuma yana ƙoƙari wurin ganin ya hanata zuwa amma abin ya shiga jikinta sosai dan jishad ya lura abin dai sai a hankali zata rabu dashi amma badai rabuwa ta lokaci ɗaya ba!

      A ɓangaren momy ta lura Rabi"atu ta rage rawar kai gaskiya kuma taji daɗin haka sosai tana ta ƙara addu"a sosai wannan abun farin ciki har Ahmad ta faɗawa,

     Aysha kuwa tayi iya iyawarta su shirya da Rabi"atu amma ina Rabi"atu ta nuna mata ita jar wuyace, dan tama manta da lamarin wata Aysha banza,

    Ko a club suka haɗu haka Aysha zatayi ta binta amma Rabi"atu ko kulata batayi dan gaba ɗaya ma haushin Aysha takeji,

    Ko dady da yazo yaga Rabi"atu ta fara hankali shima yaji daɗi yayi farin ciki sosai yana ƙara addu"a sosai Allah ya shirya,

        Zaune take a palo saman kujera wayarta maƙale a kunnenta tana cewa, don Allah nidai ka barni na fita wayyo Allahna, ta ƙarasa maganar cikin sigar sagwaɓa sosai,

     Murmushi jishad yayi sannan yace nifa nace bazaki fita ba idan kuma fitar zakiyi tou mu gani, saida tayi "yar ƙaramar jiniya sannan tace nidai gaskiya saina je,

    Rabi"atu ni kike cewa sai kinje? Eyyy ta faɗa tare da murguɗa bakinta kamar jishad yana kallonta, ni ko? Eyy nace sai naje, tou babu damuwa Allah ya baki haƙuri a sauka lafiya idan kin dawo kimin magana, ba tare data bashi amsa ba ta kashe wayarta,

       Shirinta tayi, tayi ficewarta daga gida saida tasha casunta mai isarta sannan ta dawo gida, bata kira jishad ba kuma batayi chat dashi ba, shima ido ya sa mata bai kirata ba kuma koda yaga tana online baiyi mata magana ba!

     Haka suka share kusan wata ɗaya babu wanda yayi ma wani magana, itace ta gaji da gabar tayi masa magana a chat,

                             _Assalamu alaikum_

_Wassalamu alaikum_

                           _Ya kake?_

_Shiru_

                             _Friend ya kake?_

_Shiru_

                              _Ya resmin?_

_Shiru_

                  Tayi magana takai goma amma idan jishad ya gani saiya basar gashi fa ya gani amma baya bata amsa,

          Wannan abun yayi ma Rabi"atu baƙin ciki dan haka tayi wani irin ihu tare da kwaɗa wayarta a ƙasa, ta fara kuka sosai wanda ihunta yasa momy fitowa daga ɗakinta da gudu,

Amma tana taɓa ƙofar ɗakin tajita rufe ruff, ga Rabi"atu a ciki sai kuka takeyi kamar ranta zai fita,

      Dukan ƙofar ɗakin ta farayi tare da cewa daughter buɗe mana, wai miye haka ne Eye? Buɗe buɗe kinji auta, ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi!

          Ina Rabi"atu kuka takeyi babu ji babu gani, dan ta tsani a rayuwarta tayi magana ayi mata shiru, momy tana nan tsaye taji ƙarar fashewar abubuwa masu glass duk wani abu daya danganci hannu zai iya fasawa Rabi"atu saida ta ɓarar dashi a ɗakin nan,

        Sannan ta koma gefe ɗaya ta zauna tana mai ci gaba da kuka a hankali mai kama zuciya, momy ta rasa yanda zatayi dole ta haƙura ta koma ɗakinta,

       Har gari ya kusa wayewa Rabi"atu bata daina kuka ba kuma bataci abinci ba, ita ta kasa ganewa miye ma take wani tada hankalinta akan jishad ɗin banza? Wata zuciya ta gargaɗeta da ta daina cewa na banza,

     Ganin ta kasa samun sassauci yasa ta haƙura ta tashi tana laye kamar sabuwar "yar maye ta tafi tangal tangal gaban wayarta ta durƙusa ta ɗauki wayarta data tsastsage ta ɗauka a hankali ta koma saman gado ta zauna saida ta goge hawayen idonta sannan ta fara ƙiran wayar jishad,

         Haka tayi ta kira amma jishad bai ɗauka ba, ta koma chat ta tura masa saƙo yafi a irga amma babu amsa, haƙura tayi ta barshi,

Bayan wasu kwanaki masu dama duk wanda yaga Rabi"atu yasan tana cikin damuwa dan gaba ɗaya ta canja launi, ta rame tayi duhu, bata cin wani abinci kullum tana ɗaki a kulle kamar matar mamaci, duk mai imani idan yaga Rabi"atu sai ta bashi tausayi,

       Kullum tana ƙoƙarin kira amma jishad baya ɗauka, momy tayi rarrashin duniya amma ta gaji ta haƙura, yau kam tana ƙoƙarin rubuta masa saƙo,

          
                             _Friend don Allah me nayi maka?_

                         _Kayi haƙuri don Allah, kada ka manta kace na zama mai martaba abota, na zama mai riƙe alƙawari kuma ban saɓa alƙawari ba mi yasa kai ka karya?_

_Shiru_

                    _Tou babu damuwa, nidai na baka haƙuri kayi haƙuri ka yafe min, nasan nice ta farko dana fara tura maka da saƙon gaisuwa, ina neman yafiyarka ka yafemin....._

_Shiru_

                       _Daga ƙarshe ina maka fatan alkairi ka dawwama cikin farin ciki da nishaɗi, na barka lafiya......_

       Typing... jishad ya fara wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar Rabi"atu lallai da tasan abinda ake cewa so haƙiƙa da tace son jishad takeyi amma ita a ganinta babu wani soyayya ko ɗaya kawai dai sabo ne da tayi dashi wanda dama ko mutuwa sabo ne akema kuka,

    Ta kasa ɗauke idonta a wayar tana jiran saƙon jishad ya shigo,........

SANADIN SOCIAL MEDIADonde viven las historias. Descúbrelo ahora