Page 4

971 76 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

             *Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukar gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

29/06/2018

4.

Saida ta sauke glasis in jikin window toilet tsaff sannan tayi dariya ganin hanyar da zatabi ta wuce ta buɗe,

    Jiki na kyarma tabi ta window ta fita, tana ganin ta fice a hankali ta dawo cikin toilet in cike da farin ciki tayi wani irin tsalle tare da dunƙule duka hannayenta tace yeccccccccch,

             Da gudu ta fito daga toilet tana rawa tare da raira "yan guntuwar waƙa tanajin daɗi sosai a cikin ranta, tana fitowa jikinta har tsumi yake dan wannan farin cikin lallai ta danganawa ranta dole sai taji waƙa,

Dan haka ta kunna waƙar dake ɗauke a bakinta, tanayi tana rawa tare da tsantsarawa jikinta ado, bayan ta gama shafa ta ɗauki kayanta ta zuge kamar yanda ta saba ɗaukar ado!

             Bayan ta gama ta ɗauki duk wani abinda tasan zata buƙata, stool ta ɗauka ta nufi toilet dashi,

       Glasis in data kwanto daga jikin window ta jera su akai, sannan tabi ta window ta fice, tana fita ta samu wata kujera ta taka ta kaso glass in ta fara jerasu kamar yanda suke a farko,

    Tana gamawa ta kama hanyar fita kanta tsaye takeyin tafiyarta ba tare da jin shakku tsoro ko fargaba,

Harta fita daga gidan babu wanda ta gani ko ya ganta dan bada moter ta fita ba, bata san inda makullin yake ba tun dukan da aka mata a safiyar jiya, babu waya ba makullin moter,

     Tana fita napep ta tare sai gidansu Aisha, a ƙofar gidan taga mutane suna fitowa, bata wani ji damuwa ba ta nufi hanyar shiga gidan gadan gadan........

Da sallama ta shiga cikin gidan, Aisha dake daga cikin ɗaki taji sallama Rabi"atu ta fito da gudu tare da rungume ta, a hankali ta ɗago dan kallon idon rabi,a amma sai tayi tozali da fuskar Rabi"atu duk an kwamtseta

        Haɗari kikayi? Ta faɗi maganar cikin nuna damuwa, murmushi rabi tayi tare da cewa miya faru naga gidanku mutane suna fita? Ta tambayeta ba tare data bata amsar tambayar da Aisha ta mata ba!

Murmushi Aisha tayi tare da cewa wai tsohon gidanmu ne aka ɗan gogeshi da moter, subahanallah Rabi"a ta faɗa cikin nuna damuwa da tashin hankali yana ina ta faɗa a ruɗe?

    Aisha tace ummm tare dayin ɗan gajeran tsaki cewa tou yana can ɗaki aka ajiyeshi shima tsoho ya cika taurin rai ya buɗa kawai ya wani tsaya  kwakwar tsiya ni banma ga bura'ubar dazai tsinta a duniyar nan ba danni dai wallahi kona samu kuɗina bazanyi wani wahala dashi ba nima takaina nakeyi in samu in tara kuɗin da za"asha lemo da shinkafa dan bazai yiwu ba in tara mutane wurin zaman gaisuwa ayi ta ɗirkaka musu tuwo kamar tumakai ba!

      Da sauri Rabi"a ta zare glashin idonta tabi Aisha da wani irin wulaƙantaccen kallo mai nuni da kin halaka,

Ɗan taɓe baki Aisha tayi tare da ci gaba da cewa kinji wani iri ko? Ta ƙarasa maganar tana mai ɗagawa Rabi"a gira ɗaya, har yanzun Rabi"a, kallon Aisha takeyi kallon mai nuni da Aisha ta samu warwarewar tunani,

Aisha taci gaba da cewa ni babban baƙin cikina ma gidan nan sai yaci buhun siminti huɗu, to ko sayen yashi maginin ma cewa saidai a ajiyemin tifa ɗaya, ni banma san bokitin fenti ya tashi ba, kuma lallai gidan nan zai iya haɗiye bokati biyar a tunani na haka na ƙiyasta,

SANADIN SOCIAL MEDIADonde viven las historias. Descúbrelo ahora