Page 19

730 56 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

26/07/2018

19.

Shiru Rabi"atu tayi tare ƙurawa wayarta ido tana kallon chat in mamaki ne kwance a fuskarta, tama rasa abin cewa dan gani takeyi ma jishad ya rainata, duk wanda ya ganta dai yasan ita musulma ce,

Kuma a cikin arna babu suna Rabi"atu bata taɓa ji ba amma wai kamar ita da iliminta da addi"ninta jishad yake cewa wai yayi mamaki da nace masa ni musulma ne, ai duk wanda ya ganni yasan ina da banbanci da ɗiyan arna,


Hawaye taji ya ziraro mata daga cikin kwayar idonta, haƙiƙa duk wayewar da bata musulinci ba lallai ta zama daƙiƙanci, lallai wayewar zamani halaka ce!

Tana bahausa cikakkar bahausa, iyayen ta musulmai ta tashi a cikin addinin musulinci kuma shi ya reneta iyayenta suka ginata da ilimin addini tun tana ƙarama har girmanta wai yau ita ba'indiye zaice mata bai yadda musulma bace,

Sauka tayi daga online jiki a sanyaye ta ajiye wayarta a gefe, tunani ta shiga yi har na tsawon wasu lokutta, murmushi tayi tare dayin magana a bayyane cewa aidai tsoron Allah a zuciya yake can kai ta matsewa nidai Allah ya sani musulma ce tunda ma ina sallahta abuna,

Fara kwaikwayon maganar jishad tayi kamar a gabanta yayi magana bayan fa cht sukayi, saida ta yatsina fuska tare da ɓata bakinta kamar tasha wani abu waishi ba daɗi....,

Lallai nasha mamaki da kika ce min ke musulma ce! Kuma na ƙaryataki, dubi tulin attach in dake bisa kanki, kalli fa, kalli kalli haba, haba haba........

Miƙewa tayi tare da cewa ɗan rainin hankali, da gunguni ta shega toilet har tayo wanka ta fito mita takeyi tare da tisa zancen kamar wanda aka cinyewa haƙƙin gado ta,

Agogo ta kalla tare da maida hankali wurin shiri, tanayi tana cewa ai suma indiawan ai munsan komai suma suna saka gashin doki ba munsan duk karyar banza bace har man bilicin suke shafawa,

Haka kawai haɗuwar SOCIAL MEDIA ka nemi ka wani mayar dani ƙaramar yarinya, bama sai na sake chat ɗin dakai ba zaka sake raina ni?

Bayan ta gama shafa jikin wadrof ta matsa ta fara duba kaya, murmushi tayi tare da zaro wasu matsaccu, fitinannu, sheɗanu, halakakkun ɓadda tunanin mai shirin sakawa,

Haka ta zuge abunta, tare da sakin gashin kanta a jikin madubi ta matsa cewa wai wannan gashin ne na attach? Baka san gashi na bane ba,

Wayarta ta ɗauka tare da ficewa daga cikin ɗakin da sauri, aikin dai ɗaya ne fa, dan tsayawa in faɗa muku cinye feji ne, sai 12:39am ta dawo gida, yau kam babu wata gajiya a jikinta ko bacci a cikin idanuwanta,

Wanka kawai tayi ta shirya cikin kayan bacci, sannan ta fita daga ɗakinta dan yunwa takeji tana kartar mata hanji, kicin ta nufa ta dafa indomie bayan ta gama ta zuwa a flet, ɗakinta ta koma taci tare da korewa da ruwan lemu mai sanyi!

Tana zaune a ƙasa saman kafet ta miƙe kafafuwanta ta ɗan ɗora hannunta a gefen gadonta, wayarta ce riƙe a hannunta da mata riƙon mutunci da hannu biyu,

Murmushi tayi a lokacin data ga saƙon jishad, buɗewa tayi ta fara karantawa kamar haka,

_Har yanzu bakiyi bacci ba?_

SANADIN SOCIAL MEDIATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang