Page 5

848 69 0
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊


💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝

             *Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_

*Follow me on wattpad @ meelatmusa*

*Kulli nafsin za"ikatl maut......., innalillihi wa"inna ilaihir raji"un, ina miƙa saƙon ta'aziyyata a gareki NUSAIBAH UTHMAN, Allah ya jiƙan baba ubangiji yasa ya huta, Allah yakai rahma kabarinsa, ubangiji ya baku haƙurin rashin sa Allah ya albarkaci abinda ya bari, ubangiji ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gaskiya, mu kuma Allah ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo*

*FATIMA MUHAMMED Allah ya raya baby yasa cikon addini ne, Allah ya baki lafiyar shayarwar dashi am3n*

*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*

01/07/2018

5.

Kamahlllll...............Asha shagali lafiya..............

Da "yar rawarta ta juya tana takawa irin rawar "yan duniyar nan kamar kwarto ya samu matar matacce, haka taci gaba da iskancin rawarta harta koma cikin club ranta fayau kamar ta kashe kishiya!

          Rabi"atu kuwa a gaban mota sai ciccira idanuwa takeyi kamar tayi sata a gaban sarki!

Kallo ɗaya kamal yayi mata ya ɗan gauda kansa domin shi ɗin jugunan ɗan bariki, kuma ya iya yiwa mace hajiji harsai ya kwaɗata ƙasa,

      Ita kuwa abinka da ba saban ba sai irin kakkame jikinta takeyi kamar dai ɗan kauye ya shiga jirgi,

       Hajiyata yadai? Duk kin wani kama ko ina kin tsutsuke sai kace zan wani ciccinyeki ya ƙarasa maganar yana mai matsawa kusa da fuskar Rabi"a yaɗan buɗe bakinsa,

             Tsarrrr taji a jikinta duk tsikar jikinta ta mimmiƙe, murmushi yayi tare da ɗan ɗora harshensa a leɓonsa na ƙasa yaɗan riƙeshi da haƙoransa yana mai kashe mata ido ɗaya,

Murmushi rabi"atu tayi a ranta, amma a fuskarta murtuke take kamar hadarin tsakar dare, mayaudarin murmushi kamal yayi tare da miƙa hannunsa ya taɓo hannun rabi"a,

           Ɗaga idonta tayi ta kalleshi cikin yanayin fushi amma sai ya basar cewa swry! Hannuta riƙe a hannunsa yaci gaba da driving ba tare da wanin su ya sake cewa komai ba har suka iso ƙofar gidansu,

      """Ajiyar zuciya kamal ya sauke mai bin ɓargon jikin wanda yaji, a kasalance ya kwantar da jikinsa a site in moter ya lafe kamar ƙadangare yahau bango mai manja, amma har zuwa wannan lokaci hannun rabu"atu yana a cikin nasa!

      Ƙoƙarin buɗa motar rabi"atu ta farayi, amma sai taji ta a lock, kallon kamal tayi tare da cewa buɗemin mana, murmushi yayi mai sauti sannan yace duk wahalar nan da nasha nufikinki a haka zaki barni?

      To na gode rabi"atu ta faɗa a taƙaice, murmushi kamal yayi sannan yace ai ba haka a keyin godiya ba, ɗaure fuska tayi sannan tace kowa na duniya yasan abinda kalmar na gode take nuf.....

Bata gama rufe bakinta ba taji kamal yaɗan rungumo ta jikinsa a daidai kunnenta yayi mata raɗa wanda bazan iya jiyo abinda yace mata ba, bayan ya ɗago ne ya kalli cikin kwayar idonta tare da sauke kwakwkwaran ajiyar zuciya wanda haka yayi sanadiyar mutuwar jikin rabi"a ji tayi kamar an zare mata lakkar jikinta,

     Buɗe mata murfin motar yayi yana murmushi tare da cewa to ki huta gajiya kinji zuciyata ya ƙarasa magana yana mai dafa ƙirjinsa, jiki a sanyaye Rabi"atu ta fita ta fara tafiya cikin rashin ƙwarin jiki,

     Murmushi kamal yayi ganin yanda Rabi"atu take tafiya, dariya yayi sosai tare dakai dukawa sitiyarin motarsa yabar ƙofar gidan zuciyarsa na masa saƙe saƙe sosai akan Rabi"atu dan ya lura ita lusara ce!

   Jiki babu ƙwari Rabi"atu ta isa ƙofar gidansu, a gajiye takai hannunta ta taɓa ƙofar amma sai tajita rufe ruff, ƙara turawa tayi taji da gaske rufe take sosai, cikin tashin hankali ta ɗago da kanta ta kalli agogon dake ɗaure a tsintaiyar hannunta 3:02am,

      Ɗan zaro ido tayi da sauri ta juya ta nufi ta bayan gidansu, daidai saitin BQ ɗin gidansu ta tsaya da akwai wani babbar kwata ne a wurin an giggita rodiner amma sunɗanyi wara wara dan haka cikin rawar jiki ta fara turniƙa kanta, ganin bazata wuce ba yasa ta ɗauko wani ƙaton dutsi ta fara duka summun buƙmun!

        Sai 03:55am ta samu ta buɗe hanyar data iya wucewa, da sauri ta ajiye dutsen a can gefe sannan tabi ta wurin ta shige cikin gida, tana shiga wani samu wani katako ta rufe wurin ta danne da babban dutse,

Da gudu take wucewa ciki, har ta isa ta bayan toilet in ɗakinta, cikin rawar jiki ta fara zare glasis ɗin addu"arta ɗaya kada momy ta ganta a wannan daren yama zata faɗa mata? Daga ina zatace ta dawo? Duk wanda ya ganta a wannan lokacin lallai babu abinda zai hana baza ace mata "yar iska ba!

A haka tayi ta tunani harta gama zarewa, bayan ta gama da sauri tayi ƙundun bala cikin toilet ɗin, murmushi Yaya Ahmad yayi jin shigowar Rabi"atu a daidai lokacin daya ɗaga kansa ya kalli agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakin 04:05am, jinjina kansa yayi alamar zata ci ubanta,

     Tana shigowa ta maida glassan yanda suke, sannan ta cire kayan jikinta ta fara wanka, Yaya Ahmad yace lallai yariyar nan kinfa zo da rainin hankali,

      Banjam banjam tayi wankanta tana gamawa ta ɗauki towel ta ɗaura ta nufo cikin ɗaki sannu da zuwa haka Yaya Ahmad ya faɗa, ɗan yatsina fuska Rabi"atu tayi tare da wucewa kamar bata ganshi ba,

        Jikin wedrof ta tsaya, zuwa wani lokaci ta fiddo da kayan baccinta ta koma toilet ta saka sannan tazo ta baza towel in a jikin ƙofar toilet in ta ja ta rufe,

  Tana ƙoƙarin hawa saman gado Yaya Ahmad ya sauko inda Rabi"atu take kwance ya kamo ƙafafuwan ta ya jawota ƙiyyyy hakan da yayi ne yayi sanadiyar  faɗowarta ƙasa feff, wani irin ihu ta saki sakamakon buguwar da tayi sosai,

        Innalillahi wa"inna ilaihir raji"un momy ta faɗa dan jiyo ihun rabi"atu da tayi a cikin bacci, kafin ta gama buɗe idonta taji kukan ya ƙaru sosai dan yafi na farko jin hakan da saurin ta, ta sauko daga saman gado tayo ɗakin dan ganin ko lafiya............................

Ihu take sosai dan tun tana ƙoƙarin rama duka wurin Yaya Ahmad har ƙarfinta ya ƙare saboda duka yake mata bana wasa ba ko ina na jikinta zane sa yake kuma shigar sauri yake ma fatar ta, dan kafin ta sosai wani wurin belt inshi ya sake shigewa wani sashen,

      Momy tayi iya bakin ƙoƙarinta ta karɓi Rabi"atu amma ta kasa, dan haka a ruɗe ta fito tana cewa a kawo mata ɗauki Ahmad zaiyi kisan kai saboda shi zuciya yake dashi kuma bai iya ɓacin rai ba dan in yana cikin fushi saidai a mutu, wannan dalili yasa hankalin momy yafi jirgin sama tashi, dan dukanshi yana yi yana dirdira mata ne, cikin tashin hankali momy jikinta har kyarma yake take kiran sunan fadeel......................

SANADIN SOCIAL MEDIAWhere stories live. Discover now