Abinda ake gudu
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 1
Batul Mamman💖
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Daki ne cike da 'yan mata sai hayaniya suke yi. Wasu suna saka kaya wanda ya kasance atampa ce ja mai adon baki, wasu kuwa kwalliya suke yi a gaban madubi. Wadanda basu sami wuri a gaban madubin ba da na jikin hodarsu suke amfani ana ta fentin fuska cikin nishadi.
Suna wannan hirar da shewa wata mace da bazata wuce shekaru talatin ba ta shigo da katon cikinta ita ma irin atampar jikinsu ta saka tayi kwalliya daidai gwargwado cike da damuwa ta soma magana.
" don Allah kuyi sauri ku fito ku ake ta jira. Umma sai fada take min babu amarya babu kawayenta. Kun dai san tayi ta kashedi akan African time".Wata cikinsu wadda da alama ta gama nata shirin tace "kiyi hakuri Anti Shema'u yanzu zamu fito".
"Babu wani yanzu zaku fito. Ina Asma'un?" Ta fada tana dube dube.
Can gefen gado ta hango kanwar tata ana rangada mata kwalliya irin ta amare tayi kyau sosai. Kusa dasu Shemau ta koma ta sake nanatawa mai kwalliyar tayi sauri ta gama a fito da amarya. Ita dai Asma'u har yayarta ta gama magana bata ce komai ba saboda kada ta bata kwalliyarta. Wannan rana ce mai matukar mahimmanci a rayuwarta. Ranar kamunta da mutumin da take ganin tamkar babu irinsa a duniya.
Har Shema'u ta fara tafiya tayi saurin dawowa da sauri ta sake kai idonta gaban rigar jikin amarya. Daure fuska tayi " duk amaryar duniya idan ana bikinta rama takeyi saboda zulumin barin gida da sabuwar rayuwa banda ke Asmau. Dubi yadda rigar nan ta sake matse ki duk kirjinki ya fito ta sama".
Hannu Asmau tasa ta rufe jikinta saboda yadda 'yan uwa da kawayenta na dakin suka maido da kallonsu gareta. Shemau ta cigaba da magana "ki tabbatar abinda zaki yafa ya rufe miki kirji don bani da amsar bawa Umma idan ta fara fada." Daga nan ta fice tana mamakin irin wannan jiki na kanwarta. Dama can ita mai jikin kiba ce....
******
Farfajiyar gidan ta gama cika da mata inda aka kawata wani bangare da ado irin na gargajiya domin zaman amarya. Ga kujeru da tebura wurin yayi kyau sosai harda turaren wuta na tsinke da na garwashi aka kunna sai kamshi ke tashi.Mai gabatar da taron mace ce ta nemi kowa yayi shiru saboda amarya zata fito. Mai kida ya canza salon kidansa da wanda ya dace da amarya aka fara ita da kawayenta suka fito suna taku daidai.
Sunyi matukar kyau da burge mutane da irin salon fitowarsu. Aka dauki tafi, masu hoto kuwa na camera da na waya suka fara aikinsu. Haka suka rinka tafiya har suka karasa inda zata zauna. Autarsu ce Aina'u 'yar kimanin shekaru sha uku a tsaye da mafici irin na kaba yayarta na zama ta soma yi mata fifita a hankali. Hakan ma ya kayatar da mutane.
Hajiya Bara'atu dake zaune cikin 'yan uwanta da kawaye har 'yar kwalla sai da tayi. Gashi cikin ikon Allah karo na biyu kenan da zata aurar da daya daga cikin 'ya'yanta. A hankali tace " Allah Ka jikan Alhaji" bai rayu yaga auren 'ya'yansa ba bare yaga jikokin da suka fara tarawa.
Daga nan fa aka soma shagalin biki inda aka bukaci dangin ango su fito domin kamun amarya. Suna tahowa Asma'u ta bawa Walida aminiyarta wayarta ta rada mata a kunne ta dauketa a hoto idan ana fesa mata turaren kamun. Walida tace "uhmm su Asmau an iya soyayya. Nasan sarai Abubakar zaki turawa".
Asmau ta juya ido tana fari "ke kuwa an hana bawan Allah ganin iyalinsa dole na taimaka masa da hoto". Dariya duk suka yi sannan aka cigaba da biki.
******
Ana soma kiran sallar magriba aka gama taron shiyasa dama Haj Bara'atu ta rinka nanata musu banda African time. Sallah aka tafi a gabatar harda amarya wadda ta gaji sosai. Dakinta suka nufa ita da kawayenta suka yi tasu sallar. Tana idarwa aka fara yi mata tayin abinci, kafin a kawo ta dauki wayarta ta turawa Abubakar hotunan kamu.