57

5.3K 316 7
                                    

ABINDA AKE GUDU🙆🏽57

Batul Mamman💖



Washegari garau ta tashi kamar ba ita ba. Sai a lokacin hankalin Col. Ishaq ya kwanta ya ce lallai wani satin ta huta har ta kara samun lafiya.

Sun cigaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ya karbo mata form din Jamb suka cike tare sai jiran lokacin jarabawa. Bayan sati daya Walida ta kirata ta sanar da ita zata kawo mata ziyara da neman shawara. Dadi ya kama Asmau  ta shiga dakin Jikamshinta ta fada masa ta same shi ya mike akan gado yana baccin gajiya ko uniform dinsa bai iya cirewa ba. Daga taje ta zuba masa abinci kafin yayi wanka sai bacci. Asmau ta tsaya tana kallonsa cike da tausayi. Babu abinda baya wadata su dashi ita da Amatullah. Ji tayi a ranta inama zata haifa masa da ko 'ya mai kama dashi. Yana da tsayi da girma kana ganinsa kaga soja. Bata gajiya da kallon mijinta abin alfaharinta, komai nasa yayi mata. Fuskarsa kullum bata rabo da yi mata murmushi, idan kaga ya hade rai to yana wurin aiki ne. Amma duk da haka mutanen dake karkashinsa suna yabonsa da kirki da iya jan mutane a jiki. Col. Ishaq mutum ne mai jama'a, a irin zamansu da kyautatawarsa gareta haihuwa ce kadai tasan zata yi ta faranta masa rai sosai. Hawaye taji ya zubo mata tayi saurin sharewa kada ya gani hankalinsa ya tashi.

Wayarta ta saita a kansa ta kashe flash light ta fara daukarsa a hoto. Sai da ta gaji don kanta ta juya zata fita taji ya tade mata kafa ta fado a kansa. Da farko ta tsorata sai kuma ta fasa bayan taji yadda ya riketa a jikinsa. Ta dube shi idanunsa har lokacin da alamar bacci ya sake kwantar da kansa ya rufe ido. Tace
"Tun yaushe ka tashi?"

Bai bude idon ba yace "tun da kika shigo kina kare min kallo mana. Ko nayi miki kyau ne"

Tayi murmushi tana shafa sajensa "kullum ma kyau kake min Jikamshina. Musamman idan kasa kayan nan kamar kada ka fita"

Yaji dadin abinda ta fada. Kamar yadda mata ke son a yabe su haka maza suke so suma matansu su yaba musu. Wayarta ya karba ya daukesu selfie suna yiwa juna murmushi. Bayan ya dauka yace "Matar Jikamshi kinyi kuka ko"

Asmau tayi saurin kai hannunta wurin idonta zata goge sauran hawayen da tayi lokacin da take tsaye yana bacci.
"Abu ne ya shigar min ido fa"

"Uhmm uhm Matar Jikamshi kada mu fara yiwa juna karya. Na kuma san halinki da saurin kuka. Fada min me kika saka a ranki."

A nutse yake kallonta ta sake shige masa tana jin wani hawayen na kokarin zuba.
"Kawai ina tunanin abinda zanyi maka ne na faranta maka rai sosai. Kayi min komai a rayuwa har bana jin akwai matar da tayi dacen abokin rayuwa kamar ni. Har kunyarka nakan ji a raina in ga kamar bana yi maka abin da ya dace"

"Babu abinda nake so daga gareki da baki bani ba. Kin bani Asmau da duk abinda Asmau ta mallaka. Adduata kullum Allah Ya bamu zaman lafiya mai dorewa."

Ta amsa da amin hawayen da take boyewa suka gangaro. Ba su suka fito ba sai da Amatullah ta dawo daga islamiyya lokacin an kusa kiran magariba.
*****

Bayan ya tafi aiki da safe sannan Amatullah ta tafi makaranta ta gama gyaran gida ta dora abinci. Walida na son alala shiyasa da tayiwa Jikamshi nashi abincin ta gyara wake tayi musu alala mai cike da dafaffen kwai da ta yanka kanana da kayan hadi. Kafin ta iso ta gama komai da zatayi har da juice din kwakwa da ayaba.

Sai da tayi wanka Walida ta iso suka zauna hira. A hirar ne suna cin abinci Walida take neman shawararta akan abokin Col. Ishaq wanda shina soja ne kuma likita a nan asibitin barrack dinsu. Sunansa Hussaini, yana da mace daya da yara hudu. Asmau dadi ya kamata tace "ashe dai da gaske yake, Walida ki amince ni dai a dan haduwarmu a fuskanci mutumin kirki ne kuma mai addini. Yazo gidannan tare da Jikamshina yayi min tambayoyi a kanki. Dama shiru nayi sai kinji daga bakinsa."

ABINDA AKE GUDU (Completed)Where stories live. Discover now