ABINDA AKE GUDU🙆🏽36
Batul Mamman💖
Ba karamin damunsa rashin daukar wayarsa da Asmau take yi yayi ba. Sai dai kuma ya kuduri niyyar bazai barta ba. Murmushi yayi....yana son mace mai jan aji, amma bazai bari ta ja masa aji da yawa ba saboda yadda yake ji da ita a zuciyarsa. Har mamakin kansa yake yi. Bai yarda sonta yake yi har haka ba sai bayan 'yar hirarsu ta dazu. Yana son muryarta, kunyarta, yanayinta....ya dan shafa kansa yana murmushi ya tura mata da text
"Asmau Ummin Safina ki shirya, don Jikamshi da gaske yake. Kiran wayarki kuma yanzu na fara. Gudnyt"
*****Hannunta har rawa ya soma bayan ta karanta text din. Wani abu taji ya ratsa jikinta gabadaya don dadi. Bayan Abubakar bata taba tunanin sake jin wani abu makamancin wannan akan kowane da namiji ba sai akan Col I.M Jikamshi. Sai dai kuma wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Yaudarar kai ne ma ta yarda wani abu yayi nisa tsakaninsu. Tafi kowa sanin ko ita wacece, bata cikin mata da zasu sami rabon aure a wannan duniyar. Dadin dadawa Jikamshi ba karamin mutum bane. Yana da wata kima ta daban a idonta, sam bazata so suyi rabuwa mara dadi ba. Gara tun ba'a soma ba kada a fara. Tana wannan tunanin ne bacci ya kwasheta.
Washegari Umma ke fada mata su fara shiri nan da kwana biyu zasu tafi Zaria da Aina'u. Sati daya zasu yi daga nan zata zo ta same su su wuce Wushishi. Jin zata je Zaria wurin Anti Bintu yasa ta farinciki har ta dan manta da tunanin da ta kwana ta tashi dashi.
Shirye shirye suke yi daga ita har Aina'u sun hada kayansu da komai. Yassar ne zai kaisu ya dawo washegari.
Da yamma ne ta tafi gidan Jafar saboda yace yana son ganinta tace ya bari zata zo da kanta. A gida ta bar Amatullah tana bacci. Sun dan taba hira da Sabira ta tashi ta basu wuri. Ba wani dogon abu bane maganar karatu yayi mata wanda yace sunyi shawara ne da Shemau zasu hada kudi su biya mata ta koma makaranta. Kuka take yi sosai kamar yasan abinda take son yi kenan.
"Yaya Jafar Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai, nima abinda yake raina kenan don bana son nayi ta zaman haka.""Kada ki damu Asmau. Ina so ki manta da rayuwar baya kiyi kokarin gina rayuwa mai kyau daga yanzu. Kada ki manta ko ke wacece a duk inda kike. A yanzu da kika dawo gida inda mutane suka sanki suka san labarin rayuwarki ki zauna da shiri na fuskantar kalubale kala kala. Dole duk inda kika shiga kiji maganganu marasa dadi daga bakin mutane daban daban. Abinda nake bukata daga gareki bai wuce ki toshe kunnuwanki ba. Komai yayi farko yana da karshe. Ki mayarda dukkan lamarinki ga Allah sai kiga kinyi nasara."
Tayi murmushin takaici "hakane, kuma nagode da shawararka. Dole ne nayi hakuri da dukkan abinda mutane zasu ce game dani da Amatullah. Irin labarinmu dai da wuya yake zama tarihi. Duk wanda ya sanmu duk sanda muka hadu sai sun tuna. Wannan kaddara har jikoki idan da rabo nasan za'a goranta musu wata rana" ta kare maganar da kuka.
Tausayin kanwarsa yaji sosai. Ya dade da sanin cewa illar zina tana bibiyar mutum duk inda yaje. Musamman idan akwai haihuwa tsakani. Fatanmu kawai Allah Ya tsare mana imaninmu Ya karemu daga fadawa sharrin shaidan da mukarrabansa.
"Ki tsarkake zuciyarki Asmau, daga nan ki barwa Allah komai. Rayuwa ce kowa da irin tasa. Babban abin dubawa dama shine tuba da komawa ga Allah. Idan kika yi haka to babu ruwanki da zancen mutane. Duk wanda ya fiye bibiyar kuskuren dan uwansa don tonon asiri to Allah na kallonsa kuma Shine Yasan yadda zaiyi da bayinSa."Godiya ta sake yi masa har ta kira Shemau tace zata je har gida tayi mata godiya. Dan uwa rabin jiki inji bahaushe...banga mai kamarka ba. Abinda suka aikata ita da Abubakar ba su kadai yake bi ba domin kuwa tasan za'a nuna iyayensu da 'yan uwansu idan dalili ya kawo suma a goranta musu. Kai zina laifi ce mai muni, kazanta ce mai kaskantar da mai daraja. Ya Allah Kasa mufi karfin zukatanmu. Masu neman aure maza da mata Allah Ka basu abokan rayuwa nagari. Mu kuma Ka bamu zaman lafiya da wadanda Ka hadamu dasu.
*****