ABINDA AKE GUDU🙆🏽11
Batul Mamman💖
Rabe ne ya fito yasha sabuwar shadda sai kyalli take yi. Idonsa a kan Bara'atu da yanayin da ta shiga yayi dariyar mugunta. Don tsabar wulakanci yace
"A'a bazawara kune a garin? Ya hanya?"Hawaye take yi wani na bin wani ta durkusa a gaban Hajjo
"Nasan har mijina ya rasu baku taba kaunata ba amma Hajjo wallahi cin dukiyar marayu haramun ne. Gidan nan baku da hakki a kansa to a wane dalili zaku zo ku tare batare da izini ba"."Eh, lallai wuyanki ya isa yanka Bara'atu. Ni da gidan dana kike gaya min maganar banza." Hajjo ta amsa itama rai a bace.
"Ko kinki ko kinso zama dole muyi a gidan nan. Idan bazaki iya zama damu ba sai ki bar min yaran ki kama gabanki."
Yusuf mijin Anti Bintu yace "Anti kada ki sake cewa komai. Ai basu fi karfin hukuma ba. Kuma rabon gado ba hauka bane. Ki bari mu kwana yau gobe sai mu san abinyi."
Mikewa tayi cikin zafin nama tana kallonsu daidai. Garzali banda taba babu abinda yake busawa. Rabe da amaryarsa suna tsaye suna mata kallon banza. Hannu tasa ta share hawayenta
"Dama can saboda marigayi nake raga muku to amma wallahi yanzu an wuce wurin. Mu zuba ni daku shege ka fasa."Yaranta ta dakawa tsawa duk suka tashi daga gaban Hajjo suka bita cikin gidan.
Hajjo da su Rabe kowa yayi tsit suna mamakin wai yau Bara'atu ke mayar musu da martani haka.
*****A cikin gidan dakuna biyu ta samu a bude ita da Yusuf da su Shemau suka rinka shiga da kayansu. Sai cikin dare tana zaune tana kallon 'ya'yanta na bacci ta rinka kuka.
Washegari ko karyawa batayi ba suka fito ita da yaran suka hadu da Yusuf zasu tafi ofishin 'yan sanda.
Rabe yana tsaye a waje yace " kinga basai kun wahala ba a bayan layin nan akwai gidan wani babban dan sanda. Maza ku tafi ku kai kara kada kuda ya rigaku."
Basu kula shi ba suka wuce. Duk wani bayani sun gabatarwa 'yan sandan. Mutum hudu aka hado su dasu suka zo aka bukaci su Rabe su fita.
Wannan muguwar dariyar yake yi ya dauko takardun gida sai gashi sunansa ne dana Shu'aibu a jiki a matsayin tare suka gina.
Kuka sosai Bara'atu take yi tana karyata shi. Sai dai kuma bata da shaida. Bata san yadda akayi ya sami takardun gidan ba wanda a hannunta suke har akayi canje canje haka.
Dole 'yan sanda suka tafi domin basu da wata shaida.
Yusuf ya nemi ta bishi su koma Zaria daga nan ta koma garinsu da zama.
Tana kuka tace "ko zasu kashemu babu inda zamu je. Gidan nan namu ne kuma duk rintse sai ya dawo hannun masu shi."
Babu yadda Yusuf ya iya dole ya tafi ya barta. A dakin kwanansu ta sayi risho mai kai biyu da kayan abinci. Kullum suna daki tana saka yadda zata bullo musu.
A karshen sati ne abokan marigayi biyu suka zo. Anyi ta kai ruwa rana Hajjo da Rabe da sauran 'ya'yan gidan suka hade musu kai. Magana dai har wurin dan sandan dake bayan layinsu, Adamu Matawalle ashe abokin daya daga cikinsu ne. Shima ya gamsu da bayanansu sai dai ga shaida kurukuru suna gani gida na Rabe da Shu'aibu ne. Shawara suka bata akan ta koma gida kawai tace babu inda zata je.
Wani katon fili wanda gida daya ne tsakaninsa da gidan dan sandan ta nuna musu. Rabi nata ne ta siya da kudin kasuwancinta daya rabin kuma Shu'aibu ne ya siya mata. Takardun ta bawa dan sandan ta roke shi ya rike mata amana zata gina kayanta a hankali sannan su tashi daga can gidan. Duk ta basu tausayi. Wani cikinsu ne yayi cuku-cukun nema mata aiki a kamfanin sadarwa na MTN , duk wannan abu batare da sanin su Rabe ba. Tayi musu godiya kamar ta ari baki.