ABINDA AKE GUDU🙆🏽12
Batul Mamman💖
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Anti Bintu tazo Kano wurin yayarta yawon arba'in. Tunda tazo kullum sai sun fita kasuwa siyayyar kayan amfanin gida. Duk wani kudin Bara'atu na albashi, kasuwanci da abinda ta samu na gado ta hada shi a gini da zuba kayan bukata a sabon gidan. A lokacin falo da dakuna biyu kawai ta gama sai kitchen amma bahaushe yace da babu gara ba dadi. Hatta sutura da Hajjo ke yi mata gorin bata siyawa yaranta duk ta siya. Dama tara kudin take sai ta gama da abinda yafi mahimmanci.
Sai da ta gama shirinta tsaf sannan wata juma'a bayan su Asmau sun dawo daga makaranta tasa sukayi wanka duk ta basu sababbin kaya sannan ta hada sauran 'yan kayansu suka tafi dakin Hajjo. Duk yaran mamaki ya ishe su ina Umma zata kaisu sun kwashe duka kaya.Kwadon zogale take ci yaran Rabe suna zaune suna wasa a gefenta tana dariya. Shigowar Bara'atu da 'ya'yanta yasa ta hade rai.
Dan Rabe na biyu sarkin gulma ya ruga ya fadawa babansa ga Anti Bara da su Jafar zasu fita yau sunyi kwalliya. Daga shi sai dogon wando haka ya fito da sauri jin kwaf.
Bara'atu na dauke da jaririyar Bintu tace
" Hajjo albarkacin zaman tare a yafemu Allah Yayi zamu tashi"Zaro ido sukayi ita da Rabe. Shi a son ransa idan Bara'atu ta gaji da takurata da akeyi ta yarda da aurensu. A ranar ma zai saki Sagira.
"Ina zaki kai min yaran da kike cewa zaku tashi? Idan tafiya zakiyi ke kadai dai ga hanya nan."
"Ba nisa zanyi ba Hajjo, nan layin gidan sabon kwamishinan 'yan sanda zan koma. Cikin ikon Allah na kammala gini na."
Ashar Rabe ya fara saki sannan yace "kika kammala wane ginin? Waye ya baki filin da kudin ginin?kada ki raina mana wayo wani saurayin kika yi kuke zaman....."
Katse shi tayi kafin yayi barambarama gaban yara.
"Fili dai tare muka siya da wannan da kuke ciki ni da babansu Yassar. Ina sana'a ina aiki. Allah Ya buda min gashi nayi gidan kaina. Wannan da kuke ciki kuma har abada ku sani cewa gidan marayu ne. Allah SWT kuma Yace wanda yaci dukiyar marayu tamkar yana ciwa cikinsa wuta ne."Hajjo ta bata rai "nufinki mune 'yan wutan..Bara'atu ki kiyayeni wallahi. Kuma idan kika fita da yaran nan to ki sani babu ni babu su."
"Ai aikin gama ya gama. Yara dai ke kika haifi babansu saboda haka jininki ne. In Allah Ya yarda zasu rinka zuwa gaisheki tunda ba nisa mukayi ba."
Daga haka suka fice Rabe yana binsu a baya yana kiranta.
******Sabuwar Rayuwa*
Wannan tashin nasu shine ya kara kiyayya tsakanin iyalan mariyayi Shu'aibu da gidan Hajjo. Kamar yadda ta fada duk juma'a bayan masallaci take tura yaran gaishe da Hajjo. Manyan kullum sai sun dawo rai a bace ko da hawaye a idonsu. Amma hakan baisa ta dena turasu ba saboda tasan su din dai suka rage musu dangin uba.
Rayuwa sabuwa suke yi cike da 'yanci da jindadi. Bara'atu ta dage wurin bawa yaranta tarbiya. Sannan tana nuna musu soyayya irin wadda bazata sa su sangarce ba. Shakuwa mai karfi ce a tsakaninta da 'ya'yanta.
Washegarin tarewarsu suka shiga makota domin gabatar da kai. Lokacin da suka shiga gidan Kwamishina Mama Yalwa tayi musu tarba ta karramawa. Dama sun saba da Umma. Duk yaranta suna gida ta kirasu ta gabatar dasu ga 'yan uwansu kamar yadda ta fada musu. Abdulhalim, Nasiba da Abubakar dai duk sun girmesu amma suma sunyi kokarin jansu a jiki.
Bayan 'yan kwanaki ne Mama Yalwa taje gidan Umma take sanar da ita Baba yace ta rinka turo su Asmau ana yin magariba masallacin gidansu akwai Malamin da yake koyar dasu Sadiya karatun Qur'ani zuwa karfe tara.
Umma taji dadi sosai,duk da suna zuwa islamiyya amma wannan ma zai taimaka kuma ba nisa suka yi da gida ba.