ABINDA AKE GUDU🙆🏽15
Batul Mamman💖
Asmau da Walida sun shiga aji uku karatu ya fara zafi. Abubakar ya kusa gama hada lefe domin ya sami aiki a Kaduna. Duk juma'a yake tahowa Kano ya koma lahadi da yamma. Wasu lokutan kuma sai bayan sati biyu yake iya zuwa. Iyaye maza sun shiga
maganar auren har an kai kudi sannan an sa rana wata bakwai saboda wanda yake haya a gidan Abubakar din ya nemi alfarmar a kara masa lokaci ya kusa gama gininsa. Idan ya tashi sai anyi 'yan gyare gyare a gidan.Dubu hamsin dangin Abubakar suka bayar kudin aure amma ko kwandala Alh Rabe bai aikawa Umma ba kamar yadda yayi a na Shema'u. Shiru tayi kawai ta barsu da halinsu. Cin haram ba komai bane a wurinsa.
*****
Lecture akeyi ta Chemistry hankalin Asmau yana wurin malamin tana jindadin bayanin da yake yi musu. Daga gefenta Walida hankalinta gabadaya yana kan wayarta. Sau biyu Asmau na tabata idan ta kula kamar ita malamin yake kallo sai ta doke mata hannu.
Takowa yayi har wurin zamansu ya tsaya gaban Walida amma ko motsinsa bata ji ba. Murmushi ne a fuskarta mai nuni da tana jindadin abinda take yi. Hankalin Asmau duk ya tashi ta sake zungurinta da hannu. Walida na dago kai zata yi mata fadan ta dameta suka hada ido da malamin yace ta bashi wayar.
A take ta rude ta fara bashi hakuri. Gani yayi zata bata mishi lokaci yace ta zabi ko wayar ko kuma ta kawo ID card dinta. Ba yadda ta iya dole ta bashi wayar tana ta turo baki.
Bayan minti arba'in da biyar suka fito Walida sai tsaki take yi. Asmau ta gyara jakarta tana kallon kawarta.
"Ni kina bani mamaki Walida, sai ki kafawa waya ido ko sassautawa bakya yi. Ace ana lecture ma bazaki hakura ba. Da wa kike chatting haka?"
Tsayawa Walida ta yi tana jiran fitowar malamin "nifa ba chatting nake yi ba. Wani novel nake karantawa mai dan karen dadi. Don bakiji yadda ake soyewa bane a labarin" ta fada tana lumshe ido.
"Tunda har an turo miki ba sai ki hakura mu fito ba sannan ki karanta. Yanzu gashi kin rasa wayar ai."
Idanun Walida na duban ta inda Malamin nasu zai fito tace "bazaki gane irin dadin labarin ba sai kin karanta. Kuma naga idan an fito lokacin sallah yayi bazan nutsu a sallar ba bayan nasan an turo shiyasa na karanta a aji. Bari na samu ya bani zan turo miki."
"Nima ina karantawa kinsani amma gaskiya ba ko wanne ba. Kuma bana bari karatun novel yaci karo da abubuwa masu mahimmanci na rayuwata. Komai idan kika bashi lokacinsa yafi."
Fitowar malamin ta katse musu hira nan fa Walida ta hau magiya. Da kyar ya bata wayar tare da gargadi sosai. Ita dai ta karba tayi masa godiya sannan suka nufi masallaci. Kafadar Asmau ta dafa cikin zumudi ta cigaba da karatun duk da ranar da akeyi bata ganin rubutun sosai. Ko inda take ajiye kafa bata damu ba ta mayar da Asmau tamkar 'yar jagora.
Har Asmau ta idar da sallah Walida tana karatu ko alwala bata yi ba.
Tsaki Asmau tayi "dama bai baki wayar ba muga tsiya. Dazu kinki sauraron lecture yanzu kuma sallah ta gagara. Wallahi kiji tsoron Allah. Ina mamakin yadda mata yanzu suke matsuwa da labarai irin haka har ya hanasu gabatar da abubuwan da suka fisu mahimmanci."
Mitar Asmau ce ta ishi Walida ta tashi tayi sallah. Daga nan suka sayi awara da kunun aya suna ci Walida tace
"Asmau anya kina karanta novels din da nake turo miki?"