35

5.3K 356 2
                                    

ABINDA AKE GUDU🙆🏽35

Batul Mamman💖



A tsorace take har a lokacin ga hawaye ya gama jike mata fuska. Col. Ishaq ya dubeta da tausayawa ya dauko hankici ya bata
"Goge hawayenki kada Safina ta gani"

Kin karba tayi cikin rawar murya tace "karen waye?"

"Nawa ne"

Albarkacin girmansa da take gani yasa bata ce komai ba daga cikin kalaman da ta shiryawa mai karen nan sai wata harara da ta doka masa ta tashi tayi hanyar motar da suka zo kafafunta duk kura, takalmanta kuwa bata ma san a ina suka rabu ba don masu tudu ne.

Col Ishaq yana tsaye yana binta da kallo, ba dai fushi tayi ba saboda karensa ya biyota ya tambayi kansa. Yana kallo ta bude motar Amatullah ta fado jikinta suka rungume juna. Wannan uwa da 'ya sai Allah ya sake fada a ransa sannan ya juya ya tsinto mata takalmanta.

Kafin su kai ga shiga gidan su Umma sun fito gabadayansu. Haj Lubabatu tace
"Allah Sarki Asmau muna ciki kina fama da karen nan. Nima kaina tsoronsa nake yi. Wani abokin yayansu ne yaje turai ya kawo masa tsarabarsa wai tsada ne dashi. Sai dan karen muni kamar a gudu"

Umma da Mama suka yi dariya "Ita ma banda abinta ai da ta tsaya. Yawanci karnuka basa bin mutum idan ya tsaya wuri guda" Umma ta fada tana kallon 'yarta wadda har yanzu jikinta bai dena rawa ba.

Hajjo ta rike hannun Asmau suka shiga ciki "ki dena zancen kada ta gudu Bara'atu. Ko ni nan naga kare sai inda kafata zata kaini. Haka nayi ta fama da na Garzali. Na rasa dalilin da yake sa mutane ke kiwonsa."

Mama ta dauki Amatullah suka shiga ciki. Bayan sun zazzauna Col. Ishaq ya shigo ya zauna a kan wata kujera daga gefe suka gaisa dasu Umma. Yayi ta kokarin su hada ido da Asmau saboda yana son suyi magana ya bata hakuri amma sam taki kallonsa. Amatullah itama yau gaishe shi kawai tayi ta sake lafewa a jikin Asmau. Yayi dan murmushi ya tashi. Sai yayi da gaske don yaga alama yadda Asmau tayi fushi Amatullah ko dai ba fushin take yi ba ga dukkan alamu halin da ta ga Umminta yasa jikinta yayi sanyi. Shi burgeshi ma suka yi yadda suka shaku suke son juna.

Hira suke yi sosai kamar sun jima da sabawa da juna banda Asmau. Ana ta jan Amatullah da hira taki sakewa daga baya ne ta hau bada labarin karen da ya biyo Umminta har tana cewa zata fadawa Babanta ya kai shi bola ya yar. Sai da suka yi sallar magriba suka tashi tafiya da Yassar ya dawo. Sannan ne Asmau ta dan sake suna hira da Bilkisu tana bata labarin makaranta da take yi.

Sun fito zasu tafi Col. Ishaq shima ya fito sanye da shirt maroon da bakin wando. Idan ka ganshi baka ce ya baiwa shekara arbain baya ba saboda yanayin aikinsa yana taimaka masa wurin kula da jikinsa sosai. Sai kamshi yake zubawa ya ce da Hajjo "bari na rage muku naga kamar a matse kuke a motar."

Yassar yayi dariya yana kallon Col. Ishaq da girmamawa. Tunda yaji soja ne yake burge shi "duk nauyin Ya Asmau ne dama ya kusa sace mana taya"

Shima harara ya samu. Dama tunda Col Ishaq ya fito taki kallon inda yake tsaye ma. Saboda karensa ji gudun da tasha duk 'yar kwalliyar da ta zauna yi hawaye da gumi sun goge mata. Idonsa a kanta yace "ni Hajjo zan dauka kawai da 'yata. Bilkisu muje ki rakani" cike da murna ta shige cike zata dan gyara fuska.

Hajjo bude bayan motar Yassar "Soja rabani da wahalar 'yarka. Kana kallo yau wani makalewa take jikin mamanta. Ka dauke su dai tare ka barni da 'ya'yana."

"Gani take kamar karen nan zai sake biyo Umminta ne ko Safinatu? Mu dai duk babu laifinmu don karen babanki ne" Haj Lubabatu ta fada.

"Babana wai naka ne?"

Yarinya ta tsare shi da ido yace "bani aka yi amma yau zan fitar dashi daga gidan nan"

"Ummina bata son kaye da inada kayfi sai nayi fada dashi nayi masa duka. Har kuka fa Ummi tayi dazu baka zo da wuyi ka kama shi ba."

ABINDA AKE GUDU (Completed)Where stories live. Discover now