ABINDA AKE GUDU🙆🏽8
Batul Mamman💖
Tafiya su Asmau suke yi a inda tafi tunanin kasuwa ce saboda yawan shaguna da ta gani da mutane suna kai kawo kamar ba dare ba. A bakin kofar wani gida suka tsaya mai kofa daya. Sai da suka shiga ta ga ashe gidan yana da girma ta ciki. Dakuna ne birjik ta bangaren hagu , dama da tsakiya. Ga 'yan mata kamar ba dare ba suna ta bidirinsu babu mai shigar arziki. Harda masu daurin kirji. Tun daga nan Asmau ta fara dana sanin biyo mutumin.
'Yan matan taga suna gaisawa da mutumin da ta biyo suna tambayarsa bakuwa ya kawo musu yace eh. Tafiya suka cigaba da yi har sai da suka je kofar wani daki daga gefe. Dan mukulli yasa ya buga kofar dakin wata budurwa ta fito a fusace. Wani mugun kallo ta watsa musu shi da Asmau sannan ta matsa gefe wata babbar mata ta fito. Doguwa ce da gani shekaru sun ja, jikinta kuma yayi jaja-jaja alamun anci bleaching lokacin da ake ji da sauran kuruciya. Ganin su Asmau yasa ta washe baki tana murmushi.
" Bulayi kaine a daren nan? Bakuwa ka samo mana ne?"Shima murmushin yayi "a bamu wurin zama mana sai muyi magana a nutse".
Yarinyar da take ta hararsa a kofar dakin matar ta kalla ta koma ciki ta dauko musu tabarma aka shimfida a wurin. Sauran 'yan matan gidan kowacce harkar gabanta take yi.
Mutumin da ya amsa suna Bulayi yace
" ina shirin fita daga tasha nayi gamdakatar. Dubi tsaleliyar da na gano. Ina ganinta nace wannan taki ce don duk garin nan gidanki ne gidan kyawawa."Matar ta maida kallonta ga Asmau " yarinya ina miki barka da zuwa. Ni sunana Uwargida haka kowa yake kirana. Kuma tunda kika zo gidan nan zamu taru mu sharewa juna hawaye. Babu ruwana da abinda ya fito dake bariki indai zaki kiyaye dokar gidana shikenan."
Asmau ta mike tsaye domin ta gano wane irin gida aka kawota. Jakarta a hannu tace "Hajiya kiyi hakuri ni ba yawon bariki na fito ba. Bazan iya zaman gidan nan ba. Nagode".
Takalminta ta fara kokarin sakawa ta dan hada ido da yarinyar dake tsaye a wurin. Ga mamakinta murmushi sosai yarinyar tayi mata.
Uwargida tayi dariya sosai "duk yaran gidan nan da kika gani babu wacce take yarda karuwanci ta fito yi sai babu ta sakata a gaba. Ni bazan matsa miki ba. Akwai daki na haya dubu goma duk wata. Idan kina so a jona injin gidan nan dake ki rinka samun wuta idan babu a gari duk sati zaki biya dari biyar. Ci, da sha da sutura kuma kowa ta kansa yake yi. Zabi ya rage naki. Zaki zauna ne ko zaki fita ki kwana a titi".
Shiru Asmau tayi tana tunani. Yanzu idan ta fita ina ta nufa.
Matar ta katse mata tunani " bana tilasta mace tayi sana'ar da bata so amma indai ba kina da jari ko wurin zuwa fa to nan ne gidan da kowace 'ya da bakincikin rayuwa ya korota zata kira gida."
Bulayi yace "kuma gata da jikin sana'ar ba. Fatarta har wani sheki take yi tayi luwai-luwai. Ni da na matsa kusa da ita ma har kamshi naji tana yi shiyasa nace da shirinta ta fito."
Dan murmushi Uwargida tayi sannan ta zaunar da Asmau a kusa da ita
" ke amarya ce ko?" Ta fada tana daga gira."Irinku yawanci mijin ne bakwa so sai ku gudu. Shiga duniya ba da ka ake yinsa ba. Dole ki fara ta wani wurin. Kamar yadda na fada miki ko wurin zama ki samu nan gaba idan kika shafa kika ji babu abinda zaki ci nasan zaki fara sana'ar da bata tsufa. A lokacin zan taimaka miki da kayan aiki wato maganin mata sannan na hadaki da kilayen(client). A tsarin gidan nan duk wadda tayi ciniki a gida ko a waje zata bani kaso goma a ciki. Sauran bayani dai sai kin shigo hannu. A lokacin kuma zan saka miki suna. Ni nan babu ruwana da sunan kowace yarinya na gaskiya."
Yarinyar dake tsaye a gefe tayi tsaki "haba Mama tace ba abinda ya fito da ita ba kenan ko dole ne?"
Bulayi ya kalleta yana dariyar shakiyanci "ustaziya Zubaida kenan, kina nan da halinki na korar mana alheri".