ABINDA AKE GUDU🙆🏽56
Batul Mamman💖
*Assalam alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu. Gaisuwa da fatan alkhairi gareku masoya Abinda ake gudu. Kira garemu baki daya Allah Mai iko, ABINDA AKE GUDU ya faru, wata yar uwa ta sanar dani cewa anyi bikin kanwarta bayan wata biyu ta haihu. A cewarta yarinya ce karama kuma tana da siffa ta kamala daga ita har saurayin da yayi mata cikin wanda shi ya aureta. Saboda haka Allah Ya shirya babu wanda ya taba sanin da cikin sai da akayi aure. Yanzu haka ta haihu ita da mijin sai kukan nadama suke. Yan uwana mata don Allah mu hankalta mu rike mutumcinmu. Idan ya zube babu yadda za'ayi martabarki ta dawo a idon al'umma. Mu yawaita addua, kada soyayya ta rufe mana ido, kada shaawa tafi karfin zukatanmu. Ita kuma yarinyar nan Allah Ya yafe musu Ya kawo musu sassauci a lamarinsu. Amin*
Bakin da suka zo daga gidan Hajiya suna zuwa gida suka shiga bada labarin abinda suka gani. Wata har cewa tayi tana jin tashinsu kenan daga bacci. Manyan cikinsu dai sai korafi da mita. Hajiya tayi shiru bata iya cewa komai ba. Tun da suka ce zasu je tayi tunanin zuwan nasu yayi wuri. To amma tana gudun magana ace tayi rashin kunya tunda dan fari ne ko ta goyi bayan nata. Da suka yi mata wayar anki bude gate ma a ranta sai da tace indai shine (Ishaq) kadan suka gani. Gashi wata zuga guda sun sake tafiya harda Mami bata san yadda zasu kwashe ba.
A gidan Umma ma haka abin yake. An ce ango ya fito da jallabiya sannan amarya ita ma da alama dai tayi wanka amma fuskarta ko hoda da kwalli babu da gani bata dade da tashi ba. Amaren zamani basu da kunya. Suna ta mayar da zance Umma na jinsu. Anti Bintu tana kusa da ita tace mata "sai da nace zan hanasu zuwa kika ki ai gashi nan nasan wannan labarin har Wushishi"
Hajjo ta fito falon tace "yaron nan yayi min daidai. Ina ce abinda kuka je gani kenan. Yaya amarya da ango suka kwana ko, to ai kun ganewa idonunku. Dama yadda nake ganin yaron nan abinda yafi haka ma zaku gani"
Wata dattijuwa cikinsu tace "haba Hajjo kinsa n fa a al'adar hausa dai an saba da zuwa gidan amarya washegari. Kamata yayi ace ya ma fita yadda zamu dan sake mu zaga gidan"
Hajjo tace "ai sai ku koma ku ga abinda baku gani ba"Anti Bintu ta fashe da dariya don ta fuskanci dama tun da suka fara shirin zuwa ranta bai so ba.
******A ra'ayin Col. Ishaq a ranar fita masallaci ce kawai zata kai shi waje. Sai gashi tun ba'aje ko ina ba 'yan ganin amarya suna shigar masa hanci domin bayan ya dawo daga sallar azahar yana shigowa gida yaji tsayuwar mota. Abin ma sai yaso bashi dariya. Yaga alama da biyu bakin nan suke zuwa. Gobe in sun zo sai su ga gidan su koma ya fada a ransa. Ciki ya shige ya sami Asmau tana kitchen a tsaye tana kallon sama kamar mai tunani.
Ya shigo yana kallonta, dazu da tazo bada hakuri ba karamin kyau kayan suka yi mata ba, amma yanzu sai ya kula har tafi kyau. Ta juyo tana sunkuyar da kai. Shi bashi da aiki sai na kallonta ne, gashi kayan nata ba'a cewa komai. Suna cikin wanda tayi niyyar sawa bayan kamar sati biyu da aure lokacin an kara sabawa. To zuwan baki sun sa ango fushi dole a bashi hakuri. A yanzu haka so take ta dan je daga gabansa tayi masa sannu da zuwa sai kuma taji kunyar kallon nasa. Ya hade hannuwansa a kirji yana jingine da bango.
"Me yasa bana gajiya da kallonki Matar Jikamshi?"Tayi murmushi sosai "nima tambayar da zan maka kenan"
Ya soma matsowa gabanta "bari nazo na fada miki dalili"
Yana kai hannu zai kamota suka ji sallamar mata. Asmau har dan tsorata tayi tace masa
"Kaji ana sallama bari naje na gani"Shi kuwa hade fuska yayi "ina shigowa naji tsayuwar mota, rabu dasu nema suke su hanani sakewa da matata. Idan kuma zaki wurinsu ki barni ne kamar dazu shikenan"
Kada a maimaita fushin dazu sai ta dan tsaya amma hankalinta yana kan masu sallamar nan. Shi kuwa riko hannunta yayi yace "ni fada min tunanin me kike yi daga fita ta masallaci, ko duk nine bakya so nayi nisa da ke"