ABINDA AKE GUDU🙆🏽14
Batul Mamman💖
Kwance tashi babu wuya a wurin Allah. Anyi bikin Suwaiba da Sadiya lokaci daya. Asmau kuma ana ta shirin fara WAEC da NECO. Ita kuma Shemau tana aji uku a jami'a sannan ansa bikinta wata hudu masu zuwa. Asmau tayi murna don lokacin ta gama jarabawa. Karatu take yi sosai saboda don cika burinta na zama likita. Har gidan su Abubakar yaje da laptop dinsa yayi mata registration din JAMB. Anan ne ya cike mata medicine a matsayin zabin farko sai pharmacy a zabi na biyu.
Duk abinda ya shige mata gaba tana tambayarsa ya koya mata.
Gab da fara jarabar tasu ne posting din su Abubakar ya fito an tura shi jihar Ebonyi bautar kasa. Da yaje fadawa Umma yana kula da yadda fuskar Asmau ta nuna rashin jindadi sosai. Shi kuwa hakan yayi masa don yanzu ya tabbatar ba shi kadai ne zuciyarsa ta kamu da sonta ba. Jira yake yi ta kammala makaranta sannan ya fada mata.
Watansa biyu da tafiya watarana tana dawowa daga makaranta sun gama practical din food and nutrition yamma tayi sosai wani saurayi ya tareta a hanya. Tunda ta fito daga makaranta bayan sunyi sallama da Walida kawarta yake binta a baya. Tsoro ne ya cika mata zuciya bare da yayi mata sallama ya bukaci ta tsaya. Yana bayyana mata soyayyarsa tace yayi hakuri tana da mijin aure har ansa mata rana. Saurayin ya gamsu ya tafi. Ita kuwa a ranta gani takeyi kamar taci amanar Abubakar ne ma idan ta tsaya da wani duk da bai taba cewa yana sonta ba.
Alhamdulillah sun gama jarabawarsu lafiya sai jiran sakamako. Ranar da ta gama tana dawowa gida Umma na kitchen ta kwala mata kira. Ko kayan makaranta bata cire ba taje amsa kiran.
Umma na murmushi tace "Asmau yau an gama jarabawa ko? To ki dage da addu'a kamar yadda kullum nake yi muku. Allah Ya bada sa'a Yasa ku gama lafiya."
"Amin Ummana".
"Kije dakina akan gado duk abinda kika gani naki ne na tayin murnar gama exams. Sauran kyauta sai naga result mai kyau."
Dadi ya kama Asmau tana ta godiya ta ruga dakin Umman.
Kwalin waya ta gani akan gadon hannunta har yana rawa ta dauka tare da yin ihun murna.
Daga kitchen Umma tace "Asmau babu hamdala sai ihu ko? Kin kyauta."
Dena ihun tayi ta fara godiya ga Allah sannan ta fito falo wurinsu Jafar. Sun tayata murna Yassar yana rokonta ta rinka bashi yana yin game. Shema'u da Jafar kayansu baya tabuwa.
Jafar ya bude kwalin harda sabon sim na mtn. To dama Umma yanzu ta kara samun matsayi don har mota ta siya. Masu abu da abinsu. Duk wanda ta sayawa waya dole yayi sim din mtn.
Suna gama murnarsu ta saka hijab ta fadawa Umma zata je ta nunawa Mama. Umma tace "babu inda zaki sai kinyi wanka kin canja kaya. Kin yini da uniform kuma kice dasu zaki fita?"
Komawa tayi ciki tayi wanka ta canja kaya ta. Tare da Aina'u da Yassar suka tafi. Umma ta girgiza kai kawai tana dariya.
Da sallama ta shiga ganin Nasiba tayi a falon da danta Amir. Asmau ta karasa ta rungume Nasiba tana murna sannan ta karbi Amir.
"Tun dazu nazo fa, naje munsha hira da Umma tace kina makaranta. To ya exams din?"
Maimakon amsa wayar ta mikowa Nasiba bakin nan yaki rufuwa. Ta tayata murna suna duba wayar Mama ta fito "yau Idon kuka ce take ta murna haka kamar an baki takardar karatun likita."
"Haba Mama na dena fa. Kinga wayar da Umma ta bani."
"Masha Allah, Allah Ya tsare. A kula sosai don Allah banda yin abinda bai dace ba kinji ko. Ni zaki fara bawa numbar kuma" .