ABINDA AKE GUDU🙆🏽10
Batul Mamman💖
Bara'atu ta gama girkinta tayi wanka sannan tayiwa yaranta. Albishir gareta ga maigidanta idan ya dawo wanda take tunanin zai rage masa bacin rai. Ciki ne da ita har wata biyu. Dayake ranar babu islamiyya su Jafar sai wasansu suke yi a gida.
Sallamar maza taji a kofar gidan ta dauki mayafi ta fita. Ga mamakinta har da 'yan sanda biyu. A tsorace ta gaisa da su sannan guda cikin 'yan sandan ya miko mata ID card ko ta gane wanda yake jiki.
Tana ganin hoton jikinta ya fara rawa "ku fada min abinda ya same shi"
Wani mutum a gefe yace "Hajiya sai dai hakuri a hanyar shiga gari muka ga motarsa yayi hatsari. Allah Yayi masa rasuwa".
Kuka Bara'atu ta saka har yaranta suka fito. Ganin Ummansu na kuka suma suka fara. Bare Shemau da Jafar masu wayo sosai.
Cikin dan kankanin lokaci sauran abokan aikinsa suka zo. Bintu da mijinta ma duk sun zo da makotansu. Karfe uku suka kama hanyar Kano.
Basu tsaya ko'ina ba sai kofar gidan Marigayi Mal Yahaya a unguwar kofar mazugal. Hajjo tayi kuka sosai na rasuwar danta sai fadin irin halinsa na hakuri da kawaici take yi. A nan aka yi masa sutura aka kaishi.
Bara'atu duk ta rame a cikin 'yan kwanakin nan saboda tashin hankali. Saukinta daya shine canjin data gani a tattare da Hajjo. Mutuwar ta daketa sosai shiyasa duk tayi sanyi. Sabanin yadda ta saba yanzu tana jan su Shemau a jiki. A da kuwa sai dai tace su dena kallonta da kwala-kwalan idanunsu na mayu.
Bayan sati biyu da rasuwar gabadaya 'ya'yan Hajjo suka taru da Kawun Bara'atu tare da wani malami da Rabe ya kira akan rabon gado. Kafin malamin ya fara jawabi Bara'atu ta sanar dasu cewa tana da ciki.
Ran Rabe yayi matukar baci ita kuwa Hajjo abin yayi mata dadi. Dole aka hakura da rabon gado sai ta haihu.Da amincewar Hajjo ta koma Zaria saboda makarantar yara. Tausayin Bara'atu ne kawai ya kamata tun bayan rasuwar Shu'aibu.
Bayan wata shida ta haifi 'yarta mace Hajjo da kanta ta zaba mata suna Aina'u. Yarinyar duk tafi sauran 'yan uwanta kama da mahaifinsu shiyasa ta shiga ran Hajjo sosai. Kano suka dawo lokacin kafin tayi arbain. Kwana goma da haihuwar Bara'atu Rabe ya sake dawowa da Malamin rabon gado. An gabatar masa da dukkan kadarar Shu'aibu wanda ya hada da motarsa guda daya da kuma makeken gida da ya gama ginawa a unguwar Hotoro sai 'yan kudade a banki da kuma wanda wurin aikinsu suka bawa iyalinsa sai kuma wata gona a Zaria. Malam ya gyara zama
"Tunda mamacin yana da 'ya'ya da mata sannan mahaifiyarsa tana da rai duk 'yan uwansa basu da gadon shi."Rabe yaji kamar an kwada masa guduma "Malam ya zaka ce bamu da gado? Dukkanmu fa uwa da uba daya muke. Ni nan da kake gani shi ya saki nono na kama ko ba haka ba Hajjo?"
Malam yayi murmushi "Alh Rabe ai shi rabon gado ba'a yi masa katsalandan. Allah SWT da Kansa Ya raba saboda haka babu wani son zuciya a nan. Zan nemi 'yan uwana malamai kamar mutum biyu sai muyi abinda ya dace. Allah Ya jikan Alh Shu'aibu".
Malamin na fita Rabe ya soma fada ya dubi 'yan uwansa. Babu wanda yace masa komai. Dama Garzali karamin cikinsu baya shiga sabgarsu sosai shaye shayensa ne a gabansa. Yaya Abu da Lami ma basuyi magana ba ganin Hajjo tayi shiru. A haka taron ya watse Bara'atu na mamakin wannan hali na Rabe.
Har daki Rabe yabi Hajjo tana daga kwance akan gado ta tashi zaune.
Ya numfasa yace "Hajjo kina jin malamin nan. Yanzu banda sharri yace bamu da gado. Nufinsa wannan gidan da Yaya yake ta shirin komawa Bara'atu da 'ya'yanta ne kadai zasu tare?"
Hajjo tace "banda abinka Rabe ai haka rabon gado yake. Da so kake ace kaima ka shiga gidan ko yaya? Dubi fa yadda ya sake gyara gidan nan. Ni bana son tashin hankali. Kada na sake jin zancen nan ya taso". Da haka ta kashe maganar.