ABINDA AKE GUDU🙆🏽34
Batul Mamman💖
Qasim ya kalli Amatullah ya koma ya kalli Asmau. Abu daya ne yazo masa a rai shine tunanin ko Asmau tayi aure.
Umma ce ta amsa masa duk da bai furta tambayar ba ta hanyar yi masa bayanin waye Amatullah ta dauka babanta. Yayi murmushi "dole muje har gida muyi musu godiya"
Asmau taji dadin yadda ya nuna damuwarsa a kansu. Sai ma da aka shiga yi mata bayanin irin neman da yake mata. Godiya tayi masa tare da fatan alkhairi. Suna tattaunawa wayar Umma tayi kara ta dauka. Mama ce take tuni akan su Asmau su taho yanzu. Aikin da ya kai Alh Adamu Port Harcourt ya kasa tsayawa ya gama tunda yaji batun dawowar Asmau da jikarsa. A yanzu haka an tafi dauko shi daga filin jirgi.
Tashi suka yi aka rankaya gidan don babu mai son a barshi a baya.Zuciyar Asmau sai bugu take yi da suka shiga. Rabonta da gidan tun ranar da suka zo Umma tana rokonsu da su karbi cikinta a matsayin na Abubukar. A take taji hawaye yana neman zubo mata ta mayar dashi. Basu dade da zuwa ba su Baba suka iso gidan. Asmau ta durkusa har kasa ta gaishe shi ya amsa fuska a sake. Mama ta turo masa Amatullah gabansa ya rungumeta sosai kamar bai taba jika ba. Tausayin rayuwarta yake ji da irin abinda suka fuskanta ita da mahaifiyarta. Bayan an zauna an dan yi hira Nasiba ta dauko wani hoton Abubakar ta nunawa Amatullah dake zaune akan cinyarta.
"Mamana kinga Babanki"Kan Amatullah ya fara rikicewa tace "shi wannan yana ina".
Falon sai yayi shiru Asmau tana ganin hoton ta sai kuka aka rasa mai rarrashinta domin su ma kukan suke yi. Amatullah ta koma gaban Asmau tace "Ummi ko wannan baban ne ya tafi aljannah shiyasa ban ganshi ba?"
Wannan tambayar tata tasa hatta Alh Adamu sai da yaji kwalla ta cika masa ido. Muryar a raunane yace "Safina bazai dawo ba kinji. Addua zamu rinka yi masa"
Da dan murmushinta tace "ai munayi ni da Ummina, sai muce Allah Ya jikan Babana Ya sashi a aljannah. Muma zamu je wurinsa idan Ummi ta tara kudi"
_Innalillahi wa inna ilaihi rajiun_. Duk wanda yasan Abubakar a wurin sai da ya zubar da hawaye. Babu ma kamar Asmau da kuma Mama Yalwa. Baba yayi gyaran murya saboda kukan ya zama babu babba babu yaro, shi kansa sun gama karyar masa da zuciya.
"Ina tunanin yau ba ranar kuka bace garemu. Allah Ya amsa adduarmu Ya dawo mana da 'yarmu lafiya da abinda ta haifa. Wannan ya ishemu farinciki da godiya ga Allah. Allah Ya kara tsare mana zuria da sauran musulmi daga fadawa tarkon shaidan. Shi kuma Abubakar Allah Ya karbi tubansa Ya yafe masa.""Amin" suka amsa baki daya sannan Baba ya tashi ya shiga dakinsa ya matan da su Qasim. Duk jikinsu yayi sanyi an kasa yin hira kamar yadda suka ci burin yi idan an hadu da sauran 'ya'yan gidan. Abdulhalim ne yayi ta maza ya shiga nunawa 'ya'yansu Amatullah da kuma matsayinta a garesu. Daga haka shirun da akayi ya dan ragu har aka fara hira.
Asmau ke tambayar Rashida da Zubaida yadda suka hadu dasu Umma. Ai kuwa suka bata labarin komai game da zuwan Zubaida Kano. Rashida tace "haduwarmu dake alkhairi ta haifar tunda gashi duk mun zama 'yan uwa. Sannan Zubaida ta sami irin rayuwar da take buri."
"Alhamdulillah. Nima alhairin kuka janyo min domin kun taka muhimmiyar rawa wurin ceto rayuwata daga shiga gagari. Ina Yaya Tagwai da Kawu Sada?"
Aka kwashe da dariya. Yaya Tagwai har yau basa shiri da Hajjo duk da ta dage itama ana zumuncin da ita domin ta bawa Umma hakurin korar Asmau da tayi. Sada kuwa yace yana nan zuwa Kanon tare dasu Abba sai su koma Azare da Rashida.
Juyawa tayi ga Zubaida tace "kin kara ganin Uwargida kuwa"?
Da sauri Zubaida tace "Allah Ya kiyaye wallahi. Tunda Allah Ya rabamu ni fa ko Azare ban kara zuwa ba."