ABINDA AKE GUDU🙆🏽39
Batul Mamman💖
Tsabar bacin rai yasa yayi wani irin cin taya sannan yayi parking din motar. Duk jikinsa tsuma yake yi, zai iya rantsewa bai taba jin kishi makamancin wannan ba duk tsahon rayuwarsa.
Asmau ma tuni ta hadiye dariyarta gabanta na faduwa. Duk da bata ganshi ba amma ta gane motar. Sai taji ta tsani kanta da har tayi abinda zai bata masa rai. Amma laifinsa ne don ranar da suka dawo yace zai zo shiyasa yau ta fito wurin Qasim da kwarin gwiwarta. So take yi ta fara sallamarsa sannan shima wanda yayi nasarar samun soyayyar tata ta nemi su rabu. Duk iya tunaninta karatu ne kawai mafita garesu ita da Amatullah.
Qasim bawan Allah ya kula da yadda ta canja lokaci guda har ya fara tunanin waye a motar. Motar ya rinka kallo da Asmau.
******Kamar ya juya haka ya rinka ji sai dai kuma hakan ba girmansa bane tunda har ya shigo gidan. A zuci ya karanta *Hasbunallahu wa ni'imal wakeel*har yaji bacin ran ya ragu sannan ya fito yana zuba _kamshi_. Taku yake daidai har ya iso kusa dasu. Kamshin turarensa da yake sanya Asmau nishadi ne ya fara ziyartar ta. Taji bugun zuciyarta ya tsananta. A iya saninta da Jikamshi baya boye magana ko gaban waye. Bata san me zai ce a gaban Qasim ba, mutumin da bai cancanci wulakanci ko kadan ba daga gareta.
Yana karasowa ya saki fuska duk da ta ciki na ciki ya mikawa Qasim hannu yayi masa sallama.
Qasim ya karbi hannun shima cikin fara'a ya tashi suka gaisa. Sai kuma suka kalli Asmau suna jira ta gabatar dasu. Tsuru tayi da ido kamar wadda tayiwa sarki karya.
Da kyar ta saita kanta tace "Yaya Qasim ga baban Amatullah da nake fada maka. Col. I M Jikamshi."
Sake kama hannunsa Qasim yayi yana murmushi "naso ace har gida nazo na sameka domin kara mika godiya bisa taimakon da kayi mana. Allah Ya saka da alkhairi Ya bada lada. Ashe manyanmu ne masu tsaron kasa. Bari na baka girmanka yallabai."
Gyara tsayuwa Qasim yayi ya daidaita kafafunsa sannan yayi saluting Jikamshi. Shima murmushi yayi ya tsaya a attention ya mayar masa da salute din duk suka yi dariya banda Asmau.
Col. Ishaq yace "ka kirani Ishaq kawai. Asmau bata iya kiran sunana kai tsaye ne shiyasa kaji tana maka kwana kwana ko" ya fada yana mata kallon da ke kara kashe mata zuciya. Ta sunkuyar da kanta kawai. Abinda take gudu kenan ya bata kunya a gaban Qasim.
Ta daure tace "ga Yaya Qasim shi dan sanda ne"
"Allah Sarki, its a pleasure meeting you. Ai ta bani labarinka. Kune manyan ai muna bayanku. Baka ji ana cewa abokin kowa dan sanda" Col Ishaq ya fada yana kara kallonsa zuciyarsa fal kishi yana ta kokarin dannewa.
"Nima ta fada min yadda ta hadu daku. Muna kara godiya."
"Kada ka damu ai yiwa kai ne. Amma me kuke yi a waje haka ga kura? Ina tsammanin damuna ta kusa tsayawa dai" yadda yayi maganar Asmau ce ta fahimci da biyu yake yi.
Shi kuwa Qasim ya dan sosa kai yana dariya. Ko babu komai Jikamshi ya girme shi "Yallabai kenan. A tayamu addua dai muna nema ne"
Wani abu ne ya tokarewa Col Ishaq makoshi yaki sauka kasa. Wai ya taya shi addua. A zuciyarsa yace (Allah Yasa kada ta taba yi maka soyayya irin ta mace da namiji.). Abu daya ke yi masa yawo a ka shine kada Asmau ta juya masa baya. Wannan Qasim din wani sanyi ne gareshi mai sa mutum yaji dadin mu'amala dashi.
A fili kuwa murmushin yake yayi "ah to bari naje naga Amatullah sai na tafi. Dama ita nazo gani kewarta ta isheni" daga nan gefe ya matsa ya kira Yassar. Bai dade ba ya fito ya shigar dashi ciki. Ransa a bace da ya hango Asmau da Qasim yana taya Jikamshi kishi.