ABINDA AKE GUDU🙆🏽25
Batul Mamman💖
Cikin matsanancin tsoro Asmau ta juyo tana kallon matar. Hakuri ta soma bata murya na rawa ga hawaye na wanke mata fuska tana sanar da ita bata da kudi kuma bata kowa da zai taimaketa. Matar sai tayi murmushi "kada ki damu ni ba wani abu zanyi miki bane. Hasali ma na rasa dalilin da yasa tun da na shigo dake cikin asibitin nan hankalina yake kanki. Amma dai biyoni mu koma ciki".
Ba yadda ta iya haka tabi bayan matar suka tafi wurin wata mai sharar. Matar babba ce don da gani zatayi sa'a da Umma. Wadda ta biyo ta gaisheta cikin ladabi sannan ta gabatar da Asmau a matsayin 'yar uwarta wadda bata da komai. Rokonta tayi akan ta ranta mata kudi su biya a sallameta ita kuma tayi alkawarin biyanta a hankali cikin albashinta.
Babbar matar ta kalli Asmau tayi wuri wuri da ita tana jijjiga goyonta. Da gani ma a tsorace take tace "kudin ba wasu masu yawa bane Zulaiha, ga wannan kije ki biya. Sai mu warware daga baya. Ki gaida mutan gidan."
Zulaiha tayi mata godiya itama Asmau ta saka baki suka yi tare. Bayan sun fito ne Asmau ta rasa bakin godewa wannan matar mai suna Zulaiha. Matar bazata girmeta da yawa ba. Tuna mata take da Anti Rashidan Azare. Bayanta tabi suka koma wurin likita aka sallameta duk da yaso kwarai ta kai washegari.
Zulaiha tace "babu komai yiwa kai ne. Bari na canza kaya nazo muje gidana tunda dare yayi".
Asmau sai mamaki take yi meyasa wannan matar ta taimaketa alhali bata san komai a game da ita ba. Suna fita daga asibitin bus suka hau maleji suka sauka a wata unguwa da Asmau bata sani ba. Daga nan suka bi cikin lunguna suka karasa wani gida mai karamin gate. Idan kaga gidan dole zakayi tunani masu shi suna da rufin asiri. Sai ka shiga zaka ga babu wasu abubuwan more rayuwa. Yara ne har shida suka fito suna yi mata sannu da zuwa ta amsa fuska a sake sannan suka gaishe da Asmau. Zulaiha ta dauki karamin ciki da baifi shekara ba ta soma shayar dashi. Falon da ta kai Asmau ko leda babu ta dauko tabarma ta shimfida mata.
Yaran ta tambaya ko su kadai ne a gidan suka ce eh. Babbar cikinsu mace ce da bata fi shekara tara ba sai namiji dake binta. Duk yaran babu wata tazara tsakaninsu. Ta dauko naira hamsin daga gefen zaninta ta bawa namijin "Muhsin siyo mana kan kifi, ke kuma Humaira dauko attaruhu hudu da rabin albasar nan ta safe ki jajjaga min. Sannan ki dauko katuwar tukunyar nan ki wanke a cikata da ruwa yanzu zan zo na dora"
Da murna yaran suka fita tunda suka ji batun kan kifi sun san yau gidan za'a ci dadi. Asmau na nan zaune Zulaiha ta kunna kyandir sannan ta tashi ta dora mata ruwan wanka ita da baby ta kuma dora girki.
Wankan Zulaiha ta fara yiwa jaririyar itama Asmau tayi da taimakonta dai. A ranta sai mamakin matar take yi. Haka kawai daga haduwa sai taimako? Bayan tayi wankan taji dadin jikinta tana zaune Zulaiha ta sakawa jaririyar kayan karamin danta Ali irin wanda suka yi masa kadan. Allah Sarki wannan jaririya ko kayan sakawa bata dashi. Ta gama ta nado mata ita a zani ta bata sannan aka kawo mata dafadukan taliya 'yar hausa harda yaji da ruwa. Asmau ta zauna ta narki abincin nan tana yi tana godiya. Sai da ta koshi sannan Zulaiha ta tambayeta sunanta da kuma abinda ya fito da ita. A nan Asmau ta soma kuka. Tana yi tana bawa Zulaiha labarinta mai cike da ban tausayi da gargadi ga sauran mutane. Sosai Zulaiha ta tausaya mata. Tace
" Tun da na ganki haka nan Allah Yasa naji ina son na taimaka miki. Kinga nima ba wani abu gareni ba. Ganinki da nayi sai ya tuna min da tawa rayuwar shiyasa na zabi na taimakeki ko Allah zai kawo min sassauci a cikin kuncin da nake ciki. Kinga dare yayi ki kwanta zuwa gobe zaki san nawa labarin. Allah Yasa ki sami ruwan nono da wuri kafin hakurin 'yar tamu ya soma karewa ta fara kuka".Murmushi Asmau tayi tana kallon fuskar 'yarta ta hasken kyandir. Sun tashi Zulaiha zata nuna mata dakin da zata kwanta don gidan akwai dakuna suka ji an shigo falon.