ABINDA AKE GUDU🙆🏽31
Batul Mamman💖
Bai san wane irin labari yayi zaton ji daga gareta ba amma ko da wasa baiyi tunanin zata fadi abinda take fada yanzu ba. Dari bisa dari ya gaskata ta saboda yana da yakinin babu macen da zata bude baki da gangan tace 'yarta ba da aure ta haifeta ba. Da yawa zasu yiwa zancen kwaskwarima ta hanyar cewa fyade aka yi musu ko iyaye suka koresu ko kuma miji ne ya mutu ya barsu da yara. Jin ta yake yi sosai a jikinsa har dana sanin matsa mata ta fadi sirrin rayuwarta yayi.
Asmau na hawaye ta kare labarin da haduwarsu da Haj Lubabatu sannan tace "nasan duk wani sauran mutuncina da kuke gani ya gama zubewa. Naso mu rabu kuna min kallon makaryaciya ba mazi....."
Haj Lubabatu ta dakatar da ita da sauri "ya isa haka Asmau. Hakika banyi zaton jin haka daga gareki ba. Lallai kinga rayuwa wadda da yawanmu duk shekarunmu na duniya bamu ga tashin hankali makamancinsa ba. Da yardar Allah zamu taimaka miki ki koma gaban iyayenki duk da kince baki sani ba ko zasuyi murna da dawowarki. Kuma idan har da gaske baki taba sayar da mutumcinki ba a waje bayan kin bar gida ko yin wata sana'a haramtacciya sai ince ki godewa Allah. Domin tabbas nasan harda adduar iyaye da rahmar Mai kowa Mai komai."
Asmau tayi saurin cewa "wallahi Hajiya ban taba mu'amala da kowa ba. Duk tsahon lokacin nan nayi kokari Allah Ya taimakeni na tsare mutumcina."
Tana magana Col. Ishaq yana kallonta cike da tausayi. Haj Lubabatu tayi murmushi irin na dattijai "na yarda dake Asmau. Labarin da kika fada abu ne da babu macen da zata yiwa kanta kagensa. Sai naji gabadaya waya ta fice min a rai. Hakika dolene mu taru mu kiyaye me muke karantawa ko rubutawa mu turawa wasu a waya saboda kada muyi sanadiyar lalacewar tarbiyar wasu. Rashin taimakawa mutanen da suka sami kansu a irin wannan halin shi yake ingiza masu raunin imani su fada tarkon shaidan sosai. Ba don Allah Ya kiyayeki ba da Allah kadai Yasan hannun da zaki fada. Ni ganau ce a irin wannan al'amarin."
Ishaq ya dago ya kalli Hajiyarsa, ita kuwa ta cigaba da cewa "akwai aminiyata da muka tashi tare 'yar Limanin unguwarmu. Lokacin bamu fi shekara shahudu ba tayi ciki. Duk inda tarbiya take mahaifanta sun bata to amma kunsan Allah ke shiryawa. Da magana ta fito babu irin kyama da kyarar da bata gani ba. Mu kanmu duk gudunta muka yi. Liman kuwa tsine mata albarka yayi. Haka ta tafi tana kuka tana rokon a yafe mata babu wanda ya saurareta. Sai da girma yazo min na gane rashin kyautuwar abinda aka yi mata." Ta dan numfasa tana kada kai "ina ganin mu bar komawarki gida sai Juma'atu babbar rana, nan da kwana uku kenan. Ki dan gyara kanki da Safinatu kada ku koma a jeme ko yaya kika gani?"
"Duk yadda kika ce Hajiya da yau da Juma'ar duk daya ne a wurin Allah"
Hajiya ta shige ciki tace Asmau tazo tayi wanka.
Bayan tafiyarta Asmau duk ta takura saboda irin kallon da Ishaq yake yi mata. Kunyarsa ma take ji. Ajiyar zuciya yayi wanda yasa ta dan dago kai amma bata bari sun hada ido ba
"Ummin Safina kiyi hakuri"Da mamaki ta kalle shi "hakuri kuma? Na me?"
"Shiyasa addininmu ya hana tsananta bincike a abinda babu ruwanka. Sai nake ganin kamar na shiga hurumin da ba nawa ba da na matsa miki naji sirrinki. Amma kuma naji dadin sani saboda a yanzu bani da burin da ya wuce zamewa Safina uba"
Asmau tayi murmushi irin wanda bai taba gani daga gareta ba. Gani yayi tayi masa kyau duk da fuskarta ta kumbura saboda kuka. Saurin kawar da kansa yayi gefe. Tace
"Nagode Allah Ya saka maka da alkhairi"Tashi yayi tsaye "meye na godiya kuma. Ni dai abu daya nake so dake ki dena koyawa Safinata *kayya* ko musa kafar wando daya dake"
Bata san lokacin da tayi dariya ba sai kuma tayi saurin rufe fuskarta "ranar ma akasi aka samu ba halina bane. Ka rinka kiranta Amatullah sunan kaka taci"
Col Ishaq yaji dadin yadda ta sake "Nafi son cewa Safina. My Princess ko ban isa ba?"
Asmau ta dan zaro ido "babu ruwana"
Daga nan shigewa yayi ciki yana dariya ya barta a tsaye. Inda Hajiya ta shiga itama tabi baya.
Komai da zata bukata na wanka Hajiya ta bata ta zauna ta gyara jikinta. Tana fitowa taga Amatullah da daure da tawul amma Bilkisu ta wanke mata kai an taje yasha mai ga ribbon an kama mata shi ta rinka yi mata godiya. Hajiya ta shigo duk kunya ta kama Asmau har ta kula "don Allah ki saki jikinki idan ba haka ba zan fasa kaiko wurin Umma"
Kanta a sunkuye tayi murmushi tana bata hakuri.
Akwatinsu ta bude ta daukowa Amatullah kaya. Bata ankara ba ta karbe kayan ta fice da gudu wai Babanta ne zai saka.
Bilkisu da Asmau suka rinka kiranta taki tsayawa. Haj Lubabatu ta rike haba "gaskiya akwai matsala idan kuka tafi. Kinga ikon Allah ta saba dashi sosai."
Amatullah ce ta Bilkisu suka shigo da gudu tana kuka wai an hanata zuwa wurin babanta. Muryarsa suka ji a kofar dakin yana cewa ko dai Bilkisu ta barta ta fito ko ya shigo. Asmau ta ware ido a tsorace. Hajiya kuwa dariya tayi don ta tabbatar bazai shigo din ba. Har fada ya soma yiwa Bilkisu Hajiya tace su kyaleta ta tafi. Sai gata ta shigo daga baya ya saka mata kayan ga zani yana binta daga baya kuma taki yarda a gyara.
*****Sababbi riguna 'yan kanti masu tsada Col Ishaq ya siyowa Amatullah da takalma. Kafin juma'ar har gida Hajiya ta kira mai kitso aka yi musu. Sai gashi sunyi fes. Daren juma'ar kuwa Asmau kasa baccin kirki tayi tana ta addua Allah Yasa su karbeta. Tsoro ne ya cika mata zuciya da ta tuna bata san ko suna nan ba. Har asuba tana sallah da kai kukanta wurin Allah.
Washegari ranar da take jira tazo. Col Ishaq yace su jira ya dawo daga wurin aiki bayan masallaci su tafi. Ko abinci ranar Asmau bata iya ci ba. Haj Lubabatu ta sakata a gaba amma da kyar ta iya shan rabin kofin tea.
Da Ishaq ya dawo wanka yaje yayi ya shirya ya fito yana mai amsa sunan garinsu Jikamshi, domin kuwa kamshin yake mai dadi. Amatullah an saka mata daya daga cikin rigunanta. Tayi kyau sosai, Asmau harda hawaye tayi ta musu godiya.
Bilkisu kawai aka bari a gida kamar kada su rabu da Amatullah. Hajiya da Asmau na baya, Col Ishaq yana tuki ga Amatullah a gefensa.
Da kwatancen da Asmau take yi masa suka isa har bakin gate din gidansu. Zuciyarta sai bugu take yi kamar zata fito.A wajen yayi parking ita da Hajiya suka shiga tana rike da hannun Amatullah.