ABINDA AKE GUDU🙆🏽58
Batul Mamman💖
A daddafe take iya yin komai. Cikin da alama mai laulayi ne domin bata son warin komai ga yawan tashin zuciya. Rashin wadataccen abinci yasa ko aman yazo sai dai tayi wahalar banza babu komai a cikinta. Cikin dan lokaci ta fada. Babu wanda ta iya fadawa damuwarta sai Allah. Kullum sallah take da karatu tana mai tsananta addua da neman mafita. Idan ta damu da yawa ta kira Umma suyi hira taji sauki a ranta.
A nasa bangaren Col. Ishaq ba karamin jigata yayi ba da rashin Asmau. Sonta yana nan a ransa amma yana kyamar halin da ta jefa su a jiki. Har yau ya rasa matakin da zai dauka bayan fita harkarta da yayi. Gidan yayi musu zafi duk su biyun. Gado daya suke kwana ya juya mata baya. Haka zata yi bacci tana kallon bayansa tana hawaye.
Ranar asabar lokacin sun dauki sati uku a wannan yanayin tana fitowa daga kitchen shi kuma zai shiga daukan cup ya hada tea. Kallon kallo suke yiwa juna ta matsa ta bashi hanya. Yana shiga ya bugo kofar da kafarsa ashe hannunta na wurin kofar ta matse. Ciwo taji har tafin kafarta tayi kara cikin zafin nama ya bude kofar. Hannun ta rike sosai tana fitar da hawaye ta kasa tsayuwa wuri daya don azaba. Mantawa yayi da fushinsa da komai ya kama yatsun nata biyu da yaga ta rike ya shigar da ita kitchen ya sakar mata ruwa. Idonta a rufe tana kuka a hankali. Ciwon bai dameta ba kamar yadda Jikamshinta ya canja mata.
Har zuciyarsa yake jin kukan tana bashi tausayi sosai. Ya soma hura mata yatsun amma yana gani har sun fara kumbura. Fuskarta yake kallo itama yau bata kawar da nata idon ba ta zuba masa ido. Yadda ta rame shima haka ya rame. Yana rike da hannun ya kai yatsun nata bakinsa ya saka a ciki. Kallonsa kawai take tana kara sonsa duk da halin da suke ciki a lokacin. Kusan minti uku yatsunta na bakinsa sannan ya cire yace "kinji sauki ko nasa miki kankara"
Yaushe rabon da yayi mata magana. Ita da jin muryarsa sai dai idan waya yake. Girgiza kai tayi ta janye hannunta ta tafi. Wani iri yaji, yunwar ma ta fita a kansa sai rudani na rashin sanin yadda zaiyi da Asmau. Dakinta ya bita ya sameta zaune a kasa a kuryar gado tana kuka a hankali. Bai ce mata komai ba ya bude inda take ajiye mayafai ya dauko mata wani kato mai kauri. Tayar da ita yayi tsaya ya yafa mata sannan ya riko hannunta suka fito falo ya dauki mukullin motarsa.
Cigaba yayi da jan hannunta har gaban mota. Ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya cewa Mal Sabo idan ya dauko Amatullah ya kaita gidan Ismail. Sai ta kula ya mikawa Mal Sabon wata karamar jaka wadda take tunanin kayan Amatullah ne a ciki.
Da ya zauna ya tayar da motar Ismail din ya kira ya fada masa za'a kawo Safina kila ta kwana. Shi kuwa sai murna yace dama yana gida.
*****Barrack dinsu suka je bangaren asibiti. Ita dai binsa take a baya har suka shiga ciki. Wani office ya shiga ya barta a reception. Ba dadewa ya fito yace ta shigo.
Hussaini ne a ciki sanye da kayan sojoji amma ya dora coat din likitoci.
"Ranki ya dade sai ki zauna a waje kuma? Sir kasan fa ita ce mai hadani da Walida ya kamata ka tayani kamfen"Duk su biyun ya kula babu wanda dan guntun wasansa ya bawa dariya. Shima sai ya ci serious ya koma mazauninsa. Yasan yau abokin nasa a matsayin shugabansa ya shigo.
Col. Ishaq ya kamo hannunta da ya matse wanda yatsun sun kumbura faratan kuma sunyi jawur alamar taruwar jini daya har ya fashe ta saman farcen "Doctor a duba mata hannun nan bana so ya zama babban ciwo"
Hussaini ya kallo hannun sai ya dauki waya ya kira nurse aka zo suka tafi da Asmau yace ayi mata dressing. Bayan sun fita yace "ai yadda na ganku ne har naji tsoro ko anyi fadan masoya ashe amarya ciwo taji"
"Kaga ba batun wasa ina so duk wani test da akeyi a gano ciki kayi mata please"
Hussaini ya mike da sauri "Sir ciki??? Iko sai Allah, bashi da abokin tarayya. Lallai Allah maji rokon bayi."