ABINDA AKE GUDU🙆🏽33
Batul Mamman💖
Gidan suna dai ya koma wurin zuwa kallon Asmau da 'yarta. Bayan anyi sallar la'asar ne ta tuna da Col. Ishaq da ya kawo su. Dafe kai tayi saboda tasan bata kyauta ba. Ganin su Umma yasa ta manta da kowa. Shema'u ta fadawa cewa dan matar da suka zo tare shi ya kawosu kuma yana waje. Haj Lubabatu tana jinsu sai dai kunya ta dan fari ta sanya taki tuna mata dashi. Kuma tasan yau rana ce mai matukar mahimmanci a wurin Asmau. Ta hadu da iyayenta da 'yan uwa bayan tsahon lokaci. Shema'u ta sanar da Umma. Nan da nan aka samu food flasks aka hada masa duk wani na'uin abinci na gidan sunan. Jafar aka kira akan su wuce gidansa domin bako ya samu yaci abinci ya huta.
Jafar da Sabira suka fito dauke da kayan abincin tare da Asmau dake binsu a baya rike da hannun Amatullah. Zaune yake a gaba ya kwantar da kansa a saman kujera yana sauraron karatun Al'Qur'ani kira'ar Shiek Mishary Rashid. Tausayinsa Asmau taji saboda kunyar abinda tayi masa. Babban mutum kamarsa sun shanya shi a kofar gida. Kuma ta tabbatar baici abinci ba kafin su taho. Yana dawowa daga masallaci ko zama baiyi ba yace su taho kawai.
Amatullah ta tafi da gudu ta fada jikinsa. Hakan yasa shi saurin bude ido yana murmushi. Jafar ya karasa gaban motar ya mika masa hannu suka gaisa.
"Kayi hakuri don Allah an barka a waje tun dazu. Duk laifin Idon kuka ne da bata fada mana tare kuke ba"
Col. Ishaq yace "Idon kuka kuma?"
Dariya Jafar yayi kana ganinsa kasan yana cikin farinciki, ya nuna Asmau "ai sunanta kenan."
Kyakkyawan murmushi Col. Ishaq yayi yana kada kai "sunan ya dace da ita"
Duk akayi dariya sannan Jafar ya fada masa yana son ya biyo shi gidansa domin yaci abinci. Da farko Ishaq ya nuna baya jin yunwa sai da Asmau ta bashi hakuri tare da rokonsa. Yayi yar dariya
"Haba Idon kuka, bayan ko introducing dina a wurin yayanki baki ba?"
Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Jafar ya sake mika masa hannu murmushinsa yana kara fadada "nima da laifina, sunana Jafar ni Asmau take bi,wannan matata ce Sabira. Idan kaci abinci zamu shiga ciki ka gaisa da duk 'yan uwa."
Col. Ishaq ya dafa kan Amatullah "ni kuma sunana Baban Safina"
Sabira ta kalli Asmau "kice kawai biki zamu sha kwanan nan"
Da sauri Asmau ta daga hannuwa "ba haka bane, Ama ce kawai take kiransa babanta. Sunansa...."
Shiru tayi duk suka zuba mata ido. Kunya taji ta kasa fadin sunan sai ta wayance tace ya kamata su tafi saboda kada abincin ya huce. Col. Ishaq ya nuna su shiga motarsa.
Jafar ya shiga gaba, Sabira na baya sai Amatullah da ta dage zata bi babanta. Asmau tana tsaye suka ja mota suka tafi ta koma ciki.
Hira aka dora daga inda aka tsaya. Shema'u tana goye da Abid din Sabira sai jijjiga shi take kafin Sabirar ta dawo.
*****Mata kamar kara turo su akeyi gidan ana ta zuwa kallon Asmau. Hajjo duk ta matsu su firfita don su samu ayi hira yadda ya kamata da Asmau. Duk dakin da ta shiga mata ne harda wadanda ma basu zo ba da farko. Su Umma ma dai kara kawai suke yi amma duk a matse suke da a basu fili suyi hira da 'yarsu. Da suka ga abu yaki karewa Hajjo da kanta ta shiga falo rai a bace tana mita yadda masu hankali zasu fahimta
"Kai jama'a ace anzo taron suna anci tatsotse dinnan anci salak, anci tuwo anci wannan anci wancan amma mata sai tururuwa suke yi. Fisabilillahi ko irin karar nan ta a fita a bamu waje da jikarmu muyi hirar yaushe gamo ya gagara".Wasu nan suka fara jin kunya suka fara hada kayansu suna fita. Sauran da suka yi biris kuwa Hajjo ta rufe idonta ta sallamesu. Umma da Mama dai sunji kunya to amma halinmu na mata wurin saka ido da bin kwaf ya janyo musu.