ABINDA AKE GUDU🙆🏽53
Batul Mamman💖
Amsa sallamar tasa tayi suka gaisa a mutunce. Shiru ya biyo baya ya katse shi ta hanyar tambayarta ya maigidanta da danta Nabil. Dan gyaran murya tayi tace
"Uhmm Ishaq dama dazu naje yini gida ne aka bani katin bikinka. Ashe aure zakayi babu labari"
"Badar kenan, kina gidan mijinki ai bai kamata na kiraki nace zanyi aure ba. Dama Hajiya tace zata aika cards nasan zaki ji labari"
Rayuwa kenan, mutumin da suke matukar son juna gashi yanzu akwai katanga mai karfi tsakaninsu. Tayi dan murmushi. Wayar ma sai da ta nemi izinin mijinta dama ta kira saboda kare hakkin aure. Zancen ba'a son ranta akayi auren ba tuni ya wuce da ta sami ciki.
"Allah Ya sanya alkhairi na bugu inyi maka dama. Sai dai naji wani labari a gida da ya tada min hankali...."Katseta yayi wayar ta fara isarsa. Abokai da mutanen da bai ba sani ba duk sun ishe shi da irin wannan maganar. Ga kiran Asmau yana ta shiga call waiting.
"Cewa Asmau tana da 'yar da ta haifa babu aure ko? Haka ne abu daya kawai zakiyi min shine adduar da kika yi ta Allah Ya sanya alkhairi ki cigaba da yi"Maganarsa batayi mata dadi ba "idan saboda rashin haihuwa ne don Allah ka nemi wata mai 'ya'yan. Me zakayi da wadda ta gama yawonta a gari?"
Runtse ido yayi ransa na kara baci. Haka ce zata yi ta faruwa kenan ko bayan aurensu. Albakarcin zaman tare da son da yayi mata a baya ya hana shi fada mata maganar da zata dade tana mata ciwo a rai.
"Kema kinsan bazanyi aure irin wannan ba. Ina son Asmau da zuciya daya. Anyway nagode da wayar taki. Ki gaida mijinki"Ya katse wayar Mami tace "kayi hakuri Yaya. Nasan bazai wuce irin maganar da mukayi ba ita ma shi tayi. Sai an sami mai zurfin tunani ne zai nemi jin ainihin labarin Asmau kafin ya yanke muku hukunci."
"Gaskiya ne, Allah Ya kyauta. Babu mai iyawa mutane sai Ubangijin da Ya haliccemu. Komai kayi a wurin mutane baka iya ba a wurin wasu."
Dakinsa ya tafi ya kira Asmaunsa yana bata hakurin rashin jinsa da tayi. Dayake tasan yana aiki tace babu damuwa. Sunyi hira wadda duk akan abinda ya shafi biki ce sannan ta kwanta.
*****Ranar Jumaa gidan Umma tun safe ya cika da jama'a duk da a katin an rubuta ba a gidan za'ayi kamun ba. Mutane sun rasa daga inda wasu ma suke zuwa. Abin mamaki sai ga Sagira matar Rabe da 'ya'yansu matan. Duk ta yamushe rayuwar kauye babu dadi. Umma batayi zaton zasu zo ba ganin da Asmau ta dawo an aika musu. Hajjo ce ma ta hana Asmaun zuwa Dakasoyen ta gaishe da Kawu Raben saboda shima ya dauke musu kafa. Gashi dai shine da laifi amma yafi kowa fushi.
Su Anti Lami da Yaya Abu duk sun iso da safe da yaransu har na gidan miji. Abu yayi kyau ko babu komai dai dangi ba'a canza su.
Lalle aka zauna yi mata ja da baki wanda aka bata lokaci wurin yinsa. Tasha zama kuwa don 'yan uwanta sun dage bazata cire da wuri ba sai ya fito sosai yadda za'a jima ana cin amarci.
Ana idar da sallar jumaa aka fara wanka don gidan Umma, Mama da na Jafar duk babu masaka tsinke. Itama Asmau kafin a kira la'asar tayi wankanta mai kwalliya Najah tazo ya fara aikinta. Fuska ta dauka don Naja ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi mugun fentin nan na foundation ba da fuskar mutum take canzawa gabadayanta. Ana gamawa ta tashi tayi sallah aka sake gyarawa sannan ta saka kaya. Idan ka ganta a lokacin bazaka ce Asmau mai wankin bandaki bace a asibitin Jos. Tayi kyau ba kadan ba. A lokacin yawancin matan dake gidan sun tafi venue din. Yaya Abu ce ta kira Zubaida akan lallai su taho da amarya da wuri mutane sun soma cika a wurin. Ita har mamaki take yi wasu daga ina suka zo.
Wata mota ango Ishaq ya turo mai kyau ta daukar amarya zuwa wurin biki. Da suka isa ita da Walida da Zulaiha ne a motar. Safiyya tazo tace ta zauna domin ango yana hanya sai ya iso zata fito. Ta saki wani murmushin jindadi bayan Safiyya ta tafi. Zulaiha ta ce
"Hmm Asmau amare na dan kuka rana irin ta yau sai fara'a kike yi."