ABINDA AKE GUDU🙆🏽16
Batul Mamman💖
Wannan karshen satin tun alhamis Abubakar yazo. Kullum sai yaje wurin Asmau sunyi hirarsu yadda suka saba. Ranar asabar ya wuce Shanono wurin Qasim suka je daurin auren wani dan uwan Qasim din. Daga nan suka koma gidansu sai zuwa yamma yayi niyar komawa cikin Kano.
Zaune suke a dakin Qasim suna kallon ball wayar abokin nasa tayi kara. Rage sautin TV din yayi ya amsa wayar. Ya dan jima suna hira d wadda Abubakar ya fuskanci mace ce sai daga baya yaji akalar hirar ta canja. Qasim yana tambayar yarinyar wane irin kaya ta saka.
Murmushi yayi bayan ta bashi amsa "me kika saka a ciki?"
"Ni kwance nake a daki da shorts(gajeren wando) ina shan iska ina tunaninki" (karya yakeyi. Kufta da wando ya saka).
Irin wannan hirar ya kusa rabin awa suna yi da budurwarsa. Abubakar sai kada kai yake don takaicin wannan hali na Qasim. Yayi fadan da nasihar har ya gaji gashi ya kasa rabuwa dashi saboda shakuwarsu. In dai hirar banza ce a waya to Qasim ya ciri tuta. Sai ance ya fidda matar aure yace duk mata babu tagari.
Mugun kallon da Abubakar yake jifansa dashi yasa ya katse wayar yana dariya.
"Ya Ustaz irin wannan harara haka. Ni fa bance ka tsaya jin hirar ba duk ka wane hade rai."
"Yanzu bazaka dena wannan muguwar dabi'ar ba? Ina jiye maka tsoron kada watarana kayi me gabadaya. Kasan zuciya bata da kashi".
Kujerar kusa da Abubakar ya dawo ya zauna.
"Kaima kasan duk abuna bazan yarda nayi lalata da 'yar mutane ba. Irin wannan hirar dai da dan abinda ba'a rasa ba shi muke yi don mu rage yawa.
Sanin kanka ne yadda aure yayi tsada ni kuma ba wani abu na tara ba. To kuma ga abu mu muna so suma matan suna so. Sai a taimaki juna".
Runtse ido Abubakar yayi "ji yadda kake cewa a taimaki juna kamar wani aikin kwarai. Kana dan malam har ka manta haramcin taba jikin macen da ba muharramarka ba? Ko ka manta inda Allah SWT Yake cewa : *WALA TAQRABUZ ZINA INNAHU KANA FAAHISHATAW WA SAA'A SABILA*
(ISRA' 32)Ma'ana _KUMA KADA KU KUSANCI ZINA DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA HANYAR BATA_
Taba jikin budurwa da niyar gusar da sha'awa batare da kunyi abin gabadaya ba yana cikin abinda Allah Yayi hani dashi. Kallo wannan da irin maganganun nan da kuke yi duk yana ciki. Wata rana sai kaga anyi abinda ake gudu azo ana cizon yatsa."
Qasim yayi murmushi jikinsa ya danyi sanyi sai dai shaidan bai barshi ba.
"Naji kuma duk nasani to amma ka manta cewa Allah SWT mai yawan gafara ne da jinkai? Idan mutum ya aikata irin haka tuba fa kawai zanyi a kankare min zunubin. Haba Abubakar kaima kasan yadda zuciya take. Ni a haka nasan ina kokari don ban taba ketawa kowace mace haddi ba. Za'ayi abin sama sama gayyar ta watse."Abubakar yace "Muna cikin wani zamani ne da hanyoyin gurbata tarbiya musamman masu nuni da zina suke da matukar yawa. Cartoon wannan sai kaga mage da bera suna kiss. Duk a haka ake lalata mana zukata. Na dade da sanin ina cikin maza masu karfin sha'awa shiyasa kaga na dage da yawan azumin litinin da alhamis. Idan naga abin zai dameni har sauran ranaku inayi. Manzon Allah SAW yace a lokacin da mutum yake zina fa babu imani a tare dashi. To me zaisa mu biyewa son zuciya haka kawai kana kan wata mace mala'ikan mutuwa ya ziyarce ka".