ABINDA AKE GUDU🙆🏽54
Batul Mamman💖
Har motarsa ta fita daga gidan Asmau ta kasa motsi kamar an kafeta a wurin. Daga ciki taji kamar ana taba kofa tayi saurin bude kofar ta shiga da sanda ga takalma a hannu. Tayi sa'a masu kwanan falo wasu sunyi bacci. Na ido biyun kuma ba 'yan tsirku bane.
Dakin Sabira ta lallaba ta shiga suma suna kwance. A ranta tace wai sun dade ne da Jikamshi a waje? Ita fa gani tayi kamar bai jima ba. Tana dukawa ta ajiye takalmanta taji ance
"Sai yanzu"Ba karamin tsorata tayi ba harda dan tsalle. Ta juya suka hada ido da Zulaiha tana murmushi.
"Meye haka kika firgice kamar an kama barawo. Kinga bakinki kuwa?"Asmau tayi saurin dora hannu akan lebenta tana rufewa don a tunaninta ana ganin abinda Jikamshi yayi mata a bakin. Ko kafin ta shigo ji take kamar a lokacin yayi. Ido a waje tace "me...me kika gani a bakin nawa?"
Zulaiha sai dariya tace "amma dai kina da matsala. Kowa ya ganki sai yasan baki da gaskiya. Yanzu yanzu kin tonawa bawan Allah asiri har na gano abinda baki son na gane"
"Da gaske ana gani? Na shiga uku. Shiyasa a falo suka bini da kallo ashe." sai kuma ta sake rufe baki da ta gane sake tonawa kanta asiri take ta shige toilet da gudu tana jin dariyar Zulaiha.
Ita Zulaiha kwanciya ta gyara tana dariya tace "dama wannan angon naki ai banga alamar wasa ba tare dashi. Goben ma gara a kaiki da wuri kada muji dirar sojoji a gidan nan".
*****Wanka Asmau tayi ta dauro alwala ta fito. Dakin dai shiru Zulaiha ma ta gyangyada. Ta dafe kirjinta oh Allah Yasa sauran basu gane ba. Amma Jikamshi ya janyo mata jin kunya sosai.
Ko mai bata shafa ba ta saka kayan bacci ta kwanta saboda gajiya. Ji tayi tana son kiransa taji ko yaje gida lafiya. Gashi har daya ta wuce idonta ya soye kamar ba wadda ta gaji ba. Tana ta tantamar kiran nasa taji wayarsa ta shigo. Saurin dauka tayi saboda kada ringing din ya tashi masu bacci.
Zaune yake akan gado ya jingina da pillow. Shima tunda yayi wanka bacci ya kaurace masa. Matarsa yake tunani da yadda yaji dadin hirarsu ta dazu. Tana dauka yace "me ya hanaki bacci"
Wannan murya ta Jikamshinta ita kadai tasan dadin da take mata. Sai taji kamar kada ya dena magana. Rufe ido tayi taki magana
"Ni ne ko? Na biya miki sabon karatu na tafi na barki da bugun zuciya"
Sake runtse ido tayi kamar yana gabanta tana jin kunyar kalamansa "ban ce ba fa"
"Ai ni nace. Kada ki manta ban dade da jin bugun zuciyarki ba a kirjina, kinsan shi baya karya. Nasan dai nawa yafi naki. Tsoronki yasa baki nutsu ba kinji zuciyar da take bugu da kaunarki. Burina na farko ya cika. Na aureki, na biyun ma in sha Allah zai cika. Shine mu sami zaman lafiya da fahimtar juna"
Tayi dan murmushi tace "Amin Jikamshina"
Kwanciya ya gyara yace "Kinsan tun yaushe nake son daukar ki? Tun ranar da kare ya biyoki. Daga ranar kika tashi daga matsayin Ummin Safina a wurina kika koma Matar Jikamshi."
"Wannan karen naka bai kyauta min ba"
"Ni kuwa yayi min komai. Ya bude kofar zuciyar Asmaun Ishaq. Ya kamata ki kwanta haka kafin gobe"
Hamma take yi amma kuma bata so ya ajiye wayar.
"Bana jin bacci. Gobe nayi idan an gama hidimar nan"Tashi yayi zaune yana kallon wayar da mamaki kamar ita ce Asmau sannan ya mayar kunnensa "ba dai a gidana ba ko?"
Asmau tace "to a ina zanyi. Kasan nan yini za'ayi babu lokacin bacci"
"Kinga Allah Ya bamu alkhairi, ki kwanta kawai ko babu baccin ki rufe idonki ki huta. Wai bacci! Matar Jikamshi anya kina sona kuwa, a ina kika taba jin anyi bacci ranar da aka kai amarya idan ba auren dole ba?" magana yake da gasken sa ya ma za'ayi ta fadi magana irin wannan.