ABINDA AKE GUDU🙆🏽49
Batul Mamman💖
Bayan tayi text din duk da hira suke mintuna kadan sai ta duba wayar ko ya aiko mata da reply. Ganin babu bai sa taji komai ba. Naci zata kafa masa har sai ya amince don dole. Wannan shine abinda ta yankewa kanta zata yi masa. Haka kawai bazata bari Jikamshinta ya kasance cikin bacin rai da sadaukarwa ba shi kadai saboda wata lalura da bai isa ya yayewa kansa ba. Wani guntun murmushi tayi ta sake daukan waya. Kafin ta fara rubuta text din taji an kwashe mata da dariya. Shemau da su Sabira ne a wurin. Asmau ta dago kai tana kallonsu. Maijego Zubaida da Ainau shayar da yaransu suke amma suna tayawa wurin yi mata dariya. Ta dan ware ido
"Me aka yi?"Sabira tace "me kuwa akayi banda kallonki da muke yi. Gaskiya wannan sojan ya cancanci a kira shi da gwarzon namiji."
Ainau ta amshe "ai baku ga komai ba ma. Sai suna tare wallahi, abin sai ya baki shaawa. Shiyasa tuni na canja takuna wurin Yaya Umar. Muma mun zama Laila Majnu"
"Lallai yaran nan kun koshi, a gaban nawa ko" Shemau ta fada amma fuskarta a sake.
Sai yanzu Asmau ta gano wai da ita suke dariyar. Ta murmusa "to me nayi yanzu"
Wannan karon Zubaida ce tayi magana "ke kadai kike ta kallon waya kina murmushi kamar yana kusa dake. Don Allah a bawa Qasim hakuri idan ya rabaku karshenta ku kamu da ciwon zuciya."
Aka sake yin dariya. Shemau tace "da dai Asmau akwai kunya amma yanzu sai a hankali. Akan _Jikamshinta_bata gane su waye a kusa. Allah Ya kaimu lokacin buki a kaiki tun asuba kafin mu laluba muji amarya ta kai kanta.
Suna dariya Asmau ta turo baki "amma kun gama dani wallahi. Kuma har yanzu da kunyata fa. Daga yau na dena magana ma"
Sabira tace "Yi abinki Asmau, idan mutum na sonka kaima ka nuna masa baka da tamkarsa. Bari nima na kira Abban Abid mu dan taba hira. Yau tunda muka fito banji muryarsa ba" sai da ta gama magana ta tuna da Shemau. Tashi tayi da gudu ta shige daki. Tsakar gidan kuwa sai dariyar su Asmau.
Sai yamma suka tashi tafiya gida. Hankalinta kwance kamar an cire mata dutse a zuciyarta. Duk da bata ga amsarsa ba ta gama yanke shawarar jurewa har sai ta shawo kansa ya amince. Ainau da Shemau tare suka tafi. Ita kuma ta bi Jafar da yazo daukar Sabira suka ajiyeta a gida.
A bayan motar tana zaune da waya a hannu Amatullah tana wasa da Abid. Text din da bata sami damar yi ba dazu ta rubuta ta tura masa.
_Don Allah kace kana sona....zanyi kuka fa._
Daga bakin gate suka sauka don lokacin har anyi magariba suna hanya. Tana tura gate din ta ga wata bakuwar mota a kusa da ta Umma. Bata damu da sanin mai motar ba ta shiga ciki tana sauri taje tayi sallah. Amatullah tace "Ummina muyi yige yigen shiga falo"
Ta bi 'yarta da murmushi "idan na riga me zaki bani?"
"Zan siya miki mota idan na giyma. Kuma zan kaiki Makkah da Madina"
"Idan kuma kika rigani me kike so?"
Amatullah tayi dariya harda alamar tunani "zaki goyani yau har nayi bacci."
"Kin girma fa Ama ga nauyi"
"to bazan ci abinci daye ba. Don Allah Ummi ki goyani" ta karashe da buga kafa.
Asmau tace "naji shirya 1, 2....." kafin ta kai 3 Amatullah ta kwasa a guje. Dariya tayi kawai tabi bayanta. Yarinya sai son goyo bata san ta girma ba. Kyaleta tayi sai da ta kusa shiga sannan ta bita da gudu. Tana sane ta bari ta rigata.
Da dariyarsu shiga falon Amatullah tana cewa ta riga. Asmau ma ta shigo da dariya sai tayi turus daga bakin kofa. Kamshin turarensa ta fara ji kafin idanunta su sauka akan Jikamshi. Shadda ce ruwan kasa a jikinsa ga hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta a kunyace. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a gidansu ba. Balle da taji shiru bai amsa sakonninta ta hanyar waya ko text ba.