ABINDA AKE GUDU 🙆🏽7
Batul Mamman💖
Ba karamin gudu Qasim yayi ba a hanya. Allah ne Ya kawo shi Shanono lafiya. Kai tsaye gidansu ya nufa. Gida ne irin ginin gargajiya amma yasha gyara ciki da waje ga sabon fenti. Duk shiririta irinta Qasim baya wasa da lamarin iyayensa. Shiyasa albashinsa duk wata a hidimar gidan yake tafiya ko tunanin aure baya yi duk da shine babba. Kanwarsa daya Jamila wadda ada yaso Abubakar ya nemi aurenta.
A soro ya tarar da mahaifinsa Mal Musa zagaye da dalibansa samari da magidanta wurin su goma. Da dai-dai Qasim ya gaisa dasu sannan ya gaishe da mahaifinsa. Yana durkusawa gaban Malam sai hawaye ya kufce masa. Ganin haka daliban suka tashi gabadayansu suka yi sallama da malaminsu.
Hankakin Mal Musa a tashe yace
"Baba wata matsalar ka sake samu a wurin aiki ne?"Qasim ya girgiza kai. A lokacin Jamila ta fito zata je makota inda Inna ta aiketa. Ganin yayanta yana hawaye yasa ta koma ta sanar da Innar abinda ta gani. Kokarin tashi tayi da kafarta daya da tasha dori sakamakon karayar da ta samu a kafar bayan ta zame a bandaki. Kafadar Jamila ta dafa ta kaita soron. Suna shiga suke jin Qasim yana sanar da mahaifinsa mummunan labarin da ya dawo dashi gida.
Inna ta saki kuka hade da salati "Abubakar din da na sani ko dai wani kake nufi Baba".
Ido fal hawaye ya fada musu abinda ya sani dangane da rasuwar amininsa. Inna da Jamila sai kuka. Ba tun yau Abubakar yake dan gida a wurinsu ba. Yadda Qasim ke zuwa Kano hutu haka Abubakar yake zuwa Shanono. Lokacin da Mal Musa ya sami mutuwar barin jiki ba karamar hidima iyalin Kwamishina Adamu suka yi musu ba. Lalurar iyayensa da canjin aiki da ya samu yasa basu je wurin bikin ba. A can Kano kuma tashin hankalin cikin Asmau yasa basu tuna da sanar musu ba.
Bayan sun gama koke-kokensu suka shirya duk da yamma tayi Qasim yasa kujerar guragun da ake tura mahaifinsa a ciki a bayan mota sannan suka kama hanyar Kano. Ana gab da magariba suka isa kofar gidan Kwamishina. Maigadi ya sanar dasu cewa gabadaya 'yan gidan suna makota wato gidansu Asmau. Gaba Qasim yayi da motarsa suka karasa can gidan. Ya taimakawa mahaifinsa ya fito jingine da jikinsa suka shiga gidan.
Jigum suka tarar da Umma da Mama Yalwa kamar basu sami sabani sakamakon jin batun cikin ba. Baba Kwamishina yana gefe shi da Abdulhalim suna ta bige bigen waya. Kowa ka gani da abinda yake yi. Sallamar Qasim ta sa hankalinsu ya koma ga kofa. Kuka sosai ya zowa Mama saboda ganin Qasim. Shima bayan ya zaunar da mahaifinsa gabanta ya koma yana kukan.
Mutuwar Abubakar ta dawo musu sabuwa. Da suka dan nutsu ne Qasim yace " Umma ina Asmau ne?"
Kamar yace a fara wani kukan suka sake dasa sabo. A gigice yace " ba dai itama ta rasu ba?"
Jafar ne ya bashi amsa da cewar ba'a ganta ba tun safe. Qasim ya share kwalla "amma me yasa Asmau bazata yi tawakkali ba. Ina ta tafi haka?"
Boye- boye bashi da amfani shiyasa Shema'u ta sanar dasu abinda ya faru. Idan ma basu fada ba a waje wasu zasu fada musu.
Labarin yayi matukar razana Qasim da iyayensa. Lallai iyalan biyu suna cikin tashin hankali. Jikinsa duk babu kuzari ya dubi wurin da Malam da Baba suke zaune "ko da ba a gabana akayi ba, ni shaida ne cikin Asmau na Abubakar ne."
Mama ta dago jajayen idanunta tana kallonsa " Qasim abokinka fa ya rasu, yanzu ka kyauta kenan kana binsa da wannan mummunar shaida".
"Mama na san inda yaje nima a ko wane lokaci zan iya tafiya. Fadin gaskiya shine adalcin da zanyi masa." Daga nan ya basu labarin abinda ya sani dangane da Abubakar da Asmau wanda babu wani mutum da ya sani. Shi kadai ne yasan wannan sirrin.
Falon ya sake rudewa da kyar Baba da Malam suka samu aka yi shiru sannan suka ce a tashi ayi sallar magriba zasu karasa maganar idan sun dawo daga masallaci.
*****
Tun kafin azahar mota ta sauke su Asmau a tasha. Kowa na ciki ya dauki kayansa yayi gaba, ban ita. Sai yanzu take tunanin inda zata je kuma bayan nan. Bata taba zuwa Azare ba kuma bata san kowa ba. Wurin da taga an kebe domin sallah taje tayi sallah sannan ta karasa wurin masu abinci ta sayi wake da shinkafa da pure water. Yunwa take ji sosai. A gefen wurin sallar ta zauna taci abincin. Da akayi la'asar ta sake yin sallah ta kuma samun wuri ta zauna. A nan dai magariba da isha suka riske ta tayi sallolinta cikin fargaba. Ga dare yana yi gashi bata da wurin zuwa.Bayan tayi Isha ne hankalinta ya kai kan akwatinta. Dama jakar na kafadarta. Akwati dai babu shi babu dalilinsa wani ko wata ya dauke batare da ta sani ba. Bakin cikinta ya karu ta soma kuka. Ita ga tsoro bare tayi cigiya. Tana kallon yadda mata ke fada a cikin tashar da maza amma bazata iya ba. Tayi sa'a ma akwatin babu kudi a ciki.
Tana wannan kukan ne taji muryar wani daga gefenta yace
"Gani nazo sai kizo mu tafi.""Mu tafi ina?" Ta fada a tsorace ga wurin babu wadatar haske.
Wata dariya mutumin yayi. Babba ne don a kalla zai shekara hamsin. Yasa riga da wando na yadi ga taba a hannunsa. Bakinsa kuwa hakoran Makkah ne har biyu daga sama. Tsoro ne ya sake shigarta ta dan matsa baya.
"Kinga ki kwantar da hankalinki yarinya kinzo gida. Irinku sunfi a kirga da nake taimakawa a tashoshin garin nan." Ya dan zuki tabar sannan ya sake kallonta. " ki taho mu tafi idan ba a tashar nan kike son kwana ba 'yan iskan gari su danneki anjima kadan.."
Asmau ta manne jikin bango zuciyarta na dukan uku-uku
"Don Allah ni dai ka kyale ni."Mutumin ya girgiza kai alamun ya saba jin irin haka.
"Kinga 'yata ta kaina. Ni dinnan da kike gani ba cutar dake zanyi ba. Billahillazi masauki zan kaiki."Cikin tsiwa tace "bazani ba"
Ya dan tabe baki "kinyiwa kanki, irinku- irinku yawa garesu. Ku fito daga gidan iyayenku duk garin da kuka ga mota zata kuje. Sai kun sauka a tasha kuke gane kunyi kuskuren barin gida. Irina kuma sai mu nuna muku cewa ku kadai zaku iya rayuwa batare da iyaye ba. Akwai gida na mata zalla dama can nayi niyar kaiki saboda kwanan tasha ga zukekiyar mace irinki ba karamin hatsari bane."
Maganganunsa kara tsorata Asmau suke yi sai dai haka kawai bazata bi mutumin da bata sani ba. Dauke kanta tayi ya gaji da tsayuwa ya juya abinsa bayan ya bulbuleta da hayakin taba.
Ajiyar zuciya ta saki bayan ya tafi sai dai kafin ta motsa daga wurin da take taji wasu maza na tahowa wurin da take. Tana jin su suna tattaunawa a tsakaninsu waye zai fara amfani da ita. Abin nasu kamar fada mutum biyu suka dage harda zage-zage. Kafin su karaso da sauri Asmau tabi bayan mutumin da ya gama yi mata magana dama baiyi nisa ba. Tana kankame da jakarta tace ya tsaya zata bishi.
Wani shu'umin murmushi yayi yana kare mata kallo. Shiyasa yake son aiki da su Shoki yaran da ya biya suka tsorata ta.
Addu'a kawai take yi tabi bayansa suka mike wata hanya da tayi kudu da tashar.
*****
Su Umma sun sake taruwa a falon gidanta inda Malam Musa ya bada shawarar a dage da addu'a da binciken mutanen da take da alaka dasu. A cewarsa babu wani abu yanzu mai mahimmanci a gabansu sama da sanin inda Asmau take. Sannan ya ce
" a gaskiya dukkanku kunyi kuskure akan yadda ku ka karbi al'amarin yarinyar nan. Dukkan dan Adam ajizi ne, Allah da Ya haliccemu mai gafara ne da jinkai. Idan mutum ya aikata ba daidai ba musamman abu irin nata dolene mu nuna mata kuskurenta sannan kuma mu jata a jiki don gudun sake faruwar makamancinsa. Mu nuna mata mahimmancin tuba da karbar kaddara. Amma idan muka watsar da lamarin 'ya'yanmu saboda sunyi laifi hakika muna tura su ne ga aikata wanda yafi shi. Wani lokacin idan hantara da kyama tayi yawa sai kawai yaro ya fandare gabadaya yace bari yayi ta laifin tunda bashi da sauran gata.Mu kula sosai idan mutum yayi laifi fada, nasiha da jankunne yakamata muyi ba sharesu ba har su bi hanya mara kyau. Allah ma muna masa laifi Ya yafe mana duk girmansa indai ba shirka bane balle mu 'yan Adam. Wani abin yana faruwa ne domin ya zama izina ga sauran mutane.
Kuma na tabbatar yadda kuka nemi tilasta ta akan a cire cikin shi ya koreta. Sannan ta fiku gaskiya domin cire ciki ba tare da wata lalura ba bashi da muhalli a addininmu. Allah Ya tsare mana ita a duk inda take."
Jikin kowa kuma sai yayi sanyi da jin bayanin Mal Musa suka ce Amin.
Haj Bara'atu dai babu abinda ke damunta sai irin yadda ta rinka fadar maganganu marasa dadi ga 'yarta cikin bacin rai. Da ta sani bincikar ta tayi taji yadda al'amarin ya faru domin a kiyaye faruwarsa ga sauran yara.
Bacin rai da fushi dole ne amma yin komai cikin hikima da ilimi shine daidai. Da ta sani fada tayi mata wanda ta tabbatar halin da take ciki ma ya isheta abin kunya. Daga nan sai a kiyayi gaba,yanzu kuwa tana iya zuwa inda rayuwarta zata iya gurbacewa gabadaya.