48

4.8K 368 0
                                    

ABINDA AKE GUDU🙆🏽48

Batul Mamman💖



Ta kagu sosai taji abinda zai fada shi kuma nauyin maganar yake ji. Idan ya fada shikenan yayi musu katanga daga wannan lokacin. Ganin babu amfani yayi ta jan abin yasa yace
"Banda sunan sunan matata ta fari baki san komai game da ita ba ko"?

Asmau ta dan turo baki kishi na cinta duk da bata san matar ba.
"Ni sunan nata ma na manta. Kawai kazo bayan sama da sati daya ka fara min da hirarta"

Yadda take hade rai ya bashi dariya. Ya gyada kai  "kishi gareki haka, mun dade da rabuwa fa har ma tayi aure".

"To ai kaine sai ka rasa hirar da zaka yi sai tata"

Ya gyara zama tare da harde kafafunsa "saboda abinda zan fada miki yana da alaka da ita. Ina so ki saurareni da kyau ki fahimci abinda zan fada miki."

Hankalin Asmau ya fara tashi. Wani abu ne ya darsu a zuciyarta ta soma hawaye babu shiri tace cikin murya mai nuna rauni  "ba ma sai kace komai ba na gane abinda kake son fada. Aurenta ya mutu zaka mayar da ita ko. Babu komai zan iya zama da kishiya. Don Allah Ka kwatanta adalci a tsakaninmu" ta kare tana jan hanci.

Col. Ishaq bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Ita kuwa Asmau tayi kicin kicin da fuska. Hankici ya dauko daga aljihun wandonsa ya bata "kinci sunanki Idon kuka. Daga fara magana ji yadda fuskarki ta kumbura. Ai dai kya bari na fadi abinda ya kawoni kafin ki soma zubar da hawaye. Mata na gidan mijinta zaki kashe mata aure da baki"

Dan sanyi taji a ranta kila ba abinda zai fada ba kenan. Har tayi  murmushi sai kuma wani tunanin yazo mata "maganar aurenmu ne?"

Ya daga kai yana kallonta. Tausayinta yake ji sosai a ransa.

Murmushi tayi mai ciwo "Hajiya bata amince ka aureni ba ko? Dama nayi tunanin haka zata faru. Ba kowace uwa bace zata iya daure zuciyarta ta bari danta ya auri mace irina. Ko nice kila nayi sama da haka ma. Abinda kayi mana na kyautatawa Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai wallahi. Ko a haka  ma nagodewa Allah da Ya hadani da kai har ka nuna min so ka zama cikin masu nuna min na kara hakuri da kaddarar rayuwa"

Hawaye ke zubo mata tana magana bata ko tunanin tare shi. Dago kansa yayi daga cikin kujerar ya dan matso gaba.
"Ya Salaam, Matar Jikamshi haka kike? Lokaci daya duk kin rikita kanki. Kada ki dauki alhakin Hajiyata wallahi ta amince da aurenmu"

Jikinta duk da haka a sanyaye yake tace "sauran 'yan uwanka ne basu amince ba?"

"A duniyar nan Hajiya ce kadai zata hanani aurenki na hanu. Banda ita babu wanda ya isa. Yara kanana akeyiwa haka ba ni ba. Kamata kowa yasan ina da hankalin da zan san abinda ya dace da rayuwata. Ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada. Kamar yadda na fara magana kafin ki katseni da dan bakin nan naki mai bani shaawa..." ya fada yana kashe mata ido.

Kunya taji sosai harda rufe fuska da hannuwanta. Yayi murmushi ya cigaba da magana "na taba aure, shekarunmu shadaya da Badar babu haihuwa. Munje asibitoci da dama ana cewa bamu da matsala. Har maganin gargajiya mun sha. Daga karshe mahaifiyarta tasa na saketa kuma cikin ikon Allah a shekarar da tayi aure ta haihu"

Asmau ta dan girgiza kanta "Allah sarki, dama haihuwa ta Allah ce. Wani baya haihuwar dan wani"

Kallonta yake da mamaki kamar bata fuskanci inda ya dosa ba
"haihuwar Badar ya tabbatar min da inda matsalar take. *Matar Jikamshi, bana haihuwa*. Saboda haka kiyi hakuri da na bata miki lokaci amma na _janye maganar aure a tsakaninmu_."

Tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi haka taji saukar maganarsa ta karshe. Shiru tayi na dan lokaci yana ta kallonta yana jiran ta fara kuka sai yaga idanunta ko alamar hawaye babu banda wanda ta zubar dazu. Shirunta tsorata shi yayi yace "kice wani abu mana."

ABINDA AKE GUDU (Completed)Where stories live. Discover now