ABINDA AKE GUDU🙆🏽13
Batul Mamman💖
Tare suka koma gidan Kwamishina sai dai su Mama har sun wuce asibiti. Sai wuraren shadayan dare Mama ta kira Umma bayan taga missed calls dinta take sanar da ita an kwantar dasu asthma din Abubakar ce ta tashi.
Gari na wayewa Shemau ta hada abincin safe harda mutanen asibiti. Ita da Umma suka tafi asibitin su Asmau kuma suka wuce makaranta. Sai bayan la'asar da zasu kai abincin dare duk da ana kaiwa daga nasu gidan Umma ta hada 'ya'yanta gabadaya suka tafi asibitin.
Jikin Asmau a sanyaye suka shiga dakin saboda ba karamin rudewa tayi ba da ganin halin da Abubakar ya shiga. Bayan an gaisa kowa yayi masa sannu ya amsa banda na Asmau. Da farko ta zata baiji ba ta sake maimaitawa. Wannan karon harararta yayi amma ita kadai ta kula da hakan. Bata gane dalilinsa na yin hakan ba amma bata ji dadi ba har suka tafi bata sake magana ba.
Sai da yamma aka sallame shi washegari. Nan ma da suka zo karatu yana falo ta sake yi masa sannu yaki amsawa har sai da Qasim yayi masa magana.
"Abubakar ana yi maka sannu baka ji ba"Hamma yayi ya gyara kwanciya batare da ya amsawa Qasim ba.
Da dan murmushi Qasim yace "jikin nasa da sauki . Ke ce Asmau ko?"
Kanta a kasa saboda abinda Abubakar yayi mata tace "eh" tare da mikewa ta tafi masallaci.
An shafe sama da wata biyu Abubakar baya amsa gaisuwar Asmau. Dama can ba wata hira suke yi ba. Abin yana matukar damunta sai dai ta kasa fadawa kowa.
Ranar lahadi da yamma tana dakinsu Yassar ya shigo ya ganta tasa littafi a gaba tana kuka. Baice mata komai ba ya fita ya fadawa Umma. Tasowa tayi ta shigo dakin da kanta.
"Me ya sami Idon kukana kike sana'ar a daki ke kadai"
Littafinta ta mikowa Umma na Physics. Assignment ne kuma duk lissafi ko daya bata yi ba.
"Tun dazu nake yi na kasa amsa ko daya. Kuma malamin duka yake yi.""To shine kike kuka kuma saboda kinfi kowa ruwan ido, uhmm? Kinga ni da yayyenki babu wanda yayi physics. Idan kuma kin amince na koya miki gobe kici kafi-zero shikenan" ta fada da dariyarta.
Murmushi Asmau tayi tana sake duban littafin.
Umma tace "kije Abubakar ya koya miki shine dan science a gidan Mama."
"Umma ai gara naci zero din. Ni da ko gaisuwata baya amsawa idan naje nasan bazai kulani ba"
"Asmau bana son karya. Baban nawa ne baya amsa gaisuwarki? Jiya da yazo ba ke nasa kika dafa masa indomie ba. Ko dai wani laifin kika yi masa?"
"Kila kunyarki yaji amma da gaske tun kwanciyarsa a asibiti ya tsaneni. Kuma ni banyi masa komai ba".
Umma ta dan kalli Asmau sannan ta fita. Abubakar yaron kirki ne kila Asmau tayi masa laifi ne ko kuma dai wani rashin fahimta suka samu. Ko ma dai meye bazata bari yayi nisan da zai shiga tsakaninsu iyaye ba. Wayarta ta dauka ta kirashi. Tayi sa'a yana gida tace yazo tana son ganinsa.
*****
Dakin Mama yaje ya fada mata Umma na kiransa. Plate din da take shan kankana ta ture ta tashi.
"Jirani muje tare jiya naji Aina'u tana ta tari. Tun dazu nake tunanin zuwa duba ta."Tare suka tafi suna 'yar hira a hanya. Umma taji dadin ganinsu su biyun. Sun dan taba hira ta kwalawa Asmau kira.
Tana fitowa da taga Abubakar sai da gabanta ya fadi...ba dai Umma kiransa tayi akan abinda ta fada ba?
A kasa ta zauna ta gaishe su. Umma ta lura tabbas bai amsa ba. Kuma bai dade da gama tsokanar Aina'u ba.
Idon Umma akan Asmau tace "dazu da nace kije Abubakar ya koya miki assignment me kika ce min"?
Cikinta har wani kullewa yayi ta daga kai suka hada ido ya harareta. Da sauri ta sauke kanta
"Uhmm, uhmm, babu komai".Mama ta kallesu duk su biyun. Asmau a tsorace, Abubakar ya hade fuska.
"Ni kun batar dani Umma, me ya faru?"Umma ta sanar da ita abinda Asmau ta fada da kuma wanda ta kula dashi a wurin. Duk su biyun Abubakar suka zubawa ido suna jiran amsarsa.
Dariya suka bashi ya mike tsaye " ni bata yi min komai ba. Bari na koma gida dama aiki nake yi."
Mama ta daure fuska "kaga abokan wasanka a nan ne, zauna ka fadi me ya hadaka da kanwarka. Ni bazan lamunce da gaba cikin 'ya'yana ba. Ku da su Asmau duk matsayinku daya a wurinmu."
Ita dai Asmau sai satar kallonsa take yi a tsorace.
"Mama kin tuna ranar da na sami attack har na kwanta a asibiti? Yarinyar nan fa tana cikin masallacin. Na kasa dauko inhaler a cikin aljihun wandona saboda yadda nake ji nayi ta nuna mata kuma ta gane wai sai ta fita kiranki. Da baki zo da wuri ba shikenan fa".
Umma da Mama sai dariya shi kuwa da gaske yaji haushi ya dubi Asmau itama shi take kallo.
"Da na mutu a lokacin idan ba fatalwa zan rinka yi miki ba."Wannan karon itama sai da tayi murmushi ganin ya dan saki fuska.
Mama ta janyota jikinta "Me yasa baki bashi inhaler din ba Asmau?"
Idonta ne ya cicciko da hawaye. Umma tace " oh ni Bara'atu yarinyar nan ko baure bazai nuna mata zuba ba. Ke baki da aiki sai na kuka daga tambayar fatar baki."
Mama ce ta lallaba Asmau muryarta na rawa ta kalli Umma.
"Ba cewa kika yi haramun bane mace ta taba namjin da ba muharraminta ba. Har a islamiyya duk ana fada mana. Da na taba shi nasan fada zaki yi min sannan a rubuta min zunubi shiyasa na kira Mama".A take Abubakar yaji wani irin yanayi game da Asmau. Shi kan shi yasan bai dace ace yana fushi da ita ba amma abinda ta fada yasa yaji ta sami wani matsayi a wurinsa. Ashe abinda tayi, tayi shi ne don bin umarnin addininta. A yadda yake matashi mai tsantseni wurin addini yana son mutane masu kiyayewa.
Yanayin kallon da yake mata ya canza zuwa sakin fuska "dauko littafin muje na koya miki kinji kanwata Idon kuka."
Sai da suka dara gabadaya sannan Umma tace "Asmau addinin musulunci yayi mana iyakokin da musulmin kwarai bai dace ya tsallakesu ba. To amma akwai sassauci akan abinda ya zama lalura. Kinga a lokacin da ya sami attack bashi da wani mataimaki sai ke kadai a wurin. Rashin taimakonsa kuskurene tunda yana cikin mawuyacin hali. Da ace akwai wani namijin to dama bai kamata ki taba shi ba. Komai na addininmu yana da sauki. Duk abinda ya zama lalura wajibi ka taimaki mutum koda kuwa baki sanshi ba. Ku tashi Allah Yayi muku albarka".
Shi Abubakar har kunya yaji. Yarinya ta fishi hangen nesa. Can gefe suka koma a cikin falon wurin wasu kananan kujeru da dan tebur a tsakaninsu. Littafin ya karba yace ta dauko text book dinta na P.N Okeke
Mama ce ta bisu da kallo har suka zauna sannan ta maida hankalinta ga Umma.
"A gaskiya Umma ina yaba miki wurin kokari a tarbiyantar da yaran nan. A zamanin nan da kananan yara sun san meye mace ko namiji amma har a irin wannan yanayin Asmau bata manta da hudubarki ba. Allah Ya kara taimaka mana wurin basu tarbiya. Shiyasa nake jinki kamar kanwata ta jini wallahi."Murmushi kawai Umma tayi.
Mama ta cigaba da magana " inama dai yaran nan su hada kansu? Wallahi ba karamin dadi zanji ba. Ji nayi Asmau ta kara shiga raina. Ni daga yau ma ta kwace matsayin auta Umar."
Wannan karon dariya Umma tayi.
"Anya wannan dan shagwabar zai yarda? Maganarki kuma akan ita da Abubakar ba tun yau ba nima nake sha'awar hakan. Allah Ya zaba mana abinda yafi alkhairi."A can gefe inda suke yin aikin kuwa ko yaya suka hada ido sai su sakarwa juna murmushi.
Wannan murmushin sai da ya zame musu jiki. Ko karatun dare suka zo sai Abubakar yayi ta kallon Asmau har sai sun hada ido anyi murmushin nan. Ita yanzu kunyarsa take ji sosai. Shi kuma duk irin basarwar nan tasa da rashin kula mutane indai suka taru suna hira ko a gidan Mama ko gidan Umma to sai yasan yadda yayi Asmau tasa baki.