ABINDA AKE GUDU🙆🏽40
Batul Mamman💖
Washegari su Asmau basu sami zaman gida ba. Sun hadu da Shemau, Sabira da su Nasiba an sake gyara gidan Ainau kamar masu shirin kai amarya. Da yamma Umar yaje ya daukota. Kana ganinsa kasan yau yana cikin farinciki. Kusan wata uku bata gida don tun kafin ta haihu aka bata bedrest shine Mama tace ya kaita gida zata fi hutawa.
Ranar Jikamshi ya kirata yafi sau shida kuma sai anyi hira akalla ta rabin awa. Yana kira sai ya tambayeta ko Qasim ya kira kuma wayar minti nawa suka yi. Sai da ta gama dariya sannan ta zolaye shi tace
"baya ajiye waya sai wata wayar ta shigo min."
Shima dariyar yayi mata kawai yace "ba zan damu ba don nasan tawa hirar ce kawai take burgeki koda kuwa ta minti daya ce. Amma zancen gaskiya ki dena kashe masa murya yadda kike yi min. Kara sonki kawai zaiyi ni kuma ba hakura zanyi na bar masa ba"Tayi dariya sosai hakan ya sanya shi nishadi.
"Haba Yaya Ishaq, kai fa Yayana ne kuma Yayan Qasim. Kaci girma kawai"
Kamar tana gabanshi ya dan daure fuska cikin wasa "ki kiyaye ni fa matar Jikamshi. Ni ba yayanki bane na fada miki. Kina magana da baban Safina mijin Asmau in Sha Allah"
Ta danyi shiru tana jin inama hakan ya tabbata.
"Baki ce amin ba"
"Amin" ta amsa ba don yana tunanin ganin ranar aurensu a gaba ba. Addua zata yi masa Allah Ya bashi mace ta gari. Amma tasan bazata je komai ba a bikin.
Daga haka suka yi sallama kowannensu yana kara jin son dan uwansa.
*****Bayan sati daya kullum Col. Ishaq da Qasim sai sun kirata a waya kowanne yana kara jaddada mata irin son da yake mata. A wannan kwanakin da Jikamshi bai zo ba ita kanta abin ba karamin damunta yayi ba. Har mamaki take yi da take masa so irin wannan duk da tana kokarin dannewa. Ranar alhamis ta kira Zubaida ta sanar da ita zata zo yini washegari. Zubaida sai murna don tun dawowarta sau daya ta samu taje gidan, basu zauna sunyi hira yadda suke so ba. Ita kuma Zubaida saboda cikinta ya tsufa babu batun fita.
Kafin shabiyun rana washegarin Asmau ta gama girkin rana tayiwa Amatullah wanka sannan itama ta shiga. Tana fitowa taga Umma ta dawo duk da ranar aiki ne. Har daki ta bita tana tambayar ko lafiya.
"Babu komai yau dai na gaji ne. Kinsan kwana biyu bamu huta ba. Kema da kin hakura da zuwa gidan Zubaidan sai wani satin. Yarinyar nan kina ta yawo da ita 'yan kwanakin nan"
"Umma Yaya Jafar yace zai kaini ba adaidaita zan hau ba."
"To kiyi maza ki karasa shiri kinsan baya son jira."
Asmau ta tashi ta koma daki ta karasa shiryawa sannan ta zauna jiran Jafar. Ko rabin awa ba ayi ba ya iso. Suna shirin fita taga Kawu Garzali shima ya shigo. Gaisawa suka yi yace mata Zubaida tun asuba take jiranta. Yanzu Kawun nasu kamar wani kaka haka yake musu wasa. Shima dai tayi mamakin ganinsa don ance mata Umma ce ta sama masa aiki a inda take wato MTN office.
*****Suna fita Umma tayi ajiyar zuciya ta tafi dakin Hajjo ta sanar da ita wayar da suka yi da Mama tun tana wurin aiki. Shine ma dalilin dawowarta gida da wuri da zuwan Kawu Garzali. Alh Adamu ne yake son ganinsu don yace gidan zai zo idan ta taso aiki. Kasa hakura tayi saboda Mama tace mata batun auren Asmau da Qasim ne zai kawo shi. Shiyasa ta fada Garzalin suka dawo gida kawai. A cikin satin da tayi magana da Asmau akan manemanta biyun ta nuna mata ita karatu kawai zatayi duk zata sallamesu batare da bacin rai ba. Sai dai kuma tuni Umma ta gano inda zuciyar 'yarta tafi karkata. Matsalar dai bai wuce abinda itama Asmau take jiyewa tsoro ba na dangane da gori ko rashin amincewa daga dangin mazan.
Bayan ta gama bayaninta Hajjo tace "yaron nan da gaske yake da rike amanar amininsa. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Ta danyi shiru kamar mai tunani sannan tace
"Amma idan banyi kuskuren fahimta ba sai naga Ishaq shima kamar fa sonta yake yi. Kinsan mu idonmu idon soyayya. Muna ganinta muke ganewa"Umma tayi dariya sannan ta fada mata wayarsu da Anti Bintu da kuma yadda suka yi da Asmau
"Bazamu zuba mata ido ba duk da muna jin tsoron surutun mutane auren shine rufin asirinmu. Duka su biyun ni bana kin kowa amma Hajjo kinga Qasim muka fi sani kuma gashi har maganarsa ta kai kunnen manya. Garzali ma ya shigo ina tsammanin a falo ya tsaya. Shine namiji dole ayi komai dashi ""Kinga wancan mutumin banzan shi ya kamata ace zaiyi komai akan lamarin yaran nan amma kafin a ganshi ma aiki ne"
Umma ta fahimci da Kawu Rabe take. Murmushi kawai tayi "kada ki damu Hajjo, Garzalin ma ai babanta ne kuma na fadawa su Yaya Abu don su san me ake ciki. Saura kuma sai yazo munji"
Kawu Garzali sallama zai shigo dakin yaji Hajjo tace "Kinsan Allah Bara'atu kada ku yarda kuce kun amince ba tare da munji ta bakin Asmau ba, bazan yarda kuyi mata auren dole ba. Idan bata so ya hakura kawai"
Umma tace "Hajjo mu har mun isa muce bama so? Kada ki manta duk abinda ya faru da Asmau. Yanzu duk wanda yazo neman aurenta ai alfarma yayi mana"
Hajjo ta danyi shiru tana tausayawa jikarta "kuma fa haka ne. Allah Ya rabamu da mummunar kaddara"
Tashi Umma tayi "dama yanzun ma ina jin shawara ce dai yake son bamu a matsayinsa na uba gareta."
Kawu Garzali ya gaishe da Hajjo sannan tace su fito falo Alh Adamu yazo.
*****Sun zazzauna an gaisa da Alh Adamu da Mama Yalwa da bata dade da shigowa ba itama.
Yayi dan gyaran murya wanda ya janyo suka fuskance shi "Nasan Yalwa ta fara sanar dake dalilin zuwan nan. Mal Musa ya kirani a waya ya sanar dani yadda suka yi da Qasim akan auren Asmau. To shi a son ransa nan da lahadi su zo ayi magana ta iyaye a tsayar da lokaci. Shine ya bukaci lallai in fara sanar daku domin ayi shawara"
Hajjo ce ta soma magana "hakika Alhaji kai uba ne ga dukkan 'ya'yan Bara'atu. Ka rikesu tsakani da Allah tun lokacin da mu da suke dolenmu muka wofantar dasu. Duk shawarar da ka yanke akan yarinyar nan muna da tabbacin bazata cutar da ita."
"Duk da haka Hajjo me kuka gani? A basu dama su zo ko akwai wani tanadi da kuka yi mata".
Kawu Garzali yayi saurin cewa "haba haba Alhaji akwai wani tanadi ne da ya wuce aure. Amma Haj Bara'atu me kika gani?"
Idanu suka koma kan Umma. Daga yadda Alh Adamu yake magana ta tabbatar yana so su amince tunda har ya zo gidan da da kansa. Mutumin nan yayi musu gata fiye da tunanin mutane. Ta dauke shi tamkar dan uwanta bazata iya bijere masa ba balle kuma Asmau.
"Nima dai bani da zabi sai abinda kuka yanke. Wannan aure idan ya yiwu ba karamin dago mata martaba zaiyi ba a idon jama'a sai dai muyi fatan alkhairi. Shi kuma Abubakar Allah Ya gafarta masa" ta kare da guntun hawaye. Da yana raye duk wannan abin bazai taso ba.Mama ma sai ta soma kuka duk kuma zukatansu suka raunana. Alh Adamu yace "zaku fara ko?"
Da yaga sun nutsu ya ce "tsakani da Allah ni naso nasa Abdulhalim ya nemi aurenta domin kare martabarmu gabadaya. Sai na bari ta dan kara kwana biyu ashe rabon Qasim ce. Zan sanar dashi su zo jibin. Idan yaso sai mu kira dangi na kusa azo ayi komai da wuri. Iyalin Mal Musa sunyi mana abinda bazamu manta ba tunda suka bari dansu ya nemi auren tamu 'yar."
Sunyi ta tattaunawa akan maganar karshe mazan suka yi shirin zuwa masallaci. Aka bar su Mama suna kara shawara akan kamar yaushe ya kamata asa auren idan dangin Qasin sun nemi asa rana da wuri.