ABINDA AKE GUDU🙆🏽17
Batul Mamman💖
Kafin ya fito ya kira Asmau a waya ya sanar da ita zai zo. Jikinta a sanyaye ta amsa masa don ita yanzu kunyar ganinsa take yi. Ko ba'a fada ba daga nasihar Anti Bintu tasan cewa duk abinda ya faru laifinta ne.
Har daki taje ta sanar da Anti Bintun zai zo kamar yadda ta saba.
"Ki dora abinci dashi amma ki bar dan waken sai gobe don bazan bawa suriki dan wake ba"Ita da Asmau duk dariya sukayi sannan ta wuce ta dora shinkafa da miya.
Wuraren karfe uku ya iso Anti Bintu tazo suka gaisa sannan ta basu wuri.
Yau Asmau hijab ta saka dogo har kasa fuskarta babu kwalliya sai hoda da kwalli. Jikinta duk babu kwari tayi nadama sosai. Abubakar kuwa tamkar ya hadiyeta da kallo. Anyi sa'a yaran gidan suna ta gilmawa a falon. Da laasar suka tafi islamiyya shi kuma yaje yayi sallah.
Ana idarwa ya dawo ya kalli Asmau dake zaune a can gefe.
"Asmy dawo nan kusa dani nafi jindadi". Ya nuna kujerar gefensa.Tashi tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tana zama ya kama hannunta ya rike yana lumshe idanu. Can kasa take jin muryarsa
"I love you so much Asmy. Ina ma anyi aurenmu kiga irin abinda nake nufi."A kwanakin baya har so take ya rike mata hannu amma yau sai taji ta tsani hakan. Tana son nuna masa kuskuren abinda tasan ya fita sani amma dole tabi lamarin a hankali kada yayi mata mummunar fahimta ko yace ta mayar dashi dan iska.
Har lokacin tafiyarsa yayi bata iya sakin jiki dashi ba. Shi kuwa gabadaya ya kasa samun nutsuwa. Bakin motarsa da ya ajiye a wajen gate ta raka shi ai kuwa yana bude motar ya rungumota jikinsa. Dama layin ba mutane sosai saboda unguwar bata gama cika ba ga duhun dare.
Wasu hawaye masu zafi Asmau taji sun taho mata ta hadiye. Dole ta sami lokaci suyi magana da Abubakar akan wannan abin. Rungumar da take jindadi daga gareshi yau bata so. Tana wannan tunanin taji yayi mata abinda bai taba yi ba. Abinda take ta mararin faruwarsa. Bakinsa ya hada da nata yayi mata rikon da bazata iya kwatar kanta ba koda tayi niyya.
Hawayen da take boyewa ne suka sakko ganin Abubakar tamkar baya cikin hayyacinsa. Abubuwan da yake mata sun fara wuce gona da iri. Ba shi ya saketa ba sai da don kansa yaji hankalinsa ya fara dawowa gareshi.
Ganin tana kuka ya soma bata hakuri.
"Asmy kiyi hakuri please. Na rasa dalilin da yasa nayi miki hakan. Ki sani ina sonki tsakani da Allah kuma in sha Allah bazan sake kwatanta miki haka ba sai munyi aure".Yadda yake maganar sai ya bawa mutum tausayi. Tabbas baya son abinda yake yi sai dai karfin sha'awarsa da tsananin rudin shaidan yasa ya kasa hakuri.
A hankali ta share idonta "Yaya Abubakar don Allah mu dena irin wannan abin kaga babu kyau."
"Na sami Asmy, ni kaina na rasa gane yadda akayi muka fada ga wannan masifar. Ki share idonki kinji matar Abubakar".
Kafin ya tafi sai gashi ta sake sosai hankalinta ya kwanta. Suka rabu zuciyar kowa tana nata sake saken.
*****
Abubuwan da suka gudana tsakanin Abubakar da Asmau su suka rinka yi masa yawo a kwakwalwa. Yayi tunanin zaiji saukin sha'awar dake damunsa sai abin yayi tsanani sosai. Kullum cikin mafarkinta yake yi. Baccin kirki ya gagare shi sai tunanin yadda zaiyi ko dai a matso da aurensu ko ya kashe yunwarsa ko sau daya ne.