ABINDA AKE GUDU🙆🏽9
Batul Mamman💖
Mal Yahaya dakansa ya rinka yiwa Hajjo fada amma ta takura Bara'atu. Lokacin Shua'aibu yaje gyaran gidan da zasu koma a Zaria. Yana dawowa ya tarar da mahaifinsa a kwance shine suka kaishi asibiti shi da Rabe. Likita ya duba shi aka ce malaria ke damunsa. Magunguna kawai aka rubuta suka dawo gida.
A tsakar gida Hajjo tayiwa mijinta shimfida suka kwantar dashi yana shan iska shi kuma Shu'aibu ya tafi siyan magani. Fitarsa keda wuya Rabe ya karasa kusa da Hajjo yace
"Hajjo likitan fa yace basu gane kan cutar dake damun Baba ba. Idan bakiyi wani abu ba duk sai mayun nan sun cinye mu."Hankalin Hajjo ya kara tashi. Rabe yaji dadin hakan. Bashi da burin da ya wuce asa dan uwansa ya saki Bara'atu shi kuma ya aura. Tun farkon haduwarsu yaji yana sonta. Duk wasu alamu ya nuna mata inda tayi masa tatas shine ya koma zuga Hajjo suna muzguna mata. A dalilin bata son hadashi da dan uwansa ne yasa bata tona masa asiri ba tunda dama babu mai kaunarta sai mijinta. Ko ta fada kila bazasu yarda ba.
A fusace Hajjo tace "Bara'atu fito nan muguwa mai mugun nufi".
Bara'atu tana kitchen ta fito da sauri ta durkusa. Lokacin bacci ya fara daukar Baba amma hayaniyar Hajjo tasa ya farka.
Sai da ta gama harararta sannan ta dubi Rabe "fita ka nemo min abokanka majiya karfi koda biyu ne"
Murmushin mugunta yayiwa Bara'atu sannan ya fita. Ba jimawa suka dawo su uku. Hajjo ta tashi ta nuna musu Bara'atu da Bintu "gasu nan, so nake ku sa su tsallake Malam sau bakwai ko na samu su saki kurwarsa. Bari naje na debo garwashi na kunna turaren mayu."
Bara'atu tayi matukar razana ta soma rokon Hajjo tayi hakuri. Ko kallonsu bata sake yi ba tayi gaba abinta tana masifa. Ganin haka yasa ta kama hannun Bintu zasu shiga daki su rufe Rabe ya fizgota. Suna ihu da kuka ya rike Bara'atu wani kato ya daga Bintu yana tsallaka Malam Yahaya da ita a kafadarsa.
Mal Yahaya jiki babu kwari ya kasa tashi sai daga kwance yake kokarin yi musu magana amma babu mai sauraronsa.
Bayan sun gama da Bintu suka ajiyeta sannan Rabe da dayan suka kama hannu da kafafun Bara'atu suna shillata ta saman Malam. Kuka dai tayi har muryarta ta dashe. A karo na biyar da shilla ta da suke yi Shu'aibu yayi sallama ya shigo.
Abinda da ya ga kaninsa yana yiwa matarsa yasa yaji wani mugun daci a wuya. Shi kanshi Rabe ba karamin tsorata yayi ba suka yar da Bara'atu yayi ciki inda Hajjo take tahowa da kasko fal garwashi.
Ko tunanin daga Bara'atu, Shu'aibu baiyi ba. Kan Rabe yayi da gudu ya damko shi. Dukansa yake kamar ba jininsa ba yana zaginsa. Hajjo tayi iya kokarinta amma bai sake shi ba sai da ya gaji don kansa ya koma ya daga matarsa yana haki.
Hajjo ta durkusa ta daga Rabe. Baki da hancinsa duk jini. Rai a bace tace " yanzu saboda wannan yarinyar kayiwa dan uwanka irin wannan dukan? Meye laifinsa don yana son ceto rayuwar mahaifinsa. Kuma ni na saka shi".
"Yanzu saboda Allah Hajjo ko Bara'atu ba matata bace abinda akayi mata yayi daidai kenan? Duk abinda akeyi ina dauke kai darajar Baba amma na rantse duk wanda ya sake shiga sabgar iyalina sai hukuma ce zata raba mu."
Da hannu Mal Yahaya yayi masa alama ya durkusa a gabansa. Hakuri baban nasu ya sake bashi da alkawarin idan yaji sauki zai dauki mataki.
Bayan kwana uku ciwonsa ya kara tsanani suka je wani asibitin aka ce typoid ce taci hanjinsa ma. Dama irin abinda ake gudu kenan. A kai mutum asibiti babu gwaji su hau dirka masa magani. Washegari Malam Yahaya ya cika. Iyalinsa sun sha kuka sosai. Bayan wata daya Shu'aibu ya hada nasa iyalin suka koma Zaria. Hajjo dai ta kullaci Bara'atu don ta yarda dari bisa dari su suka kama Malam.
Tunda suka koma Zaria suke samun budi. Bara'atu har kiba ta soma yi kuma ya samar mata gurbin karatu a ABU Zaria tana karanta Public Administration. Duk sati Shu'aibu yake zuwa Kano amma baya tafiya dasu. Da tayi magana yace babu amfani tunda ba kaunarta sukeyi ba. Itama Hajjon don neman magana ta tambayeshi yace hakan ya fiye musu kwanciyar hankali.
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah. Shekara bata zagayo ba Bara'atu ta haifi Shema'u. Danginsu na Wushishi sun zo sosai tunda mijinta yana bari taje ganin gida. Daga Kano ma su Yaya Abu sun zo sai dai ba'a rabu lafiya ba.
Bayan shekara daya da rabi ta haifi Jafar sannan Asmau. Shu'aibu yana kula dasu sosai. A lokacin Bintu ta gama secondary akayi bikinta.
Haka suke zamansu lafiya ga jari ya bawa Bara'atu tana sayar da kayan sawa na mata a cikin gida. Sai lokacin sallah kawai suke zuwa Kano ko idan wani abu ya faru. Basu da wata matsala a lokacin. Asmau nada shekara hudu aka haifi Yassar.
Wata rana da yamma Shu'aibu yana zaune a falo tare da iyalinsa Rabe ya zo. Shi da matarsa ne Laraba da yaransa biyu. Baraatu bata nuna wata damuwa ba tayi musu tarba mai kyau. Laraba mace ce mai mutumci shiyasa basu dauki lokaci ba suka saba a dan zuwan da suke yi Kano.
A can falo kuma Rabe yake sanar da yayansa yazo ne zasu dan kwana biyu shi da iyalinsa. Ko kadan Shu'aibu bai so hakan ba sai dai ya kyale yaga iya gudun ruwansa.
Shiru basu da niyar tafiya ita kanta Laraba har kunya take ji. A sati na uku Shu'aibu ya dawo daga makaranta zai shiga dakinsa yaji muryar Rabe yana rokon Bara'atu da ta amince masa wannan zuwan ma duk nata ne.
Daga murya tayi tana fada tace cikin kuka "idan baka fita ba sai nayi maka tonon asirin da bazaka kara mutumci ba a duniya. Matarka fa tana gidan nan. Ko don kaga tuntuni ina rufa maka asiri?"
Murya kasa kasa yace "ki amince Bara ko ba a gidan nan ba. Ni sau daya ma kawai ya isheni. Ki taimaka."
Ihu ta kurma a tsorace ganin yayo kanta Shu'aibu ya bude kofar ya shigo. Yau ma iya karfinsa yasa yana duka Rabe. Abu yayi tsanani har Laraba ta jiyo su ta fito. Korarsu yayi a yamman yace ya fice masa daga gida.
Laraba na fahimtar abinda ke faruwa ta tattara ko jiransa batayi ba ta kwashi yaranta suka tafi. Shu'aibu yayi kukan bakinciki sosai sannan yayi mata fadan rashin sanar dashi da wuri.
Washegari da safe yace mata zai je Kano ayi maganar a gaban Hajjo don yasan Rabe yanzu yanzu zai juya zance. Haka kuwa akayi Hajjo tace sai ya saki Bara'atu ko ta tsine masa. Jiya Rabe ya dawo gidan jina-jina saboda sharrin data kulla masa. Duk yadda Shu'aibu yayi Hajjo taki yarda. Laraba ma data bada shaida akan Rabe a take Hajjo tasa ya saketa.
A kan hanyarsa ta komawa ne Shu'aibu yayi hatsari. Bacin rai ne ke damunsa saboda Hajjo tace idan har bai saki Bara'atu ba sai dai ya sake wata uwar.