ABINDA AKE GUDU🙆🏽60
Batul Mamman💖
Annur ya soma murmushi haka ma Gaddafi sannan yace "Antinmu wallahi da farko ban tabbatar kece ba. Alhamdulillah, Allah Ya kaddara zamu sake haduwa"
Gaddafi yace "an kusa shekara bakwai fa idan ma ba'ayi ba"
Asmau sai murmushi take da ta sake haduwa da 'yan samarin da suka taimaka mata lokacin da take nakudar Amatullah. Bata jin zata taba manta kammaninsu duk da a wancan lokacin suna tare da kuruciya sosai bata tunanin zasu kai shekara sha takwas ma. Jikamshinta ta kalla zata yi masa bayaninsu yace "kina fadan sunansu na gane ko su waye" shima fuskarsa da fara'a. Duk wanda ya taba taimakon Matarsa yana ganinsa da kima da daraja. Sannan bashi da mantuwar sunaye indai a tarihin rayuwarta ne.
Hannu ya mika musu suka gaisa yace shine mijinta. Fuskokinsu sun nuna jindadin wannan labari sosai. Col. Ishaq yace "ku shiga kuyi siyayyarku sai muje ku ga gidanmu saboda a cigaba da zumunci."
"Ai kuma mun fasa zamu dawo wani lokacin." Annur ne yayi maganar yana kallon Amatullah da alamar tambaya amma dai yayi shiru. Tasu motar suka shiga suka bi bayansu Asmau.
Col. Ishaq na tuki ta riko hannunsa daya tana murmushi.
"Nagode da ka gayyato su gida. Bani da abinda zan saka musu dashi da irin taimakon da suka yi min amma yadda ka karrama su kadai yasa naji dadi sosai."Yayi mata murmushi "Matar Jikamshi, kin hadu da mutane da dama a rayuwarki wanda banda tsohuwar nan ta Azare kowanne cikinsu ya taka wata muhimmiyar rawa wurin nesanta rayuwarki daga lalacewa. Duk wanda ya taimakeki ni ya taimakawa dole na kyautata musu nima"
Tsohuwar da ya fada ta gane da Uwargida yake tayi 'yar dariya "Uwargida fa ta shiryu Jikamshina"
"Wani suna naji ta kiraki dashi shine raina ya baci."
Bata rai yayi sosai Asmau ta rinka dariya. Itama ta tsani wannan sunan wai 'Yar Dabas. Tuna mata yake da zamanta a gidan da irin bakar wuyar da ta sha. Tana dariya yana kallon bakinta ya dan sassauta murya "I miss you"
"Gani a kusa da kai fa"
"Ba ke ba wadannan lips din nake nufi"
Ta danyi fari da ido yace "nagode Allah da Ya bani ke Matar Jikamshi. Komai naki ina so, har da wannan fari da idon"
Kamar wadda aka jeho sai jin muryar Amatullah sukayi a tsakaninsu tana daga bayan mota tace "Babana inyi maka fayi da ido nima na iya"
Shiru suka yi duk su biyun. Saboda tana ta aikin gwada sabon takalminta sun manta tana motar ma. Ta sake maimaita tambayar yace "Princess ba kyau ayi fari da ido"
Ta turo baki "Amma kacewa Ummi kana so tayi"
Tohhh yarinya zata kure babanta. Asmau kyalesu tayi don tasan halin Amatullah yanzu ta rinka jan zancen da wata sabuwar tambayar kenan.
Sake tunani yayi sannan yace mata "baki ji abinda na fada bane sosai, cewa nayi akwai abu a saman idonta ina so tayi fari da idon sai ya fadi"
Amatullah ta koma ta zauna tana cewa "auuu ashe banji ba. Amma dai na iya fayin inyi maka?"
Rike dariyarsa yayi yace mata ta bari su je gida yanzu tuki yake yi. Shi da Asmau suka hada ido suka yi murmushi. Dole ne su rinka kiyaye abinda suke yi a gaban Amatullah don wayo ne da ita. Sai kaga kamar bata kula da abu ba sai zance ya tashi ta maido dashi.
Kyakkyawar tarba suka yiwa su Gaddafi. A nan suke bata labarin yadda rayuwarsu ta canja bayan haduwa da ita da suka yi harda komawarsu asibiti nemanta. A yanzu basu dade da dawowa daga Jami'ar Madinah ba inda sukayi degree. Asmau taji dadi da ta kasance silar shiriya garesu. Sunyi hira sosai da Col. Ishaq aka nuna musu Amatullah a matsayin yarinyar da ta haifa. Da zasu tafi duk su biyun sunyi mata alkhairi na kudi wanda su Asmau suka nuna rashin amincewarsu. Gaddafi yace sun dauketa kamar 'yarsu ne don Allah kada a mayar da hannun kyauta baya.
Haka su rabu cikin mutunta juna har nambobinsu na waya Col. Ishaq ya karba.