32

4.5K 348 2
                                    

ABINDA AKE GUDU🙆🏽32

Batul Mamman💖


Kasa motsa kafarta tayi ta cigaba da tafiya saboda wani irin yanayi da ta tsinci kanta. Jikinta duk yayi sanyi. Hajiya ta dafata
"Addua zakiyi ta yi a zuciyarki. Komai yazo karshe da yardar Allah"

Asmau tayi ajiyar zuciya ta kara kallon gidan. Yasha sabon fenti ga wasu filawoyi da aka zagaye shi dasu. Daya gefen da yake da girma shima tunda tun asali filin biyu ne a hade ta kula gini akeyi ga katanga da aka fara wadda zata raba gidajen biyu. Tafiya ta rinka yi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki suka karasa kofar gidan. Ta daga hannu zata kwankwasa kenan aka bude.

Bakuwar fuska ta gani wata mace da danta karami a hannu yana ta rigima. Da alama sauri take yi ta fita daga gidan. Kallon kallo suka tsaya yiwa juna da ita da Asmau wadda tuni hawaye ya wanke mata fuska. Wacece wannan ta tambayi kanta, kuma ina su Umma suke???

Asmau zata girmi matar amma ba sosai ba ta kara kallonta da kyau kawai sai ta kwala ihu tana cewa _Alhamdulillah_ sannan babu zato babu tsammani ta rungume Asmau kamar  taga 'yar uwa ta jini. Yaron hannunta ya soma wani sabon kukan ta dungure masa kai "kai don Allah rufa mana bakin sarkin kyuya mamanka ce wannan"

Tana dariya ta kama hannun Asmau  duk ta rude da murna "ikon Allah Asmau sannu da zuwa, ni na rasa me zan fara yi. Shigowa zakuyi ko tafiya zamuyi ne?" Ita kadai take maganar tana gyara yaron hannunta.

"Banganeki ba baiwar Allah, ina masu gidan na da?" Asmau ta fada cikin kuka.

Daga waje Col Ishaq kasa zama wuri daya yayi ya dan turo gate din. Ganin da yayi musu a tsaye a bakin kofa yasa yayi saurin karasowa daidai inda matar take cewa "yi hakuri wallahi ji nake yi kamar a mafarki. Sunana Sabira, matar yayanki ce Jafar."

Sai a lokacin hankalin Asmau ya dan kwanta. Sabira ta nuna yaron da ta ke rike dashi "ga Abid mai sunan Baba. Su Umma suna gidansu tun kafin aurenmu suka tashi daga nan"

"Gidansu kuma?"

Cikin tsabar murna tace "Eh kada ki damu babu nisa. Suna ake yi nima can zan koma. Jafar ne ya manta mukullinsa na gida kuma motar na wurin Yassar shine na dawo yaci abinci. Fitarsa kenan ya koma wurin aiki."

Col Ishaq da ya soma gajiya da zancen baiga an yunkura ba yace "kuzo muje inda suka koma din"

Sabira tayi gaba Hajiya na bin bayanta rike da hannun Amatullah. Asmau zata wuce ta gaban Ishaq yayi magana daidai yadda ita kadai zata ji "haka kike da saurin kuka Ummin Safina? Gaskiya shima kada ki koya mata, 'yar soja ba raguwa bace"

Tayi dan murmushi ta daga mayafi zata goge fuskarta yace "kada kisa mayafinki akwai tissue a mota."

Bata ce komai ba ta shige motar. Baya tayi niyar shiga ya dan kalleta "ki dawo nan, zaku matsu a bayan"

Amatullah ta dora a cinyarta a gaban ya ja motar Sabira tana yi masa kwatance. Tafiya yake yi amma hankalinsa yana kan Asmau ya kula hankalinta a tashe yake. Amatullah kuwa baya take lekawa tana tambayar Sabira ko zata bata baby idan sun sauka.

Hajiya tace "banda tsaurin  ido ina ke ina karfin daukarsa. Sai dai ayi rungumeni mu fadi"

"Babana wai bani da kayfi?" Ta tambayi Ishaq.

"Princess dina akwai karfi sosai. Ina jin kema soja zaki zama kawai".

Sabira tana son tambaya game da Amatullah sai ta daure. Bari dai su karasa bata san irin farincikin da zasuyi ba.
Daga kwatancen da take yi Asmau ta fahimci gidan Hajjo suka nufa. To me Umma take yi a gidan? Tambayoyi da dama ne suke yi mata yawo a kanta.

Tun daga nesa ta gane gidan duk da anyi fenti ta waje an canja gate din. A nan ma daga waje ya ajiye motar saboda mata dake shige da fice. Suka firfito shi kuma ya zauna tare da bude kofar ya ziro kafafunsa waje.

ABINDA AKE GUDU (Completed)Where stories live. Discover now