NIDA YA AHMAD

5.7K 389 79
                                    

*🍒🌺NIDA YA AHMAD🌺🍒*

*[ROMANTIC LOVE]*

*WATTPAD@ASMASANEE*

*INSTAGRAM@BYNERH_AUGIE*

*SNAPCHAT@ASMASANEE*

_Wannan shafin na kune masoyan asmerhluv group ina yinku sosai ina matukar jin dadin comment dinku ana mugun tare💃💃💃🌹🌹🌹_

*97~98*

Kyakyawan matshin mutum wanda baxai wuce shekara 28 ba a duniya ,sanye yake cikin kayan bacci riga da wando cotton(idan ma baka san kayan bacci baxa ka dauka kayan bacci bane)farare ne Kal,
"A hkl yake driving motar sa kirara benze E class ,cos of ruwan da akeyi kmr bakin kwarya,.
Bakomi yasa shi fitowa cikin wannan daren ba sai don matar sa dake da juna biyu ba abinda take bukatar ci a cikin daren nan sai doughnut koshi sabo da xafin sa,shi yasa shi fitowa yanxu ,yana kuma fitowa koh nisa baiyi ba a barke da ruwan sama,
"Har ya wuce ya kara dawo baya ya tsayar da motar sa bai kashe ba yana kokarin fitowa ,na riga sa ganin ya tsaya ,ba kalmar dake fitowa baki na sai help ina fada ina jijjiga abyaz dake fitar da numfashi a wahalar ce,
"Shi da kansa yayi mun alama da hannu sa in shigo lkc da ya bude murfin motar,
"Ba tare da wani tunani ba na shiga motar ina rawar sanyi ga hawayen da suka k'asa tsayowa saman fuska ta,,,
"Tada motar yayi bai iya cewa komi ba cos tunani fal cikin xuciyar sa komi ya fito da wannan mata shiyar yarinya cikin dare koh dare ma kusan 1 ga kuma ruwa harda yara guda biyu,,,,
"Bai kalle gefen da nike ba yace ina xaki da wannan tsofon dare? Baki na na karkarwa nace area two daga nayi shiru na maida ido nuna kan abyaz cos ganin nake yaron rasuwa xaiyi doba da yadda gaba daya ya birkice,
"Direct area two ya nufa lkc an fara tsagaita ruwan da akeyi,
"Saida ya shiga unguwar kamin yace na nuna gidan ,koda ma gidan su ammy farko ne baya da wuyur gane wa,
"Horn yayi amma shiru ba alamar xa'a bude gate din lkc da na nuna masa gidan,,
"Saida yayi kusan sau 5 kamin wani karfafen soja ya fito ,tun lkc da na shigo motar tasa bai kalle ni ba sai lkc da na dago ina masa godiya cikin muryar ta wadda sanyi ya rin jaye ta ,
"Duk da yadda fuska ta ta kumbura tayi huku huku ,duk shatin hannuwan ya Ahmad ne kwance saman fuska ta duk da haka bai hana shi hango tsantsar kyaun dake kwance saman fuskar tawa ,gyada min kai yayi baice komi,
Shi da kansa ya fito ya bude min kofar ya kuma amshe abyaz daga hannu wanda xuwa lkc jikin sa ba kmr yadda muka shigo motar bane,
"Sojan na ganin mu ya gane ni yasan wannan matar oga Ahmad ce hakan yasa ya bude kofar kamin kuma ya amshe abyaz daga hannu wannan mutumin,,nan ma saida na kara yi masa godiya kamin na shiga gidan,
****Tunda dare take jin jikin ta weak sosai hakan yasa ta kasa bacci gashi abbu baya nan ,sai ta dauki Qur'an tana karan tawa,duk ruwan da ake lemawa karatun ta takeyi ,ta kare karatu ta fito babban parlour don daukar ruwa a daidai kuma lkc nake dan bell tare da knocking ,
"Har ta soma raxana kamin taxo saitin kofar cike da mamaki tace waye ?
"Ina jin muryar ta cikin kuka nace nice ammy ,baby ta maimai cike da mamaki kamin ta bude k'ofar ,kmr jira nakeyi ta bude kofar na fada jikin ta ina sakin kuka mai tsuma xuciya,,,
"Bata ce komi ba sai cireni jikin ta tayi ta amso abyaz daga hannu sojan nan da ya rakoni,sa'an ta maida kofar ta rufe,,,,
"Xare ido tayi ganin yadda abyaz yake karkarwa ga idon sa da suka canxa kala sosai,ba kalmar dake fitowa bakin ta sai inalillahi wainnailaihi raji'un,,,
Bata ce mun kala ba ta wuce dakin ta ta barni tsaye wurin nan,
Direct toilet ta wuce ta surka ruwa masu dumi sosai tayi wa yaron wanka , sosai ta gasa masa jiki,
"Kayan sanyi masu nauhi sosai ta dauko cikin clot ta saka masa ,sai alkcin yaron ya fara numfashi daidai,na'urar zafi ta kunnawa dakin nan da nan dakin ya dauki zafi,
Inda tabar ni nan taxo ta same ni saide yanxu na sauke abyan daga baya na ,tun lkc da ta kira baby bata kara mgn ba sai yanxu da tace oya baby tashi kiyi wanka tafada lkc da ta k'arbe abyan daga hannu na,
Yadda tayi wa abyaz haka tayi wa abyan,wanda mura ta kama su,nima wanka nayi na sanya doguwar rigar bacci cotton,
"Abun da yayi mun dadi yadda ammy bata ce mun k'ala ba dan gane da abunda ya dawo ni gida ,saima cewa tayi in kwanta in futa ,ta fita....
Sosai wannan abun ya bata ma ammy rai duk abunda Ahmad keyi bai taba bata mata rai ba irin na yau ,duk da tasan ba cikin hankalin sa yake ba at less yasa abunda xaiyi inba da rashin imani ba komi nayi masa ay koh don darajar yaran sa xai raga min,iya dauka da xafi ammy ta dauka da zafi kawai daurewa takeyi don kar ta nuna gaxawar ta,,,
***Allah sarki Ahmad duk yadda yaso yayi bacci kasawa yayi ba abunda idon sa ke nuna masa sai nabla daure da towel,agefe kuma najib yake gani wanda ke sanye da short nicker ,wani irin iska mai xafi yake fitar wa,yana ayya na irin yadda xai ci uban najib idan sun hadu a k'aro na 3,wannan haduwar batayi musu kyau ba,,,,
"A gefe daya koh wani tsanar nabla yake ji na kara linkuwa cikin xuciyar sa ,idan ya tuna wani abu ya taba shiga tsakanin su ji yake kmr ya kashe kansa ya futa,yana cikin haka lubna ta haura saman ta ,yana jin mgnr da take masa cikin kunne amma koh gizo baiyi ba saima lumshe idon sa yayi kmr mai bacci,,,
****Kwance take saman makeken bed dinta sai famar doka murmushi takeyi burin ta ya kusa ciki ,a hankali can kasan makoshin ta take fadi , kuddi ba da kuddin da kike so dasu xan hallaka rayuwar ki sai naga bayan ki sai na maida ke goro koh abin saya,,,koh nace ma rayuwar taki ta nakkasa,,,ni ZEENATU na dauki alkawarin ganin bayan ki da duk kan wata zuri'ar ki,,,,
****Da safe ma koh da na tashi ammy har tayiwa twins wanka ta basu mgnr da abinci su har sun koma bacci ,koda na tashi daga bacci fuska ta tayi ja sosai ta kumbura duk da gasa ta da nayi da ruwan xafi,ga wani sarawa da kaina keyi mun,
Hakan nayi wanka na kara gasa fuska na ,na shirya cikin riga da skirt din atampa simple sai dankwalin atamfa da na aza saman kaina,
"Koda na fito ramlarh na xaune saman kujera tana kallo ammy koh tana kitchen,
"Cike da mamaki ramlarh tace sis yaushe kika xo lkc da ta rungume ni jikin ta ,
Bance komi ba sai murmushi yake da nayi ,ahkl nace bari naci abinci sis ina fadin haka na wuce dining table ba wani abu naci ba sai tsakurar shi da nayi,,,
Lkc da ammy taga fuska ta ba karamin xuciya ammy tayi ba har saida ta kasa shiru cos duk wanda ya kalle fuska ta yasan mari ne nasha har na mara misultuwa,,
"Nikoh baby me ya same ki a fuska har haka duk ta kumbura kmr wadda aka mara ta fada da full confidence dinta tana jiran abunda xance,
"Bance kala ba sai wasa da nakeyi da yatsun hannu na ,ba mgn nakeyi miki ba ammy ta fada a xafafe,alamar tafara hasala,,
"Raurau nayi da ido alamar kuka nayi kamin nace....ya...Ah..mad...ne..ya..ma..re...Ni.....kuma sai nayi shiru na kasa isuwa,
Kuma me ammy ta tambaya cike da faduwar gaba ,ba karamin tashin hankali ta shiga ba ta ida mgnr tana xare mun idanu don ma kar nayi mata karya,
Kuka na fashe dashi cike da cracking nace ya s..a..k..e..ni, ina fadin haka na mike na bar wurin da dan gudu na,
"Ba kalmar dake fitowa daga bakin ammy sai kalmar shahada ,wace rayuwa ce wannan ammy tafada ,ji takeyi kmr tayi kuka da badon ta daure ba da hawaye sai sun sauko mata,,,
Duk wani abu da ammy keji game da sakin da nace anyi mun daure wa takeyi bata karamin mgn akan wannan batun ba,
"Da dare da tayi waya da abbu ta xayyane masa duk abunda na fada mata hadda mari sosai shima abun ya suka shi kuma yace idan ya dawo cikin sati mai xuwa dole a sanar da baffa abunda ake ciki,sosai ammy tayi na'am da wannan shawara,
"Sosai cikin satin nan guda muka canxa ,gaba daya na tattara alamarukka na na mike su gun mahalacci na kullun cikin kai kuka na nakeyi ga mahalacci na,,,,
"Cikin week din na dai bana jin dadin jiki na sosai kullun cikin kasala nake saide ban sanar ma kowa ba,,
Xaune nake saman kujera sanye cikin doguwar rigar material gefe na ramlarh ce kiyi wa twins wasa sosai wasar tasu ta shagalar dani ina kallon su cikin so da kwana ,sunaye suke fadi idan tun satin da ya wuce suka iya aunta(aunty)yau kuma sona tashi kmr hadin baki suka tashi da mani(mami)shine fa take kuya musu abbie amma sun kasa fadi sai gwalanniya sukeyi,suna dariyar su basu da wata dry
Muna cikin haka door bell yayi kara , ramlarh ce ta mike ta dubo , sis wai anayi miki sallama a waje ramlarh tafada lkc da ta dawo ,kira kuma?Na maimai ta cike da mamaki,, ramlarh bata kawo komi ba sai xama tayi ta cigaba da wasan ta da twins
________________________________
"Daji ne sa hihin sa ,baxa ka taba cewa akwai mutanen dake zama cikin dajin ba ,
Zan iya cewa kusan an ci rabin dajin kamin a samu gida kwara daya ,xan iya cewa gidan xai kai girman estate,anyi masa painting da ja koh ja irin jawur din nan,sai kuma ratsin baki ak'asa irin kuma paint din nan mai mai,,
Cikin gidan kuwa anyi painting da red colour , Allah idan kaga painting kadai sai abun ya tsora ta ka ,tun bakin kofar xaki fara ganin mutane sanye da doguwar riga ja amma bata ida kai kasa ba anyi xanen kai da kafa☠️ kmr wannan symbol de,
"Duk maxan dake bakin kofar kan su anyi musu tauttoli kmr ki gina masu sok'o,har wani walkiya yakeyi kmr abunda aka xuba ma kwalbar mai,
"Lungu lungu ne wuraren gidan,
"Babban parlour ne wanda ba komi ciki sai kayan tsafi abubuwa kam xar tsoro,koh ina anyi like like sai de abubuwan dake wurin red colour sunfi yawa ,sai can kuma xaki ga black colour,,
"Wurin ba kujera koh daya sai wani abu kmr capet shi ba capet ba ,sai can gaba kuma aka dan dibe wuri daya alamar na wanda shine babba wurin xai xona ,anfi kawata wurin da kayan tsafi,inda a dan saman wurin aka rubuta
*Barewa cultism association*da red colour,
"Baba daya both maxa da matan ke xaune a wurin koh wannen su sanye suke cikin kayan irin wa'inda nayi bayani a baya da mata da maxa duk kaya iri guda ne,
"Mutum daya ce bata sanye da kayan tana sanye da normal kayan ta ,kuma kallo daya xakayi mata ka gane a matukar tsora ce take kawai tana daure wa ne,
"Abubuwa da sukeyi ne suka gabatar da wakoki ne sukeyi koh me Allah kadai yasan abunda suke fadi sai kuma su dake fadin abunsu,
"Nan kuma aka kama yawo da wani abu cikin kwarya ba kadan na tsora ta ba ganin jini ne xube a cikin kwaryar,gaba daya mutanen dake xaune cikin wurin sun sha jinin amma banda mutum daya,
"Sunyi duk wani abu da sukeyi idan suka taro kamin kuma a koma kan wannan matar mai sanyi da moopty mgnr,,,
"Duk inda muni yake wannan bawan ya hada shi ,da kuma gani shine babba a wurin,sosai kowa ya natsu yana jin abunda yake fadama wannan matar,
"Tun lkc da wannan mutumin ya fara mgn wannan matar bata dago ba duk da yadda mgn tashi ke firgita sai yanxu da yake fadi,,,
*Duk tsari na wannan gida kin sani ,kuma kinga daular da kike cikin ta ,sai dai baxa ki fara abubuwan da kika ga munyi yau ba har sai karshen shekara alkcin kuma xaki bada wani abu da ya xama jigo na rayuwar ki ,ina nufin dole sai kin sa sadaukar da jinin ki wato jinin mahaifiyar ki ,koh diyar ki ,koh kuma mijin ki cikin wa'inan sai kin bada daya daga cikin su a karshen shekara,duk wani abu na kungiya dake xa'ayi shi*
" Tun lkc da ya fara wannan statement tashi ga cikin tashin hankali mara misultuwa , tambayar xuciyar ta takeyi Ahmad xata bayar koh yumna koh kuma mommy ta tata bayar wa,, wayyo ni lubabatu(lubna) wane hali nake ciki
Har aka kare bata san wani hali take ciki ba illa kada kai da take famar yi har wanda suke tare ta rikoh hannu ta alamar ta mike tsaye,,,..!!!!

Sorry for d errors

Follow ,vote, share comment nd pray

Follow me on IG@bynerh_augie

Happy jum'at Mubarak

Don't forget to recite suratul khahafi🤗

Asmaluv for life🌹

NIDA YA AHMADOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz