NIDA YA AHMAD

4K 303 55
                                    

*🍒🌺NIDA YA AHMAD🌺🍒*

*WATTPAD@ASMESANEE*

*INSTAGRAM@BYNERH_AUGIE*

*DEDICATED TO REAL MAMAN WALEEDA*

*BESTOWED TO MY BOY AYMAN*

*123~124*

بسم الله الرحمن الرحيم

      "Inalillahi wa'innailaihi raji'un itace kalmar da na maimai cike da rudu,meke  shirin faruwa me abbu ke nufi ba dai yana nufi na aure isma'il ba a yanxu,dago da kaina nayi ina kai duba na inda Ya Ahmad ke xaune kmr mutum mutumi daga gani shima baya cikin hankalin sa,
  "Allah sarki sai naji damuwa ta karama ce kai ga wadda nake gani tattare ga gwarxon mijin nawa(kuji fa Nabeela wai gwarxon mijin ta koh ta manta da sakin ne? zuwairasulaiman ki bani amsa inda samu harda Aishatuduling😁😁),,wani tausayin sa naji yayi mun farar daya wanda na rasa name nene,
  "Iya sani na nasan ina son Ahmad amma idan na tuna abunda yafaru baya sai naji duk wani so da nake masa ya wanke a cikin xuciya ta,,amma yau kwata kwata banji wannan abun da nake ji ba saima wani sonsa da naji ya linku cikin xuciya ta,,amma lkc da yanxu ba igiyar aure akan mu ,bayan haka ga kuma abunda abbu yafada yasa na shiga tashin hankali farat daya wanda yasa ni sakin dan marayan kuka harda shashshe ka,,
   "Jin kukan nata yakeyi kmr ana kara masa wutur son ta ne ga wani abu da yake ji yana da wainiya dashi ,sanin kansa ne idan har bai bar parlour ba xai iya making something worst a parlour yasa ya mike koh kallon inda nake baiyi ba ya fita daga cikin parlour,,
   "Ay nan na na kara sakin kuka harda turje turje kmr karamar yarinya ina kuka ,ba karamin haushi naji ba ganin Ahmad yatafi ya barni ba tare da yalalla she ni ba(kuji mun yar wayo ita bata lallashe shi ba sai shine xai lallashe ta indeed baxa ku samu haka ba ummiejikamshi🤣),,,....
  "Ramlarh ce tafito rike da princess sai famar tsala ihu take tana naimar uwar ta ,sai suka xo suka iske uwar na tsala nata kuka hadda han kade siket din shadda😂(mmn abulkhairi miye hakan?haka abun ya kaiku)
  "Me yake damun ki sis ramlarh tafada cike da damuwa,dago da ido na da sukayi jawur na banka mata harara ina ci gaba da kuka na,,,ganin abun baxai mata ba yasa tabar wurin cike da mamakin me kuma akayi wa sis take abu kmr karamar yarinya ,bata da amsa yasa ta kama bakin ta tayi shiru,,kamin taji maxga daga wurin Nabmad😁amma adafa yanxu ta koma nab'il😜(haka abun dai ya koma meenat anfa dad'a)
*****
    "Direct dakin sa ya wuce yana mai kiran wannan rana da bad day idan har ya tuna da abunda yafaru mint ago,,,abbu xai xaba farin cinkin wani bisa ga nashi,koh a mafalki bai taba tunanin wannan abun xai faru ba,yaushe ya saki Nabeela yana so yatuna ranar amma ya kasa,,duk abunda yaso ya tuna ya kasa a baya yasan ya kore ta amma shifa bai san a wani lkc bane,,ba makawa wannan abun duk yana cikin makircin da lubna ta shirya , haushi hade da tsanar tane suka kara dirar masa a xuciya
  "Yau yau ba shawara nake baka ba kaje ka maido da matar ka idan har na isa da kai tafado masa arai nan take yaji jikin sa wani iri ya kara xama so week kmr bashi ba,
  "Amma ba yarda ya iya dole ne ya bi  mgnr abbu sa don gujewa fadawa halaka,
  "Bai canxa kaya ba sai raramar key dinsa yayi ,direct inda aka tadana don parking cars ya nufa ya shiga cikin daya daga cikin latest version dake wurin ya bata wuta a tsiya ce har tashi buge gate din gidan yayi kamin ya bude,,koh kan road haka yake gudu kmr wanda yayi shaye shaye,bai xarce koh ina ba sai gidan su lubna ya banka uwar horn,
  Da sauri gateman din gidan ya fito amma bai bude k'ofar ba ,hakan ba karamin k'ular da Ahmad yayi ba,
  "Sauke glass din mota Ahmad yayi ganin gate man din ya nufo motar ,kasa kasa Ahmad ya amsa masa,ba tare da komi ba gateman din ya sanar masa da duk kan mutanen gidan basa nan suna hospital,
   "Ya ilahi Ahmad yafada yana dakun sintering mota , general hospital yafada masa don yaji aunty Aisha lkc da taxo gida tana fadi,
  "Gdy yayi ma gate man din ya kara jan mota bai xarce koh ina ba sai hospital,
   " ward dinda ya kwanta ya nufo cikin sa'a koh yana shiga ward din ya hadu da Aunty Aisha sai xarya take hakan yasa ya nufe ta cike da kwarin gwaiwa,
  "Ay itama tana ganin sa ta ta nufo sa ba tare da wani tunani ba ta rikoh wuyan rigar sa tana sakin dan marayan kuka wanda da kaji wanda yakeyin sa kasan yana cikin tashin hankali,tafara mgnr
  "Bantafa tsammanin xuciyar ka ta kai haka ba,banxa ta baxa ka iya yiwa wanda yayi maka laifi yafiya ba ,nasan lubna tayi maka laifi mai muni amma ban xata har xaka iya yi mata cin mutuncin irin wannan ba,baxa ka taba cewa tsawon shekarar auren ka da ita ba bata taba yi maka abu da kaji dadin sa ba,amma lkc guda ka rufe ido,nasan Allah koh wannan halin da take ciki kaine sila,amma ba komi duniya yace,idan lubna ta mutu Ahmad ka xuba ruwa a k'asa kasha nasan haka xaifi maka dadi,tana gama fadin haka ta rushe da kuka mai xafi da tsuma xuciyar mai sauraro,,,ta sake wuyan rigar Ahmad ta durkushe a wurin,,
   "Gaba daya jikin Ahmad yayi sanyi da mgnr Aisha,amma koh daya baiji tausayin lubna ba ,don duk halin da ta tsince kanta ita ce silan faruwan haka,
  "Suna ahaka doc ya fito daga cikin dakin da lubna take daga gani kuma shine head cikin doc hakan yasa Aisha na ganin sa ta mara masa baya,
  "Ahmad na ganin haka shima yabi bayan su,
  "Koda ya isa Aisha har ta xauna haka yasa shima ya samu daya daga cikin kujerun dake daki,
  ",Koda likita yaga Ahmad bai damu ba ya dauka mijin ita marasa lpy ce  hakan yasa ya fara mgn yana kallon su biyu din,
  "Gsk am sorry to tell u patient din tamu na gab da rasa heart dinta ,heart attack dinda ta samu kuma yana gab da ida bugawa hakan yasa kika ga ta fara wannan vomited na jini kuma yana xubo mata both hancin ta da baki,,, shawara daya xan baku patient dinmu na bukatar kulawa abunda yasa ta shiga wannan halin inba hakan ba xata iya rasa ranta cikin kankanen lkc,,,ya ida mgn yana nisawa hade da furxar da iska mai xafi,
  "Don Allah doc xamu iya samun transfer I want us to live dis country within 2 days ,cos duk abunda ka fada ba wanda xata samu so gara we should move per koda hakan xaisa ta rage radadin abunda take ji,
  "Bcos of wat doc yafada ,baya da amfani kasani Aisha tafada ba tare da damuwa ba,
  "Shima bai damu ba yace xa ku iya samu amma xan baku shawarar kuje Egypt xaku  samu kula sosai bisa ga nan ,godiya tayi masa tace yau xata je ta naimo visa,
  Ba matsala ,shide Ahmad kallon ikon Allah yakeyi don ba abunda ya gane cikin mgnr su ,amma idan ya fahimce abunda suke nufi lubna ce bata da lpy,
  "Koh da yafito Aisha har ta shiga mota ta hakan yasa shima ya shiga tashi da yaso yayi tafiyar sa sai wata xuciya ta bashi shawara da yabi bayan ta haka koh yabi ta maimakon yaga tabi hanyar gida sai yaga tabi hanya daban hakan ya kara basa mamaki,
  "Agefen ta koh shawara ta yanke da taje taga mommy kamin su wuce koh da akwai abunda ake bukata
  "Daidai asibitin mahaukata tayi parking mota,
  "Sosai ya maimata sunan da ya gani gaban asibitin ,ganin har tafito yasa yayi saurin fitowa ya mara mata ba,
  "Ganin yayi tayi mgn da wannan matar ta ranar sai gata ta mike itace gaba Aisha na bayan ta dakin da mommy ke ciki ta bude , subhanallah itace kalmar da Aisha ta maimai ta kasa ida karasa tsaka kafar ta dakin,
  "Hakan kawai yake son ganin abunda Aisha ta gani har take kiran subhanallah don yaji lkc da ta furta,
  "Hakan yasa ya nufo wurin kai tsaye,
  "Inalillahi wa'innailaihi raji'un yafada yana mai saurin rufe idon sa hadda saka tafin hannu,
  "Me hakan ke nufe kada ace dai abunda lubna tafada gsk,kasa iya hada word yayi koh daya sai juyowa yayi ya bar wurin da sauri har yana tuntube,
   "Mumu ce tsaye ba kaya a jikin ta kayan da aka sa mata ta cire gefe ta koma tsirara ,sai hixge hixge take ,ta rame ta kanjame idan ka ganta xaka dauka HIV take dauke dashi kamannun ta sun sauya ta jemaye ,hakan koh tana samun kulawa sosai ne fa don kwanan kin nan ma aka cire mata kacar da aka sanya mata ganin xaiyi mata illa,,,
  "Kai tsaye gida ya wuce yana jin wani kasala da rashin kuxari idan har ya tuna iftila'in da ya gamu dashi(kai kuji Ahmad mommy ce iftila'i),
******
   "Da ker na iya tashi naje daki na ina jan kafa ,yanxu dole sai na aika ta abunda abbu keso gashi yace yau ,oh ni Nabeela diyar 2 jikayan mutum 4 meke shirin faruwa dani akaro na biyu?
  "Bani da yadda xanyi sai yadda abbu keso hakan yasa bayan na gabatar da sallah magrib na kira isma'il kira biyu yayi picking call,
  "Hello....nafada can kasan makoshi
"Hello nabla yakike da fatan ba matsala?,ismail ya tambaya
"Ba matsala saide sai nayi shiru na kasa cewa komi...sai mi nabla kifadi abunda kike son fada kinji yafada cikin sigar lallashi,
  "Abbu....ya...ce...ka..turo nafada murya can kasa hade da cracking ina kuma fadi na datse kiran sakamakon wani kololon bakin ciki da naji ya mamaye min xuciya ina ji lkc da kiran sa ke shigo wa amma nayi banxa kmr banji ba,
  ****
   "Asuba bayan ya tashi yayi sallah rashin baccin da bai samu ba jiya da dare yasa yana tashi yaji wani malala cin bacci ya sure sa bashi ya falka ba sai wuraren 12 ,sosai lkc da ya fallaka yayi mamakin irin wannan baccin da yayi,wanka yayi a gaggwa ce amma duk da haka bai gama shiri ba sai kusan 2 hakan yasa saida ya biya massala cin dake makale a gidan yayi sallah kamin ya shiga mota sa ya bata wuta sai hospital,,
  "Idan ya hadu da Aisha jiya nan amma bai ganta ba , cikin sa'a ya hadu da doc jiya,nan yake tambayar sa ,nan take doc yafada masa ay suna amshi transfer,kuma da yadda ta fada masa jirgin su xai daga by 12,
  "Gdy yayi ma doc yafito jiki a sanyaye,yaso ya iske Aisha don akwai abunda yaso fada mata ,baiso sukayi tafiyar nan bai fada mata maimakon yayi gida sai ya canxa akala mota sa xuwa gidan ammar,,,,,

Nasan sai kun samu errors da yawa aciki manage🙏

Muje xuwa nida ya Ahmad,vote share comment,follow ar all need

Asmerhluv ce💕💕💕💕
 

NIDA YA AHMADDonde viven las historias. Descúbrelo ahora